Hattara da neman kudi dare daya ta intanet —NITDA
Hukumar kula da fasahar sadarwa (NITDA) ta sake gargadi ga ’yan Najeriya bisa shiga harkokin kudi da nufin zuba jari ta intanet musamman wadanda ake turawa ta shafin sada zumunta na WhatsApp. Hukumar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ta yi gargadi a kan shiga harkokin samun riba cikin gaggawa wato Ponzi wanda ake […]
Hukumar kula da fasahar sadarwa (NITDA) ta sake gargadi ga ’yan Najeriya bisa shiga harkokin kudi da nufin zuba jari ta intanet musamman wadanda ake turawa ta shafin sada zumunta na WhatsApp.
Hukumar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ta yi gargadi a kan shiga harkokin samun riba cikin gaggawa wato Ponzi wanda ake yi a kafofin sada zumunta.
“Muna shawaratar daukacin al’umma da kafin su shiga duk wata kafa ta harkokin kudi, su tabbatar tana da rijista da hukuma da ya dace kuma suna da lasisi”, inji NITDA.
Hukumar ta kuma karyata rahotanni da ke alakanta ta da yin na’am da duk wani shiri na samun arziki dare daya a intanet.
Ta ce ya kamata mutane su dinga tantance duk wata harka da ake tallata saurin samun riba, musamman idan ta saba da ka’idojin kare bayanai na intanet (Data Protection Regulation).
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan damfara suna amfani da wannan dama inda suke gayyatar mutane da su shiga kungiyarsu ta shafin WhatsApp.
Kazalika suna samun sauki wajen mallakar lambobin wayar mutane. Suna iya amfani da lambobin na mutane domin aikata muggan laifuka musamman ta intanet.