Hatsarin tirela ya ci rayuka 21 a hanyar Kaduna-Abuja

Mutane 21 sun rasu a hatsarin tirela da wava bas a kan Babar Hanyar Auja zuwa Kaduna a safiyar Alhamis.

Hatsarin tirela ya ci rayuka 21 a hanyar Kaduna-Abuja

Tirelar raken da ta yi hatsari a Babbar Hanyar Kubwa da ke Abuja

Mutane 21 sun rasu a hatsarin tirela da wava bas a kan Babar Hanyar Auja zuwa Kaduna a safiyar Alhamis.

Hatsarin ya ritsa da matafiyan ne a tsakanin yankin Gidan da Abe da ke Karamar Hukumar Kagarko.

Matafiyan sun gamu da ajalinsu ne bayan tirelar da ke hanyar zuwa Kano da wata bas kirar bumber da ke hanyar zuwa Batsari a Jihar Katsina sun yi karo.

Wani jami’in hukumar kiyaye haddura da ke cikin masu aikin ceto ya ce fasinjoji uku rayu suna kwance a asibitin tunawa da Umaru Musa da ke garin Sabon-Wuse, inda a nan aka ajiye gawarwakin a mutuware.

Jami’in ya ce an yi hatsarin ne kusa da wata mahada, lamarin da ya  toshe hannu daya na hanyar tare da kawo cunkoson ababen hawa.

Wasu shaidu na zargin diraben tirelan ya tsere ya bar ta a wurin.

DPO na ’yan sanda a yankin Tafa da ke kan hanyar, S.P Idris Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce suna kokarin kammala tattara bayanai.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan