Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru a Ghana

Gwamnatin Ghana ta alaƙanta matsalar da annobar Coronavirus.

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru a Ghana

Hukumar Kididiga ta Kasar Ghana ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 42.2 a watan Mayun da ya gabata, maimakon kashi 41.2 da yake a watan Afrilu.

Hukumar ta ce farashin kayayyakin ya ƙaru ne sakamakon ƙaruwar farashin kayan abinci zuwa kashi 52.4 cikin 100 adadi mafi yawa da ya taɓa kaiwa cikin watanni masu yawa.

Sauran abubuwan da suka haddasa hauhawar farashin, sun haɗa da tashin farashin gidaje da ruwa da wutar lantarki da man fetur.

Ƙasar Ghana na yunƙurin farfaɗowa daga hauhawar farashin kaya ne bayan da a watan Disamban bara ya kai kashi 54 cikin 100.

Iyalai da dama na fama matsin tattalin arziki a Ghana.

Gwamnatin ƙasar na alaƙanta matsalar da annobar Coronavirus da ta shafi duniya da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, to sai dai ’yan adawa na ganin laifin gwamnatin ƙasar ce.

A yanzu ƙasar na karɓar bashin Dala biliyan uku a ƙarƙashin wani shiri na shekara uku daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF).

Hakan na nufin gwamnatin ƙasar za ta gabatar da wasu tsaretsare masu tsauri domin bunƙasa kuɗin shigar ƙasar.

Shugaban ƙasar Nana Akufo Addo ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su yi haƙuri kasancewar taimakon IMF ba zai iya warware matsalolin da ƙasar ke fuskanta ba.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu