Hausa Da Hausawa (14)
Abin da za mu yi kila a nan domin daidaita tunani, shi ne mu kawo abubuwan da za su iya zama hujja game da ire-iren wadannan hasashe-hasashe da muka yi game da Hausa da Hausawa a doron kasa. Hanyoyin da kuma za su tabbatar da kafuwar wadannan hasashe-hasashe ko watsi da su su ne na […]
Abin da za mu yi kila a nan domin daidaita tunani, shi ne mu kawo abubuwan da za su iya zama hujja game da ire-iren wadannan hasashe-hasashe da muka yi game da Hausa da Hausawa a doron kasa. Hanyoyin da kuma za su tabbatar da kafuwar wadannan hasashe-hasashe ko watsi da su su ne na bin diddigin kalmomin da ke da dangantaka da na wasu harsunan da ke makwabtaka da Hausa da Hausawa ta fuskar al’adu da addini da adabi da sauran sassan zamantakewar yau da kullum.
Abu na farko da za mu soma dubawa shi ne bautar da Hausa da Hausawa suka yi a can da, daga kalmomin da suka ambata a cikin harshen nasu na jiya da kuma yau. Yawancin wadanda suka rayu a shekarun baya, ko kuma mu ce wadanda suka wanzu tsakanin shekarun 1960 zuwa 1970, suka kuma rayu cikin nishadin adabin Hausawa na baka sun saba da jin wakar nan da yara kan yi ‘rana, rana bude, bude, in yanka maki ragon (Sarki) ki sha jini, shar, shar!’ Wannan aikin adabi ya fiddo karara wani nau’i na rayuwar masu wannan harshe tun can da. Ba yadda za a yi yaran da ke irin wannan waka su mayar da hankali kan ta, har ta yi musu tasiri a wake, idan ba su sha bautar a nono ba. Ba dole ne sai sun yi bautar ba, ba kuma dole ne sai iyaye da kakanni sun yi bautar ba, amma a cikin tsawon tarihi da kwayar halitta kamar yadda muka gani a can baya, sun bibiyo irin wannan bautar, shi ya sa ’ya’ya da jikoki ke bayyana bautar ta hanyar wake.
Wani zai iya cewa ai kila haduwa da masu bautar rana ce daga baya ta sa Hausa da Hausawan da ke raye a lokacin suka ari tunanin suka gina shi a cikin wakokin bakansu. Wannan zai iya zama gaskiya, amma in aka yi la’akari da cewa ita bautar rana tana da nata muhalli na musamman da masana suka ajiye ta, za a iya cewa ba haduwa ba ce kurum ta kawo wannan tunani a cikin adabin bakan Hausawa, akwai alamun gado da kwayar halitta. Wace al’umma ce ta yi tashe a cikin wannan tada ta bautar rana a duniya? Daga binciken masana, bautar rana al’adar Yahudawa da Indiyawan dauri ne. Wasu masanan ma sun yi wa bautar rana taswira ta musamman da ta shafi tsakiyar Nahiyar Asiya da yankin da a yau ake cewa wa Gabas ta Tsakiya. Idan kuma muka koma ga bayanan da muka yi can baya game da asalin Hausa da Hausawa ta fuskar kwayar halitta za mu fahimci cewa asalin kakannin kakannin Hausa da Hausawa daga wadannan yankuna ne suka tusgo ko suka zauna na wani lokaci. Ke nan idan har an ga alamun bautar rana a cikin adabi da al’adun Hausawa na yanzu, bai rasa nasaba da wancan zama ko rayuwa.
Ba wannan kadai ba, wasu masu nazarin sun yi nuni da dangantakar da ke tsakanin Hausawa da Kibdawa ko Misirawan dauri ta fuskar bautar rana ko kuma ta ’yan uwantaka. Sun yi nuni da cewa kalmar /Rana/ tana da alaka da /Ra/, wadda ke nufin gunkin rana da ake bauta wa a wancan zamani. Haka kuma alamun mallaka a cikin Hausa da harshen Misirawan dauri duk iri daya ne, musamman /na/ da /ni/, ke nan ‘Rana’ na iya nufin ‘Gunkina’, haka ma a cikin Misirancin dauri ‘Ra-na’, gunkina yake nufi. Wannan ba aro ba ne, ba kuma saduwa ba ce, ba kasuwanci ba ne, dangantaka ce ta jini da kwayar halitta. Akwai karin kalmomi da dama da suka danganta Hausa da Misirancin dauri; /tuf/ na nufin zubar da miyau, haka ma a Hausa, /tuf/ zubar da miyau ne, abin da aka yi kuma ya zama /tofi/, shi ya sa Hausawa ke cewa ‘an yi masa tofin Allah tsine!’
