Hattara dai ’yan siyasa malaman addinin kasar nan

A `yan kwanakinnan jaridun kasar nan suna ta dauko labaran irin yadda gwamnatin tarayya PDP ta ke ta rabon makudan biliyoyin Nairori ga Maluman addinan kasar nan (Musulmi da Kirista) da aniyar ganin su da magoya bayansu sun taimaka wa dan takarar neman shugabancin kasarta shugaba Goodluck Jonathan a cikin babban zaben wannan watan, ta […]

Hattara dai ’yan siyasa malaman addinin kasar nan
Hattara dai ’yan siyasa malaman addinin kasar nan

A `yan kwanakinnan jaridun kasar nan suna ta dauko labaran irin yadda gwamnatin tarayya PDP ta ke ta rabon makudan biliyoyin Nairori ga Maluman addinan kasar nan (Musulmi da Kirista) da aniyar ganin su da magoya bayansu sun taimaka wa dan takarar neman shugabancin kasarta shugaba Goodluck Jonathan a cikin babban zaben wannan watan, ta yadda zai kai ga nasarar lashe zaben. Gwamnan Jihar Ribas Cif Rotimi Amaechi, kuma Darakta Janar na yakin neman zaben dan takarar neman shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, shi ya fara zargin cewa gwam natin tarayya ta bayar da tsabar kudi har Naira biliyan shida ga kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato CAN, da aniyar `ya`yanta su taimaka wa shugaba Jonathan.

