Hattara! Ana iya satar tunaninka nan gaba

Idan aka ambaci ’yan Dandatsa a zamanin yau, ba abin da mai karatu ke iya tunawa face ’yan fasakwaurin bayanai ta hanyar kwamfuta da Intanet; masu ta’addanci cikin kwamfutocin mutane suna sace bayanan sirri da ke cikinsu, tare da haukatar da su ko barnatar da duk wani abin da suka ga damar barnatarwa, kafin su […]

Hattara! Ana iya satar tunaninka nan gaba

Yanayin kwakwalwaIdan aka ambaci ’yan Dandatsa a zamanin yau, ba abin da mai karatu ke iya tunawa face ’yan fasakwaurin bayanai ta hanyar kwamfuta da Intanet; masu ta’addanci cikin kwamfutocin mutane suna sace bayanan sirri da ke cikinsu, tare da haukatar da su ko barnatar da duk wani abin da suka ga damar barnatarwa, kafin su fice.  
Sai dai kuma, wani abin da mai karatu ba zai yarda ba, idan aka fada shi ne: akwai yiwuwar sace wa dan Adam tunaninsa daga kwakwalwarsa, ba tare da saninsa ba, ta amfani da na’urorin sadarwa da taskance bayanai na zamani.
A cikin shirinsa na musamman mai taken: ‘Through the Wormhole’, wanda tashar kimiyya mai suna ‘The Science Channel’ ke gabatarwa a duk mako, shahararren jarumin fim Morgan Freeman ya hankado yiwuwar hakan a yau da kuma nan gaba.  Dangane da tattaunarsa da shahararrun masana harkar kimiyya da kwakwalwa, a fili yake cewa nan gaba ba zai zama da wahala ba, kuma ba zai zama abin mamaki ba a sace wa mutum tunaninsa da yake yi, ko a iya fahimtar tunanin da yake yi, sannan in so samu ne ma, a iya gurbata tunanin, ta hanyar shigar da wasu nau’ukan tunanin ko hargitsi irin na sauti ko wani abu makamancin haka.
A takaice dai, nan gaba za a iya satar tunaninka, ko a gurbata shi, ko kuma a yi fasakwaurin bayanan ma, kamar yadda ’yan Dandatsa (wato Computer Hackers) ke satar bayanai daga kwamfutoci a wata uwa duniya a yau.  Tirkashi!  Wani abin sai ilimi, ba sihiri ba ne, ba kuma da’awar sanin gaibi ba ne.
Philip Low, shahararre ne a fannin sirrin kwakwalwa da maganadisunta (wato Neurotechnologist).  A halin yanzu yana aiki ne kan wata ’yar karamar na’ura wacce za a iya amfani da ita wajen “karanta” siginar bayanan masu kwakwalwa, masu dauke da nau’ukan tunanin da mai kwakwalwar ke yi a halin da yake tunanin.  Wannan na’ura mai suna ‘iBrain’, za ta iya taskance siginar bayanan  kwakwalwa (Brain Siginals) da zarar an dora ta a saman kokon kai.  Nan take za ta fara karanto siginar kwakwalwar don aikawa da ita cikin kwamfuta, inda za a iya ganinsu, tare da fassara su don gano me suke nufi.
Mista Low ya ce amfanin wannan na’ura shi ne taimaka wa wadanda suke da matsalar shanyewar hannu sanadiyyar cutar da ta same su, musamman cutar Alzheima.  Ya ce masu irin wannan cuta suna dauke ne da hannun roba, wacce idan suka dora wannan na’ura a saman kokon kansu, tare da jona ta da kwamfuta, nan take siginar kwakwalwarsu za su fara bayyana a shafin kwamfutar.  Ya ce wannan zai taimaka musu wajen gyatta tunaninsu wajen sarrafa wannan hannu nasu na roba.  To amma kuma ta yaya za su iya fahimtar abin da wadannan siginar bayanai ke nufi, wanda hakan ne zai bayyana musu tunanin da suke yi?
Wannan abu ne mai sauki, a cewar masanin kimiyya, Mista Jack Gallant, wani shahararre kan kimiyyar kwakwalwar dan Adam (Neuroscientist). Domin a halin yanzu aikin da yake yi ke nan. Ma’ana, gina wani kamus na musamman, mai dauke da yaren siginar kwakwalwa na musamman (wato Brain Dictionary).  
