Hattara APC: Hangen Dala ba shiga birni ba
Hadakar da ta samar da Jam’iyyar APC, wacce ake cewa irinta ce karo na farko a tarihin siyasar Najeriya, al’ummar Najeriya ciki da waje suka rika nuna farin cikinsu da nuna goyon bayansu, domin a zahiri ta bayyana cewa da gaske jam’iyyun hamayyar suke, don kalubalantar PDP a zaben 2015. Shugabannin APC na riko da […]
Hadakar da ta samar da Jam’iyyar APC, wacce ake cewa irinta ce karo na farko a tarihin siyasar Najeriya, al’ummar Najeriya ciki da waje suka rika nuna farin cikinsu da nuna goyon bayansu, domin a zahiri ta bayyana cewa da gaske jam’iyyun hamayyar suke, don kalubalantar PDP a zaben 2015. Shugabannin APC na riko da kuma jagororin wannan hadaka sun bazama jihohi, inda suka rika kai wa ‘yan siyasa da dama caffa, domin tafiya tare don a kawar da PDP daga kan karagar mulkin Najeriya. Wannan ta sanya sabuwar jam’iyyar APC ta farauci wasu daga cikin Gwamnonin PDP da suke da matsala da jam’iyyarsu, aka kuma yi dacen wafto wasu daga cikin ’ya’yan PDP din da suke tayar da kayar baya a cikin jam’iyyar tasu.
Tun farko APC suka kasa yi, ko kuma suka yi batun hada kawunan sababbin ’ya’yan jam’iyyar da ko dai suke da ra’ayoyi mabambanta, ko kuma suke tsananin hamayya da juna. Tunda har wadannan jam’iyyu suka iya yarda su sarayar da jam’iyyunsu, su samar da APC, babu shakka abu ne mai sauki su iya zama a kan tebur, domin su warware matsalolinsu, musamman da wadanda ake ganin akwai hamayya tsakaninsu, wannan wani janibi ne mai muhimmanci da APC ya kamata ta bai wa kulawa ta musamman tun fil azal, amma sai aka yi shakulatun bangaro da al’amarin har baraka ta bayyana kamar wata daren 15.
Tun ran-gini tun ran-zane, inji Bahaushe, a lokacin da APC ta fara zawarcin Gwamnonin PDP, suna sane da cewar akwai hamayya tsakanin wadanda aka kafa APC da su, da kuma, wadanda ake kokarin yin zawarci. Sanin kowa ne a Kano akwai hamayya tsakanin Gwamna Rabiu Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau; a Sakkwato akwai hamayya tsakanin Gwamna Aliyu Magatakarda Wammako da tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa; da kuma Adamawa, inda Janar Buba Marwa ke hamayya da Gwamna Murtala Nyako. daukacin jagororin APC suna da masaniyar wannan hamayyar. Abin da ya kamata a yi tun farko shi ne a san hanyoyin da za a bi wajen dinke wannan barakar kafin zabarin wadannan Gwamnoni. Amma sai idon jagororin APC ya rufe, inda sun san a jihohin da na fada a sama akwai Bafarawa da Shekarau da Marwa, amma aka zabi wasu aka kai wa gwamnonin wadannan jihohi ziyarar zawarci, ba tare da ko da sanar da wadannan mutane ba, babu shakka, a magana ta gaskiya, dole ko waye zai ji babu dadi a ce jam’iyyar da kuka bata lokaci wajen kafawa ta zo har jiharka wajen zabarin mutane, ba tare da wani ya sanar da kai ba! Abin akwai damuwa da rashin jin dadi, wannan ko da wanda za a zawarta ba sa hamayya da shi.
Daga baya APC suka fahimci cewar sun yi kuskure, har suka kafa kwamitin da zai zagaya jihohin Kano da Sakkwato da Adamawa domin bai wa Malam Shekarau da Bafarawa da Buba Marwa hakuri kan abin da aka yi musu na rashin sanar da su zuwan tawagar jam’iyyar jihohinsu. Babu shakka, wannan abu ne mai kyau da APC ta yi. Amma kuma daga hakan ba a yi komai ba, sai aka tsaya a wajen, maimakon a yi amfani da wannan damar wajen tuntubar wadannan mutane wajen ganin yadda za su iya zama inuwa daya da abokan hamayyarsu a siyasa cikin jam’iyya daya, sai aka yi biris da zancen. Gwamnonin Kano da Sakkwato da Adamawa suka ayyana komawa APC ba tare da APC din tana da wani shiri mai karfi a kasa ba, wajen ganin ta sasanta’ya’yanta masu hamayya da juna.
