Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS

NBS ta ce an samu ƙarin hauhawar farashin ne sakamakon ƙaruwar buƙatar kayayyakin amfani a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 a watan Disamban 2024, daga kashi 34.60 da aka samu a watan Nuwamba.

Wannan ƙarin ya faru ne sakamakon ƙaruwar buƙatar kayayyakin amfani yau da kullum a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Idan aka kwatanta da watan Disamban 2023, an samu ƙarin kashi 5.87 a farashin kayayyaki, inda farashin a wancan lokacin yake a kashi 28.92.

Sai dai, idan aka duba ƙarin daga wata zuwa wata, farashin bai yi tashin gwauron zabi ba, inda aka samu kashi 2.44 a watan Disamba, ƙasa da kashi 2.64, inda aka samu a watan Nuwamba.

Tashin farashin kayan abinci ya fi yin ƙamari a wannan karon.

A shekara guda, farashin kayan abinci ya ƙaru da kashi 39.84 a watan Disamban 2024, idan aka kwatanta da kashi 33.93 da aka samu a Disamban 2023.

Wannan ya faru ne saboda ƙarin farashin kayan abinci kamar su doya, dankali, shinkafa, masara, da busashen kifi.

Duk da haka, tashin farashin kayan abinci ya ragu daga wata zuwa wata.

An samu kashi 2.66 a watan Disamba, idan aka kwatanta da kashi 2.98 a watan Nuwamba.

Wannan ragi ya samo asali ne daga ragin farashin wasu kayayyaki kamar giyar gargajiya, ruwan inibi, shinkafa, gero, da dankalin turawa.

Rahoton, ya kuma nuna cewa matsakaicin ƙarin farashin kayan abinci na shekara zuwa shekara ya tsaya a kashi 39.12 a 2024, wanda ya fi na 2023 (kashi 27.96) da kashi 11.16.