Wannan kamus, a cewar Gallant, shi zai fassara dukkan wani sigina na kwakwalwa da mai kwakwalwar ke gani a shafin kwamfuta, don ba shi ma’anar da siginar ke ishara gare ta, cikin hotuna da rubutattun bayanai.  
Masanin ya yi hakan ne ta hanyar wani gwaji da ya fara, inda ya ajiye mutane da dama, tare da lura da siginar kwakwalwasu a lokacin da ya ba su dandazon hotuna daban-daban, suna kallo, shi kuma yana nadar irin tunanin da suke yi a tsarin siginar kwakwalwa, cikin sauki.  
Mista Gallant ya yi amfani ne da na’urar taskance siginar kwakwalwa ta zamani mai suna ‘functional Magnetic Resonance Imaging (fMRI)’.  Ya ce a halin yanzu suna nan suna ta kokarin gina wasu ka’idojin hasashen tsarin tunanin mutanen kan hotunan da suke kallo.
A daya bangaren kuma, wasu masana sun tabbatar da cewa nan gaba kana iya satar fasahar kwarewa daga kwakwalwar mai kwakwalwa a sadda yake aiwatar da sana’a ko aikinsa.  Misali, idan Tela yana dinki, ga kwakwalwarsa a jone da kwamfuta ana taskance siginar kwakwalwarsa, masana suka ce abu ne mai sauki ka iya gane sadda kwakwalwarsa ta kai makura wajen tunanin yadda yake tafiyar da aikinsa, cikin kwarewa.  
Wannan tsari, a cewar Chris Berka, na iya taimaka wa mai tunanin, ta hanyar nazarin fassararren siginar kwakwalwarsa a sadda yake tafiyar da aikinsa, don gane sadda nau’in tunanin da ke samar masa da kwarewa ke cika; da sadda yake raguwa, don ba shi damar tabbata a marhalar cika.  Ga wanda ke son “sace” wa tela tsarin tunaninsa kuwa, Berka ya ce wannan abu ne mai sauki.  Tirkashi!
To amma bayan sace tunanin a sadda mai tunanin ke yinsa, ana iya gurbata shi?
Eh, inji shahararriyar masaniya a fannin ilimin dabi’a, Ilana Hairstone.  Ta ce ana iya hakan ma ba tare da sanin mai kwakwalwar ba.  Kamar yadda ’yan Dandatsa (Hackers) ke amfani da “kafa mai rauni” tsakanin hanyoyin sadarwar kwamfuta (wato Cracks), to haka za a iya amfani da “kafa mai rauni” tsakanin hanyoyin sadarwar kwakwalwa (wato Brain Pathways), don shigar da wasu bayanai a tsarin sauti ko makamantan haka, zuwa cikin kwakwalwa, har ya saje da sauran nau’ukan tunanin da mai kwakwalwar ke yi.  
Daga cikin kayan aikin da za a iya amfani da su wajen fahimtar kafa mai rauni a kwakwalwar mutum, inji Hairstone, akwai dabi’ar “sinsino.”  Wannan dabi’a na ‘sinsino’ na iya taimakawa wajen shigar da bayanai cikin kwakwalwa.  
Ilana Hairstone ta gudanar da gwaji na musamman kan wannan al’amari, tare da tabbatar da yiwuwarsa.  Abin kamar almara.  Ta ce an tanadi mutane ne, aka umarce su da yin bacci, sannan aka fara taskance siginar kwakwalwarsu a sadda suke baccin.  Ta amfani da dabi’ar sinsino, Ilana Hairstone ta shigar da wasu bayanai a yanayin sigina, wadanda suka bi ta hanyar sadarwar kwakwalwa, don isa cikin rumbun tunanin masu kwakwalwar.  Wannan ke nuna cewa da zarar sun farka, ana iya samun nau’in bayanan da aka shigar musu kwakwalwa, idan aka yi musu tambayoyi masu alaka da su.  Allah Buwayi, gagara misali.  
Wannan ke nuna cewa nan gaba akwai yiwuwar gurbata wa masu laifi tunaninsa ba tare ba su wani abu na barasa ko amfani da tasirin wutar lantarki ba, don cinma wasu manufofi.  Allah Ka daidaita mana fahimtarmu, tare da ba mu dacewa cikin dukkan lamuranmu baki daya, amin.  

