Hatsarin sanya yara a kujerar gaban mota —FRSC

A duk lokacin da mota ta yi hatsari, kananan yara da ke gidan gaba za su fadawa waje ta taga

Hatsarin sanya yara a kujerar gaban mota —FRSC

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta yi gargadi ga iyaye da masu motocin haya kan sanya kananan yara ’yan kasa da shekara 12 a gaban mota.

Kwamandan Hukumar, Reshen Jihar Ondo, Uche Chukwurah ta ce ta bayyana cewa sanya yaran da ba su kai shekara 12 ba a gaban mota ya saba wa doka.

Ta yi karin haske da cewa a duk lokacin da aka samu hatsarin mota, kananan yara da ke gidan gaba za su iya fadawa waje ta tagar motar.

Kwamanda Uche Chukwurah ta ce a don haka, sanya su a kujerar bayan mota shi ya fi, domin kare lafiyarsu da rayukansu.

Ta bayyana haka ne a jawabinta na bikin Ranar Yara ta Duniya da rundunar ta shirya a ofishinta da ke Eleyele da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Bikin na Ranar Yara ta Duniya dai ana gudanar da shi ne a duk ranar 27 ga watan Mayu, kuma taken bikin na bana shi ne “Shiryawa Kowanne Yaro Kyakkyawar Makoma”.