Hattara: Jabun kudade sun bazu a gari —CBN

CBN ya sanar cewa hukuncin daurin shekara biyar na jiran duk wanda aka kama da jabun kudade

Hattara: Jabun kudade sun bazu a gari —CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ja hankalin ’yan Najeriya kan jabun takardun kudin kasar da ke yawo a cikin al’umma a sakamakon rade-radin da ake yadawa na karancin tsabar kudi.

Kakakin CBN, Hakama Sidi Ali ta shawarci al’umma da su kasance masu lura ganin cewa masu jabun kudade na amfani da su a matsayin kudin mota ko a wurin yin cefane da gidajen abinci sauransu.

Sanarwar ta CBN ta ce “Dokar CBN ta tanadi hukucin daurin akalla shekaru biyar ga duk wanda ya buga jabun kudade.

“CBN na aiki da hukumomin tsaro da na hadahadar kudade wajen ganowa da kwace jabun kudade da kuma tsare masu buga su.” in ji jami’ar.

Daga nan sa ta umarci bukaci bankuna, ’yan canji da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade da su dauki matakan da suka dace wajen ganowa da kuma hana yaduwar jabun kudade.

Ta kara da cewa, “ana kira ga jama’a su kai karar duk wanda suka ga yana yin jabun kudade ga ofishin yan sanda ko na CBN mafi kusa.

‘Yar China na fuskantar saki bayan ta haifi jariri baƙar fata

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna