Hattara da shafin Labaran Karya mai suna Daily Trust Hausa

Labaran karya shafin DAILIY TRUST HAUSA yake yadawa, kuma ba shi da alaka da kamfanin Aminiya da Daily Trust

Hattara da shafin Labaran Karya mai suna Daily Trust Hausa

Aminiya na sanar da jama’a cewa shafin labaran karya a Facebook da Twitter mai suna DAILY TRUST HAUSA, ba nata ba ne, kuma ba ta da kowace irin alaka da shi.

Haka kuma, babu wata dangantaka ta kusa ko ta nesa tsakanin Rukunin Kamfanin Media Trust da ke wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da shafin labaran karyan mai suna DAILY TRUST HAUSA.

Ba shi kadai ba, akwai wasu shafukan labaran karya musamman kafofin sada zumunta da ke makala Daily Trust ko Aminiya a cikin sunansu, sannan suka yi wa tsohon tambarimu kwaskwarima suna amfani da shi saboda yaudara.

Jama’a su sani cewa abin da shafin bogin da ake magana a kai, wato DAILY TRUST HAUSA yake wallafawa karya ne; ba sa tantance labarai sai dai ma su kirkiri abin da bai faru ba ko su juya magana.

Wani lokacin daga wasu wuraren suke kwafo labarai babu bincike ko tantancewa, su rika yadawa a matsyin nasu, ba tare da ambaton inda suka kwafo ba.

 

Ko a kwananan nan sun kirkiri labara, wai Shugaba Muhammadu Buhari ya je Fadar Shehun Borno, ya tona asiri kan wasu kudade da suka ce ya bai wa Gwamna Babagana Zulum.

Tambarin Aminiya a shafukan zumunta.
Shafin bogi da ke yada labaran karya a matsayin kafar Daily Trust

Saboda haka muna kira ga jama’a da su nisanci shafin bogin mai suna DAILY TRUST HAUSA, musamman ma a Facebook da Twittter.

Ku sani cewa shafi daya tal Aminiya ke da shi a Facebook da Twitter da Instagram da kuma TikTok — wato @aminiyatrust — wadanda kowannensu ke dauke da sabon tambarinmu.

Shafukanmu na Facebook da Twitter (@aminiyatrust) na da alamar sahihanci, wato koren maki.

Idan har ba shafukanmu da muka bayyana (@aminiyatrust) kuke bi ba, to kun fada a tarkon ’yan damfara, sai ku gaggauta yin watsi da su.

A namu bangaren kuma, muna daukar matakan da suka dace a bisa doka kan wadannan shafukan labaran karya da ke yaudarar al’umma suke kuma neman bata mana suna.