Hatsarin mota ya yi ajalin masu aikin Umara 20 a Saudiyya

Motar ta taso daga Khamis Mushat zuwa yankin Abha.

Hatsarin mota ya yi ajalin masu aikin Umara 20 a Saudiyya

Akalla mutum 20 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da wata bas dauke da masu zuwa Umara a ranar Litinin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kimanin mutane 29 ne kuma suka samu rauni a hatsarin motar bas din da ya auku a garin Aqaba Shaar da ke Karamar Hukumar Asir.

Motar da ke jigilar maniyyata zuwa birnin Makkah ta afka layin dogo na wata gada, wanda nan take ta kife, sannan kuma ta kama da wuta.

“Bayanan farko da muka samu yanzu, adadin wadanda suka mutu a wannan hatsarin ya kai 20, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 29,” a cewar tashar talabijin ta Al-Ekhbariya.

Tashar talabijin ta jihar ta kuma ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, hatsarin ya faru ne a lokacin da motar bas din ke dauke da maniyyatan kasashe daban-daban ta taso daga Khamis Mushat zuwa yankin Abha.

An bayyana kwacewar birki ne ta haddasa hatsarin.

Umrah wani tsagi ne na ibada da ke bai wa Musulmi damar tsarkake imaninsu, neman gafara da kuma neman daukin Allah Madaukakin Sarki game da bukatunsu.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50