Amsoshin Wasu Tambayoyinku

Assalaamu alaikum, ina son Baban Sadik ya kara mini fashin baki kan yadda ake tsara Mudawwana, wato Blog.  Ta yaya zan sa murya, da kuma shafin Youtube?  Na gode.  Daga Aliyu M. Sadisu, Minna: [email protected], http://mumbarin-musulunci.blogspot.com
Wa alaikumus salaam, Malam Aliyu ai wannan bai da wahala ko kadan. Tunda kana amfani da masarrafar Blogger ne, idan ka shiga shafinka, sai ka matsa ‘Sign In’ daga can sama a hannun dama, kana gama shigar da bayananka, za a kaika inda tsare-tsaren shafinka yake ne, kai tsaye, wato DashBoard.  Daga nan sai ka je LayOut, inda ake canza wa shafi kamanni da kintsi.  Idan ka samu kanka a can, sai ka matsa alamar ‘Add a Gadget’ da ke sama daga hannun dama.  Shafi zai budo mai dauke da nau’ukan masarrafai masu fa’idantarwa da za ka iya kara wa shafinka. Sai ka zabi wanda kake so.  Idan ma ba ka ga abin da kake so ba, duk bai baci ba.  Daga hannun hagu can kasa za ka ga inda aka rubuta: ‘Add Your Own’, sai ka matsa, ka shigar da adireshin shafin da kake son karawa, ka matsa ‘Add URL’. Ka gama ke nan.  Da fatan ka gamsu.
Salaamun alaikum Baban Sadik, don Allah wace waya ce ta fi shahara a duniya yanzu?  A gaya min sunanta da lambarta da wadda ke bi mata.  Daga: Salisu Sama’ila Zariya: 08065165819
Wa alaikumus salam. Tirkashi!  Malam Salisu ya shirya ke nan.  Akwai su da yawa.  Akwai Z10 na kamfanin Research in Motion masu yin wayoyin Blackberry, duk ba ta wuce Naira dubu dari da goma ba.  Akwai Samsung Galady S4, wacce ke iya lura da yanayin fuskarka da murya a duk sadda kake amfani da ita.  Idan kana karanta wani abu a shafin wayar, tana iya sinsino yanayin fuskarka, da zarar ka kawar da kai, za ta rage hasken shafin don manejin sinadaran batir.  Idan kana karanta rubutun da ke shafin, da zarar ka zo harafin karshe, nan take shafin gaba zai budo da kanshi ba sai ka bude ba.  Don a nuna maka cewa lallai ana amfani da yanayin jikinka ne.  Duk kudinta bai wuce Naira dubu dari da talatin da biyar ba. Ba tsada.
Akwai kuma na ya-ku-bayi, irin su ‘Nokia Asha 501’ wacce ke gab da fitowa.  Mai shafaffar fuska ce, ba ta da allon shigar da bayanai irin na al’ada, sai wanda ke ciki. Komai nata latse-latse ne. Idan har ta fito, ba a zaton za ta wuce Naira dubu goma sha tara.  Wadannan kadan ne cikin wadanda za iya tunawa.  Allah sa a dace, amin.