Hattara dai: Abin jiya na neman dawowa
A farkon wannan mako ne aka kama wani matashi mai suna Nathaniel Samuel wanda ya shiga da wasu abubuwa masu fashewa cikin cocin ‘Living Faith’ da ke Sabon Tasha a Kaduna, amma Allah Ya taimaka bai samu damar cimma burinsa na tayar da nakiyar ba. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya bayyana […]
A farkon wannan mako ne aka kama wani matashi mai suna Nathaniel Samuel wanda ya shiga da wasu abubuwa masu fashewa cikin cocin ‘Living Faith’ da ke Sabon Tasha a Kaduna, amma Allah Ya taimaka bai samu damar cimma burinsa na tayar da nakiyar ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya bayyana cewa jami’an tsaron da ke aiki a cocin ne suka kama wannan matashin a yayin da ya shiga cocin da jaka mai dauke da nakiya.
An ce jami’an tsaron sun tsargu da take-taken Nathaniel ne ganin ya shiga cocin da jaka kuma sai ya shiga ban-daki ya dade, daga nan suka kai masa samame suka kama shi kafin ya kai ga aikata mummunan aikin.
A yankin Arewacin Najeriya an fara samun tayar da bam ne a ranar 18 ga watan Janairun 1996, lokacin da wani ya tayar da bam a ban-daki na otel din Durbar da ke Kaduna da misalin karfe hudu na yammacin wannan ranar, sai dai shi ma ya yi rashin sa’a, domin shi kadai ne ya rasa ransa.
Ashe-ashe an fara ke nan, kodayake an dauki tsawon lokaci ba a sake samun rahoton tayar da bam ba, amma a watan Disamban shekarar 2010 an tayar da bam a Jos fadar Jihar Filato, bayan tayar da bam a Dandalin Eagles da ke Abuja a ranar 1 ga Oktoban 2010. Sannan a shekarar 2011 a cikin watan Disamba an tayar da bam a wani coci da ke garin Madalla a Jihar Neja, inda aka kashe mutane da yawa. Daga nan lamarin sai karuwa ya rika yi.
Da farko an rika tayar da bam din a coci-coci ne, sai kuma aka koma ana tayar wa a masallatai kanana da manya, ciki har da Babban Masallacin Juma’a na cikin birnin Kano wanda aka tayar da bama-bamai a lokacin Sallar Juma’a a ranar 28 ga watan Nuwamban shekarar 2014, inda aka rasa dimbin rayuka tare da jikkata mutane masu yawa.
Bayan ga wuraren ibada, wadannan mugayen sun kuma rika tayar da bama- bamai a tashoshin mota, mafi muni shi ne wanda aka tayar a tashar mota ta Nyanya da ke birnin Abuja da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014.
Wato dai idan an lura za a ga cewa masu mugun nufin sun fi tayar da bama- baman ne a wuraren taruwar jama’a, kamar masallatai da coci-coci da tashoshin mota da sauransu, suna yin haka ne da nufin haifar da rudani yadda za a tayar da fitina a tsakanin mabiya addinai ko a tsakanin kabilu, domin su cimma burinsu na tarwatsa kasar nan.
A sakamakon wadannan tashe-tashen bama-baman dole sai da ya kasance duk inda mutane za su shiga sai an rika caje su da kayansu, hatta a wuraren ibada haka za ka ga mutane sun yi layi ana caje su kafin su shiga wurin ibadar tasu. Haka abin yake a tashoshin mota da na jiragen sama da sauran wurare.
Masu burin tarwatsa kasar nan suna ganin ta hanyar addini da kabilanci da bangaranci ne za su iya cimma burinsu, shi ya sanya suka himmatu wajen kashe bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba, domin kawai suna son su cimma wani buri nasu na cusa kiyayya a tsakanin jama’a.
A gaskiyar magana babu wani Musulmin kirki ko Kirista na kwarai da zai hallaka mutane haka kawai, domin babu wani addini da ya koyar da haka a tsakanin addinan biyu.
Wannan abu da ya faru a Sabon Tasha zai sanya a koma gidan jiya, a rika takura wa mutane a duk inda suka shiga, a koma ana tsoron juna, kowa bai yarda da kowa ba.
Saboda haka kowa sai ya kara kulawa sosai, duk abin da aka gani ba a amince da shi ba a yi kokarin sanar da jami’an tsaro, kuma a guji daukar doka a hannu, a rika kyale jami’an tsaro suna yin aikinsu.
Allah Ubangiji Ya kare mu daga sharrin wadannan mugayen mutane, Ya kuma zaunar da kasarmu Najeriya lafiya da sauran kasashen duniya.