Akwai kuma kalmar /atishawa/ a Hausa, ita ma tana da alaka da Misarawan dauri. Kamar yadda masu bincike suka nuna /shu/ ubangiji ne a Misiranci da /Atum/ ya halitta ta hanyar yin atishawa. Ke nan /shu/ iska ce da ake shaka da fitarwa. Shi /shu/ ubangiji ne mai alamu biyu, gunkin iska da na rana. A cikin Misirancin dauri /rana/ na nufin /art-t-shu/ wato idanun Shu. Wannan ya yi kama da kalmar nan ta Hausa /atishawa/, domin shi gunkin /Atum/ da ya halicci /Shu/ ta hanyar fitar da iska shi ne asalin atishawar da Misirawa da Hausawa ke yi. Haka kuma kalmomi irin su /nika/ da /kashi/ a Hausa suna da makamanta a Misirancin dauri, /nika/ ko /kas/. Ko /mutu/ a Hausa da /mut/ a cikin Misirancin dauri. Ko kuma /uwa/; mahaifiya, a Hausa da /ua/; gunkin haihuwa a Mirisancin dauri.
Duk wadannan misalai da ma wasu irin su da dama suna kara tabbatar da alakar Hausa da Hausawa da Masar ko Misirawa ko Kibdawan dauri ta fuskar bauta da kalmomi na gama-gari, kamar yadda muka bayyana a darussan baya. Ke nan idan an ga alamun bautar rana ko wata ko wani abu mai kama da gunki, ba wai ga Maguzanci za a tsaya ba kurum, sai an hada da asali da tushe ko kwayar halitta.
Ita kuwa bauta irin ta Maguzanci za a iya yi mata tata taswirar da wani zamani dab da karni na 14 ko 15, musammam zamanin da Larabawa suka sunno kai don ciniki da al’ummar da ke zaune a wannan yanki. Duk da cewa an ga alamun Larabawan a wannan yanki tun wajajen karni na 9 zuwa na 10, ana jin samuwar kalmar Maguzawa, ta somo ne daga karshen karni na 14 ko farkon karni na 15. Kamar yadda masana suka nuna a daidai wannan lokaci ne Larabawan suka hadu da al’umma da suke tsammanin ba su taba saduwa da aikakken sako ba, ko wani annabi daga cikin Annabawan Allah ko kuma dai ba su shaki addinin Allah ba. kila ma kamar yadda masana suka yi nuni ba su bautar komai sai rana ko wuta ko gumaka. Ana kuwa iya ganin irin haka daga kalaman irin wadannan al’umma ta hanyar karin maganganu ko hikimomin azanci irin su ‘duk bori daya ake wa tsafi’ ko kuma rantsuwar al’ummar irin ta ‘kwarankwatsi’ ko ‘aradu’ da makamantansu. Ke nan al’ummar da Larabawa suka iske ce mai bautar irin wannan bauta ta gumaka suka kasance /Majus/ ko /Magus/ ko /Majusawa/ ko kuma /Maguzawa/. Ko ma dai yaya, al’ummar wannan yanki ta fuskar bauta da kalmomin gado da ayyukan adabi, da alama zaunanniyar al’umma ce mai dadadden tarihi ta kowace fuska. Abin da kila ba a da masaniya kai shi ne yaushe ta zama kasar Hausa? Wa ya samar da ita a matsayin kasa? Al’ummar yankin ne ko kuwa baki ne da suka zo daga wani yanki na wajen kasar Hausa? Ko kuwa dai batun nan na Bayajidda yana da asali da tushe a rayuwar ginuwar Hausa da Hausawa?
Za mu ci gaba