Haka nan, wadannan Gwamnoni suka shigo APC ta sama ba tare da yin wani shiri na karbarsu ba a jihohinsu, da kuma kokarin zaunar da su da abokan hamayyarsu a sasanta su ba, kai kace daman da su aka kafa APC din. Aka yi ta rade-radi game da shigowar wadannan gwamnoni, shugabancin uwar jam’iyyar APC yana ji bai ce ko “bihim” ba akan lamarin, tun kan ya kazance. Aka yi ta turka-turka akan waye ya kamata ya zama jagora ko ba waye ba a wadannan jihohi amma shugabancin jam’iyya yaki yin katabus akai. Har aka zo kan wani mataki da ka iya zamarwa APC mai matukar hadarin gaske a 2015.
A makon da ya gabata Bafarawa wanda daya ne daga cikin jiga-jigan ANPP da suka sarayar da jam’iyyarsu ta ANPP wajen ganin kafuwar APC ya bayyana ficewarsa, amma maimakon a nuna rashin jin dadi da damuwa, sai ya zama abin murna ga wasu, ana cewar Allah ya raka taki gona. Da dama suna fadin da Bafarawa da Shekarau da Buba Marwa ko da su ko babu su APC za ta iya cin zabe a jihohinsu wannan kam gaskiya ne. Ko babu wadannan mutane akwai yakinin cin zaben shugaban kasa a jihohin, amma abin da aka manta shi ne, tun da aka fara wannan sabani jam’iyya mai mulki PDP ta yi amfani da wannan baraka wajen kai wa Malam Shekarau da Bafarawa da Marwa bara, inda take neman su shigo jam’iyyar don ba su damar da aka hana su a APC.
Yana da kyau mu sani, ita APC, ita ce jam’iyyar hamayya/adawa burinta, shi ne ta ci zabe. Don haka duk wata dama da za ta iya kawo nakasu daga samun nasarar APC, ya kamata kar a ba ta kofa ko wace iri ba. Haka kuma, yana da kyau mu sani cewa, ita PDP ba yanzu suka saba cin zabe ba, don haka duk wasu dabaru na sarari da na boye sun jima da tanadin kayansu. Ita PDP ba sai ta cinye Kano da Sakkwato ko Adamawa ta ci zabe ba, kawai abin da suke da bukata shi ne kashi 25 cikin 100 da hukumar zabe ta ce sai jam’iyyar da ta samu a jihohi 23 sannan za ta iya cin zaben shugaban kasa. Masu cewar Ko da Shekarau da Bafarawa da Marwa ko babu su APC za ta iya cin jihohinsu, amma kuma sun manta cewar wadannan mutane za su iya kawo wa PDP 25 cikin 100 a jihohinsu! Anan matsalar take, domin a 2011 lokacin da ake Murna cewa Buhari ya samu kuri’u miliyan biyu a Kano an manta cewa PDP ta samu kashi 25 a kanon. To amma saboda doki da hangen Dala, sai wasu suke ganin cewar ficewar Bafarawa da Shekarau da Marwa alheri ce ga APC.
Babu shakka idan APC ta ci gaba da kame hannu, ’ya’yanta na halak malak suna zurarewa ba tare da ta rufe bakin daurin ba, to tabbas a zaben 2015 za su sha mamaki. Domin mai gishiri ai ba ya wasan shiga ruwa da mai goro. Su PDP da yake da gaske suke son tabbata akan dimokuradiyya, lokacin da Atiku Abubakar da Marigayi Abubakar Rimi suka yi zuciya suka bar jam’iyyar suna zaginta, tare da yi mata jafa’i, uwar jam’iyyar ba ta barsu haka ba, sai da ta kafa kwamati aka yi ta rarrashinsu, har suka hakura suka dawo.
Ni a fahimtata, yanzu ta bayyana cewa babu wata jam’iyya mai tsarki da take da mutanen kirki 100 bisa 100, don haka duk inda mutum ya tsinci kansa ya yi kokarin kawo gyara da kyakykyawar niyya gwargwadon ikonsa. Allah yana ba mu ladan aikin da muka yi dominsa gwargwadon yadda muka kyautata niyya. Don haka, yana da kyau APC su sani hangen Dala ba shi ke nuna an shigo birni ba, kuma mai madi ai shi ke talla!