Haukan karya (A)
Wani mutum ne yana jin yunwa, bai da ko kwabo, sai ya samu inuwa ya zauna. Zuwa can sai wata Bafulatana ta zo za ta wuce, sai mutumin ya ce mata: “A damo min fura, a ciko kokon sosai. Da aka kawo fura ya sha ya rage, sai ya daga kokon sama ya wanke kansa […]
Wani mutum ne yana jin yunwa, bai da ko kwabo, sai ya samu inuwa ya zauna. Zuwa can sai wata Bafulatana ta zo za ta wuce, sai mutumin ya ce mata: “A damo min fura, a ciko kokon sosai. Da aka kawo fura ya sha ya rage, sai ya daga kokon sama ya wanke kansa da sauran furar sai ya kama yin dariya. Bafulatana ta ce: “Lafiya?” Sai ya ce: “Da sauki dai.” Da ta ga abin babu dama, ita ma sai ta ranta a na kare.
Abdul’aziz Maska, 07068549745