Fallasa haka ke da wuya sai shugabancin kungiyar ta CAN na kasa ya ce sam-sam ba ta da masaniyar haka, sannan ta nisanta kanta da faruwar wannan badakala. Amma kuma `yan kwanaki kadan da kungiyar ta CAN ta musanta zargin, sai ga Fasto Kallamu Musa Dikwa, wanda ya ke Babban Darakta na Muryar Kiristocin Arewa, ya taso takanas ta Kano daga Maiduguri ya zo Kaduna, inda ya gana da Manema labarai, ya tabbatar wa da duniya cewa tabbatas an ba shugabannin kungiyar ta CAN, wadancan kudi da ya ce Naira biliyan bakwai ne, ba Naira biliyan shida ba, kamar yadda Gwamnan Jihar Ribas din ya fadi ba.Makasudin bayarwar in ji shi, shi ne don kungiyar ta taimaka wa shugaba Jonathan ya kai ga nasara a zabe mai zuwa.
Fasto Kallamu Dikwa da ya fadawa taron manema labaran cewa tun a ranar 26 ga watan Janairun da ya gabata aka ba CAN din wadancan kudade, kuma tuntuba da ya yi ta yi tsakanin rassan kungiyar ya tabbatar masa da cewa kowane reshen jiha an ba shi Naira miliyan uku-uku, har ya kara da cewa ya samu tabbacin rassan jihohin Neja da Jigawa da Sakkwato, akan sun karbi nasu kason. Babban Daraktan Muryar Kiristocin Arewan ya fadi cewa tun da ya fallasa wannan al`mundahana wasu Kiristoci suka yi ca… akansa, wasu na cewa bai kyauta ba, kai karewa ma da karau har barazanar daukar ransa an yi. Ya ce wasu cewa suka yi Janar Buhari ya ke wa kamfen. Ya ce ba daya, shi babban abin da ya dame shi yanzu shi ne, irin yadda ake kashe mutanensu barkatai a kulli yaumin, dadin-dadawa harkokin yau da kullum na kasa na kara tabarbarewa, abubuwan da suka sanya shi a yanzu ba wani dan takara da ke gabansa.
Daga bangaren kungiyoyin musulmi kuwa a shiyyar Arewa maso yamma akwai zargi mai karfi cewa ganawar da Mataimakin shugaban kasa Alhaji Namadi Sammbo ya yi da wasu wakilan kungiyoyin addinin Islama da Limamai da makamantansu da aka ce sun kai 3,500, a Kaduna, batun ba da kudin da sunan su taimaka wa shugaba Jonathan a wannan zabe shi ma ya bayyana, inda ya zuwa yanzu ake zargin cewa an ba mahalarta taron daga N5,000 zuwa N25,000, gwargwadon irin kimar da kowane Malami ya ke da ko Limami ya ke da ita.
A cikin martaninsa na zargin an basu wadancan kudi, Ustaz Musa Yusuf Asadus Sunnah daya daga cikin Maluman da suka halarci wancan taro na Kaduna, ya musanta afkuwar hakan yana mai cewa muddin masu kagen, ba su yi bayani ba sun cuci Musulmi. Ya tabbatar da cewa shi abin da ya sani shi ne, a wajen taron an umurcesa da ya gabatar da kasida akan “Hakkin mabiya akan shugabanni da hakkin shugabanni akan mabiya,” abin da ya ce ya gabatar da abin da Allah Ya sanar da shi. Amma sai ga shi ana ta yamadidin an samai tsabar kudi har Naira miliyan 20,a but din motarsa a zaman nasa kason. Akan zargin an ga mahalarta taron suna layi ana ba su kudin sai ya ce ai layin na cin Karin kumallon safe ne da aka ba mahalarta taron.
Shi kuwa Sheikh Sani Yahaya Jingir shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jam`atu Izalatil Bid`ah Wa Ikamatis Sunnah na kasa baki daya cewa ya yi Malamai da Limamai da `yan kugiyoyin da suka halarci taron da mataimakin shugaban kasa a Kaduna sun yi abin kunya, kuma ba su yi amfani da karatun baya ba, wanda ya ce da sun yi, da ba su halarci taron ba. Don kuwa a fadarsa “Da mutanen da suka karbi kudin wannan gwamnatin a baya sun yi tunani da a wannan karon ba su sake karbar kudin gwamnatin da ke kashe mutane take kuma lalata kusan komai na kasar nan.” Malamin ya nuna damuwarsa da irin Malaman da gwamnatin suke turawa zuwa kasa mai tsarki, da sunan su yi mata rokon Allah Ya sa ta ci gaba da mulkin. Ya bayyana Malamai da Limamai da Sarakunan addinin Islama da suka shige gaba akan lallai sai Gwamnatin Jonathan ta ci gaba da mulki a zaman makwadaita. Mai yiwuwa kauce wa wannan kwadayi da neman tsira da mutuncinsu ya sanya mutane irin su Sheikh Jingir da Dokta Sheikh Ahmed Abubakar Gumi da Sheikh Sanusi Khalid da makamantansu, suka kauracewa wancan taron da yanzu irin wannan yamadidi da Allah wadai tir ke binsa.
Daga can shiyyar Kudu maso Kudu kuwa (shiyyar da ta kunshi `yan kabilar Yarbawa), ya zuwa yanzu ta tabbata cewa Maluma da Limaman da kungiyoyin shiyyar na addinin Islama da aka gayyata don irin wancan taro na Kaduna da Shugaba Jonathan ba su halarci taron ba da aka so yi a babban Masallaci kungiyar Ansarudeen da ke Ajao Surulere Legas a ranar Lahadin da ta gabata ba. Daga cikin hanzarin da aka ce jagororin Musulmin shiyyar suka bayar bayan tattaunawar da suka yi ta waya da babban Sakataren Majalisar koli mai kula da harkokin addinin Musulunci Farfesa Ishak Oloyede, cewa suka yi wani babu dalilin da zai sa su gana da Shugaba Jonathan a irin wannan lokaci da ya rage yan makonni kadan a yi babban zabe, alhali a baya sun nuna masa damuwarsa akan irin kwarar da aka yi wa Musulmi a taron kasa akan yawan Wakilai, koken da ya ce zai duba, amma har aka kammala taron bai duba ba. Haka batun nada mutane akan manyan mikamai, in da musulman suka nuna kwarar da aka yi masu. Shi ma shugaban ya ce zai duba, amma ya yi biris da batun. Dadin-dadawa sun ce halartar taron zai iya hada su da musulmin Arewa da suka kaurace wa taron. Nepotism
Komai gaskiya ko rashin gaskiyar Gwamnati Jonathan na raba kudin fitar hankali ga kungiyoyin addinan kasar nan da aniyar su mara mata baya a wannan lokaci, ko kadan bai dace ba a ce ana samun haka daga Maluman addinan kasar nan, wadanda suke mafi daukaka a cikin kowace al`umma a koda wane lokaci kamar yadda Hadisin Manzo SAW ya ce “Malamai magada Annabawa.” Ya kamata Maluman addinan kasar nan su gane cewa wadanda suka koma Malaman gwamnati a kullum rasa mabiya suke yi fiye da yadda suke tsammani, al`amarin da ke kara muzanta da kaskantar da su a idanun duniya, baya ga abin da za su taras a gobe kiyama. Babu laifi Maluman addinai su kusanci masu mulki don su fada musu gaskiya, amma ba su tare gindinsu ba, ta yadda ba sa iya fada musu gaskiya. Don haka Hattara dai Maluman addinai, ku kiyayi aikin dana sani da ku ke mabiyanku hudubar su kauce masa.