Hattara dai ’yan Arewa
Yanzu dai an yi walkiya a yankin Arewacin kasar nan kowa ya ga matsayin kowa, saboda haka nan sai jama’a su san dangantakarsu da wadanda suke gani su ne za su agaza masu ficewa daga kangin ukubar da suke ciki sakamakon sayar da mutuncinsu da wasu tsoffin shugabanninsu suka yi ga ‘yan Kudu. Duk da […]
Yanzu dai an yi walkiya a yankin Arewacin kasar nan kowa ya ga matsayin kowa, saboda haka nan sai jama’a su san dangantakarsu da wadanda suke gani su ne za su agaza masu ficewa daga kangin ukubar da suke ciki sakamakon sayar da mutuncinsu da wasu tsoffin shugabanninsu suka yi ga ‘yan Kudu. Duk da mawuyacin halin da ake ciki, wasu shugabannin ko gezau, hasali ma kokari suke yi su kara dulmuya jama’a cikin wata sabuwar matsalar. Burinsu shi ne dorewar gwamnatin da talakawa ke kuka game da ita, don rashin dacewarta da wanzar da al’amuran kasar nan da kuma lusarancin shugabanninta, wadanda ba su san ya kamata ba, ba su kuma damu da irin kisan kiyashin da ake yi wa wasu jama’arsu ba sakamakon ta’addanci da suka ki magancewa.
Baicin tsananin matsi da kuncin rayuwar da suka addabi al’umman yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan har suka daidaice, suka fantsama cikin uwa duniya neman matsuguni a wuraren da ba su saba ba, sai kuma ga wata sabuwar fitina ta kunno masu kai game da rashin yiwuwar yin zabubbuka masu zuwa zuwa tare da su. Kaman yadda hukumar zabe ta bayyana hakan ba zai yiwu ba sai idan an yi gyara ga dokokin zabe da suka hana mutum yin zabe a wani wuri dabam da inda ya yi rajista. To me hukumar zabe ke yi don ganin ba a yi wa wadanan mutanen sakiyar da ba ruwa ba, suna ji, suna gani, a yi zabe ba su?
Akwai dabaru biyu da za a iya bi don magance wannan babbar matsalar: ta fako ita ce tabbatar da cewa hukumar zabe ta gaggauta yin gyara ga sashen dokokin zabe da ya haramta wa wadannan mutane yin zaben, na biyu kuma shi ne majalisa ta hanzarta zartar da kudurin cewa ana iya ba irin wadannan mutanen daman jefa kuri’a a duk inda suka kasance domin kuwa lalura ce ta kawo haka. Tashin-tashina, walau ta siyasa ce, ko dambarwar kabilanci da bambancin addini abubuwa ne da suka zama ruwan dare, babu shiyyar ba alamarsu. Sa’anan kuma abin da duk ya yi farko zai yi karshe, saboda haka nan ana iya cewa kafin nan da zabubbuka masu zuwa tashin hankali a ko ina a fadin tarayyar Najeriya zai iya zama tarihi.
Amma idan har ana son takura wa jama’ar Arewa, a hana su rawar gaban hantsi kafin zuwan zabe, ko kuma a ki sakar musu mara don fitsArewa a lokutan da ake zaben, to fa ba za a so a ga karshen kwaramniyar da ke faruwa yanzu haka ba a wasu sassan Arewar, domin kuwa makiya zaman lafiya da rashin kaunar ‘yan Arewa da wani abin alheri za su kai gwauro, su kai mari, don ganin abubuwan asshan da ke faruwa a Arewa sun ja geza, har zuwa lokutan zaben don hakan ya bayar da damar daukar matakan tsorata jama’a kada su firfito a wuraren da jam’iyyar gwamnati ta tabbatar ba za ta yi galba ba. Wannan dai ba sabon abu ne ba, domin kuwa hakan ya faru a wasu muhimman wurare a Arewa, inda aka tayar da yamutsin da ya jawo hasarar rayuka da dukiya don dai kawai daga bisani a tura dubban jami’an tsaron domin tsorata jama’a har suka firgice, da yawa kuma suka gigice, suka gwammace su yi zamansu a gidajensu, don gudun kada a dirka musu dalma a banza, a wofi.
Shi ya sa ake ganin cewa tun da sanyin safiya ne ake son cusa batun rashin zaman lafiya a zukatan jama’a don idan lokacin zabe ya zo ba wanda zai yi mamaki idan an dauki tsauraran matakan da za su kai talakawa kaurace wa tasoshin jefa kuri’a. Shugabannin jam’iyyar da ke da gwamnatin tarayya da kuma na jihohi fiye da 20 sun fahimci irin raunin da wadannan gwamnatocin ke da shi da kuma yadda jama’a suka juya musu baya dangane da haka. Ashe kuwa tilas ne su dukufa wajen hana zabe gudana yadda ya kamata a wuraren da suka san jam’iyyarsu za ta sha da kyar ta hanyar biye wa munanan manufofin da za su hana zaman lafiya da lumana a wuraren don ta ji dadin hada kai da baki da jami’an tsaro da kuma malaman zabe wajen tsorata mutane don aikata magudi cikin ruwan sanyi.
Akwai hanyoyi da dabaru da yawa na cusa tsoro a zukatan masu jefa kuri’a, wadanda ba sai an tsaya ana rattaba su ba, kowa ya sansu. Akwai kuma hanyoyin da ake bi wajen sanyaya gwiwowin masu jefa kuri’a wadanda da wuya a fahimce su. daya daga cikinsu ita ce wacce aka yi amfani da ita a zaben shugaban kasa na 2011, inda aka shiga yada farfagandar karya a gidajen rediyon gida da waje, ana cewa wasu masu jefa kuri’a a sassan Arewa sun fusata game da sakamakon da ya biyo bayan zabubbukan da suka gabata kafin na shugaban kasa, saboda haka nan sun zucciya, ba su yi zabe ba a wannan karon, sun kokkona takardunsu na jefa kuri’a. An kuma nuna cewa wasu kuma sun ce fitowarsu don zaben wanda ransu ke so ba ta da wata amfani don ba a aiki da sakamakon zaben. Ta haka ne aka hure wa jama’a da yawa kunnuwa, suka kuma yarda, suka ki jefa kuri’a a zaben gwamnoni da na shugaban kasa a 2011.
To, amma baicin haka nan kuma shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar mukamai daban-daban daga Arewa ba su damuwa wajen ganin cewa sun fadakar da jama’a game da muhimmancin firfitowa birjik don jefa kuri’a, domin kuwa a ranar zabe masu fitowa ‘yan kalilan ne, wadanda ba su kai ko rubu’in wadanda aka yi wa rajistar ba. Dalilin haka kuwa shi ne ba wanda za a ce ya ci zaben majalisa sai da yawun gwamnan jiharsa, saboda haka ne suke shantakewa wajen buga wa masu zabe kaimi, domin sun san dole ne hakarsu ta cimma ruwa. Irinsu ne kuma ke zame wa ‘yan amshin shatar gwamnati mai ci a majalisa, duk kuwa da cewa daga jam’iyyar adawa suke.
Samun nasara a harkar zabe, ko samun sukunin inganta hanyoyin gudanar da shi a jihohin Arewa ya dogara ne ga ‘yan siyasa da shugabanninsu, musaman ‘yan takara, wadanda tilas ne su kasance masu tsananin kishin wadanda suka zabe su, ba wadanda za su zame kajin da za su ci, su goge bakinsu ba. Yanzu ne lokacin da ‘yan siyasan Arewa za su farka, su tashi daga barci mai nauyi don su hada kai, su furta da murya guda wajen sukar lamirin tsare-tsaren da ake yi don wargaza Arewa da daidaita al’ummanta.Yanzu dai an yi walkiya a yankin Arewacin kasar nan kowa ya ga matsayin kowa, saboda haka nan sai jama’a su san dangantakarsu da wadanda suke gani su ne za su agaza masu ficewa daga kangin ukubar da suke ciki sakamakon sayar da mutuncinsu da wasu tsoffin shugabanninsu suka yi ga ‘yan Kudu. Duk da mawuyacin halin da ake ciki, wasu shugabannin ko gezau, hasali ma kokari suke yi su kara dulmuya jama’a cikin wata sabuwar matsalar. Burinsu shi ne dorewar gwamnatin da talakawa ke kuka game da ita, don rashin dacewarta da wanzar da al’amuran kasar nan da kuma lusarancin shugabanninta, wadanda ba su san ya kamata ba, ba su kuma damu da irin kisan kiyashin da ake yi wa wasu jama’arsu ba sakamakon ta’addanci da suka ki magancewa.
Baicin tsananin matsi da kuncin rayuwar da suka addabi al’umman yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan har suka daidaice, suka fantsama cikin uwa duniya neman matsuguni a wuraren da ba su saba ba, sai kuma ga wata sabuwar fitina ta kunno masu kai game da rashin yiwuwar yin zabubbuka masu zuwa zuwa tare da su. Kaman yadda hukumar zabe ta bayyana hakan ba zai yiwu ba sai idan an yi gyara ga dokokin zabe da suka hana mutum yin zabe a wani wuri dabam da inda ya yi rajista. To me hukumar zabe ke yi don ganin ba a yi wa wadanan mutanen sakiyar da ba ruwa ba, suna ji, suna gani, a yi zabe ba su?
Akwai dabaru biyu da za a iya bi don magance wannan babbar matsalar: ta fako ita ce tabbatar da cewa hukumar zabe ta gaggauta yin gyara ga sashen dokokin zabe da ya haramta wa wadannan mutane yin zaben, na biyu kuma shi ne majalisa ta hanzarta zartar da kudurin cewa ana iya ba irin wadannan mutanen daman jefa kuri’a a duk inda suka kasance domin kuwa lalura ce ta kawo haka. Tashin-tashina, walau ta siyasa ce, ko dambarwar kabilanci da bambancin addini abubuwa ne da suka zama ruwan dare, babu shiyyar ba alamarsu. Sa’anan kuma abin da duk ya yi farko zai yi karshe, saboda haka nan ana iya cewa kafin nan da zabubbuka masu zuwa tashin hankali a ko ina a fadin tarayyar Najeriya zai iya zama tarihi.
Amma idan har ana son takura wa jama’ar Arewa, a hana su rawar gaban hantsi kafin zuwan zabe, ko kuma a ki sakar musu mara don fitsArewa a lokutan da ake zaben, to fa ba za a so a ga karshen kwaramniyar da ke faruwa yanzu haka ba a wasu sassan Arewar, domin kuwa makiya zaman lafiya da rashin kaunar ‘yan Arewa da wani abin alheri za su kai gwauro, su kai mari, don ganin abubuwan asshan da ke faruwa a Arewa sun ja geza, har zuwa lokutan zaben don hakan ya bayar da damar daukar matakan tsorata jama’a kada su firfito a wuraren da jam’iyyar gwamnati ta tabbatar ba za ta yi galba ba. Wannan dai ba sabon abu ne ba, domin kuwa hakan ya faru a wasu muhimman wurare a Arewa, inda aka tayar da yamutsin da ya jawo hasarar rayuka da dukiya don dai kawai daga bisani a tura dubban jami’an tsaron domin tsorata jama’a har suka firgice, da yawa kuma suka gigice, suka gwammace su yi zamansu a gidajensu, don gudun kada a dirka musu dalma a banza, a wofi.
Shi ya sa ake ganin cewa tun da sanyin safiya ne ake son cusa batun rashin zaman lafiya a zukatan jama’a don idan lokacin zabe ya zo ba wanda zai yi mamaki idan an dauki tsauraran matakan da za su kai talakawa kaurace wa tasoshin jefa kuri’a. Shugabannin jam’iyyar da ke da gwamnatin tarayya da kuma na jihohi fiye da 20 sun fahimci irin raunin da wadannan gwamnatocin ke da shi da kuma yadda jama’a suka juya musu baya dangane da haka. Ashe kuwa tilas ne su dukufa wajen hana zabe gudana yadda ya kamata a wuraren da suka san jam’iyyarsu za ta sha da kyar ta hanyar biye wa munanan manufofin da za su hana zaman lafiya da lumana a wuraren don ta ji dadin hada kai da baki da jami’an tsaro da kuma malaman zabe wajen tsorata mutane don aikata magudi cikin ruwan sanyi.
Akwai hanyoyi da dabaru da yawa na cusa tsoro a zukatan masu jefa kuri’a, wadanda ba sai an tsaya ana rattaba su ba, kowa ya sansu. Akwai kuma hanyoyin da ake bi wajen sanyaya gwiwowin masu jefa kuri’a wadanda da wuya a fahimce su. daya daga cikinsu ita ce wacce aka yi amfani da ita a zaben shugaban kasa na 2011, inda aka shiga yada farfagandar karya a gidajen rediyon gida da waje, ana cewa wasu masu jefa kuri’a a sassan Arewa sun fusata game da sakamakon da ya biyo bayan zabubbukan da suka gabata kafin na shugaban kasa, saboda haka nan sun zucciya, ba su yi zabe ba a wannan karon, sun kokkona takardunsu na jefa kuri’a. An kuma nuna cewa wasu kuma sun ce fitowarsu don zaben wanda ransu ke so ba ta da wata amfani don ba a aiki da sakamakon zaben. Ta haka ne aka hure wa jama’a da yawa kunnuwa, suka kuma yarda, suka ki jefa kuri’a a zaben gwamnoni da na shugaban kasa a 2011.
To, amma baicin haka nan kuma shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar mukamai daban-daban daga Arewa ba su damuwa wajen ganin cewa sun fadakar da jama’a game da muhimmancin firfitowa birjik don jefa kuri’a, domin kuwa a ranar zabe masu fitowa ‘yan kalilan ne, wadanda ba su kai ko rubu’in wadanda aka yi wa rajistar ba. Dalilin haka kuwa shi ne ba wanda za a ce ya ci zaben majalisa sai da yawun gwamnan jiharsa, saboda haka ne suke shantakewa wajen buga wa masu zabe kaimi, domin sun san dole ne hakarsu ta cimma ruwa. Irinsu ne kuma ke zame wa ‘yan amshin shatar gwamnati mai ci a majalisa, duk kuwa da cewa daga jam’iyyar adawa suke.
Samun nasara a harkar zabe, ko samun sukunin inganta hanyoyin gudanar da shi a jihohin Arewa ya dogara ne ga ‘yan siyasa da shugabanninsu, musaman ‘yan takara, wadanda tilas ne su kasance masu tsananin kishin wadanda suka zabe su, ba wadanda za su zame kajin da za su ci, su goge bakinsu ba. Yanzu ne lokacin da ‘yan siyasan Arewa za su farka, su tashi daga barci mai nauyi don su hada kai, su furta da murya guda wajen sukar lamirin tsare-tsaren da ake yi don wargaza Arewa da daidaita al’ummanta.