Hattara Gwamnatin Jigawa

Ginin Asibitin Kwararru  da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi a Karamar Hukumar Hadeja mun ji gwamnatin na ikirarin aikin an cimma kashi 70 cikin 100. Sai dai kuma idan ka je ka gani da idanunka aikin bai kai kashi 70 da gwamnati ke ikirari ba. Gwamna Badaru ya dauki alkawarin gina asibitin ne  tun a […]

Hattara Gwamnatin Jigawa
Hattara Gwamnatin Jigawa

Ginin Asibitin Kwararru  da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi a Karamar Hukumar Hadeja mun ji gwamnatin na ikirarin aikin an cimma kashi 70 cikin 100. Sai dai kuma idan ka je ka gani da idanunka aikin bai kai kashi 70 da gwamnati ke ikirari ba.

Gwamna Badaru ya dauki alkawarin gina asibitin ne  tun a wa’adin mulkinsa na farko. Ba a fara gina asibitin ba sai da Sanatan Shiyyar Hadeja wato Jigawa ta Gabas na lokacin ya fito fili ya soki gwamnati game da alkawarin da ta dauka na gina asibitin. Daga bisani Gwamna Badaru ya fito fili ya bayyana wa duniya cewa magauta ne suka hana shi aiki a jihar, wanda bayan wadannan kalamai ne aka fara aikin asibitin . Sai kuma tafiyar hawainiya ta zo ta dabaibaye aikin daga baya.

Lokacin Gwamna Ibrahim Saminu Turaki gwamnatin jihar ta fara gina kamfanin sukari a Karamar Hukumar Hadeja, wanda har ya bar mulki ba a kammala aikin ba.

Gwamna Sule Lamido kuma maimakon ya karasa aikin kamfanin sai ya sayar da shi. A halin yanzu kamfanin ya zama kango domin wadanda aka sayar wa kamfani sun watsar da shi.  Saboda haka muke tsoron kada Asibitin Kwararru ya bi sahun kamfanin sukari, domin ‘yan adawa abin da suke fadi tun bara shi ne ba wani asibiti da za a gina, wai tashar mota ce  dama ake so a yi sabuwa.

Jam’iyyar APC na yi don haka ba na fata a ce yau gwamnatin APC ta gaza ta kowane fanni. Gwamna Badaru muna addu’ar Allah Ya ba ka ikon cika alkawurran da ka dauka.

Nasiru Kainuwa Hadeja

08100229699