Hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba — NBS
A cewar rahoton hukumar farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.57, idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta.
A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.57, idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
- Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan
- Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF
Ragin na zuwa ne sakamakon saukar farashin kayayyakin abinci kamar masara, garri, wake, gero, dankali, albasa, kwai, tumatir, da barkono.
Haka kuma, an bayyana cewa matsakaicin karin farashin kayan abinci na watanni 12 wanda ya ƙare a watan Satumban 2025, ya kasance a kashi 24.06, wanda ya ragu da maki 13.47 idan aka kwatanta da Satumban 2024 (37.53).
“Saukar farashin kayan abinci a watan Satumban 2025 ya kasance a kashi 16.87, idan aka kwatanta da kashi 37.77 a watan Satumban 2024, wato an samu ragi da maki 20.9.”
An kuma bayyana cewa matsakaicin hauhawar farashin kaya gaba ɗaya, ya ragu zuwa kashi 18.02 a watan Satumban 2025 daga kashi 20.12 a watan Agustan 2025.
“Idan aka kwatanta da watan Agusta, hauhawar farashin kayayyaki na watan Satumba 2025 ya ragu da kashi 2.1. Idan kuma aka yi duba da shekara-shekara, ya ragu da maki 14.68 idan aka kwatanta da watan Satumba 2024 (32.70).”
“Wannan yana nufin cewa hauhawar farashin kayayayyki (shekara zuwa shekara) ya ragu a watan Satumban 2025 idan aka kwatanta da watan Satumban 2024, duk da cewa shekarar da ake amfani da ita wajen ƙididdiga ta bambanta.
“Amma idan aka duba wata-wata, hauhawar farashin kayayyaki a watan Satumban 2025 ya kasance 0.72, ƙasa da 0.74 da aka samu a watan Agustan 2025.
“Wannan ya nuna cewa hauhwar farashin kayayyaki a watan Satumba ya sauka idan aka kwatanta da ƙarin da aka samu a watan Agusta.”