Hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kashi 34.60 a Nuwamba — NBS
Wannan na nufin an samu ƙarin 0.72 daga kashi 33.88 da aka samu a watan Oktoban 2024.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa, hauhawar farashi a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 34.60 a watan Nuwamban 2024.
Wannan na nufin an samu ƙarin 0.72 daga kashi 33.88 da aka samu a watan Oktoban 2024.
- Abba ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni ga majalisar dokokin Kano
- Boka ya shiga hannu kan sace tifa
Idan aka kwatanta da watan Nuwamban 2023, lokacin da hauhawar farashi ya kasance 28.20, a wannan shekarar an samu ƙarin 6.40.
Rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyaki sun tashi sosai a Nuwamba 2024, idan aka kwatanta da watan Nuwamban 2023.
Duk da haka, idan aka duba hauhawar farashin a kowane wata, hauhawar farashin a Nuwamba 2024 (2.638) ya yi ƙasa kaɗan da wanda aka samu a watan Oktoba 2024 (2.640).
Hauhawar farashin kayan abinci ya tashi zuwa 39.93
Hauhawar farashin kayan abinci ya tashi, wanda hakan ke nuni da kayan sun yi tsada zuwa kashi 39.93 a watan Nuwamba 2024, daga 32.84 a watan Nuwamba 2023.
Wannan ƙarin ya shafi kayayyakin kamar su ayaba, masara, shinkafa, manja, da man gyaɗa.
A kowane wata, farashin kayan abinci yna tashi da kashi 2.98 a watan Nuwamba 2024, wanda ya ƙaru kaɗan daga kashi 2.94 a watan Oktoba.
Kayayyakin da suka tashi sun haɗa da kifi, shinkafa, ayaba, madara, madarar shanu, nama, kaza da sauransu.
Matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekara
Matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekaru 12 wanda ya ƙare a watan Nuwamba 2024 ya kai kashi 38.67.
Wannan na nufin an samu ƙarin kashi 11.58 idan aka kwatanta da matsakaicin hauhawar da aka samu a cikin shekarun 12 da suka gabata, wanda ya kasance 27.09 a watan Nuwamban 2023.