Hausa Da Hausawa (15)
Wane ne kuma Bayajidda? Abin da kila ba a da masaniya a kai shi ne, yaushe wannan yanki da muke ciki ya zama kasar Hausa? Yaya ta kasance kasa guda alhali tana dauke da kasashe ko birane mabambanta? Wa ko me ya samar da ita a matsayin kasa? Al’ummar yankin ne asalinta ko kuwa baki […]
Wane ne kuma Bayajidda?
Abin da kila ba a da masaniya a kai shi ne, yaushe wannan yanki da muke ciki ya zama kasar Hausa? Yaya ta kasance kasa guda alhali tana dauke da kasashe ko birane mabambanta? Wa ko me ya samar da ita a matsayin kasa? Al’ummar yankin ne asalinta ko kuwa baki ne da suka zo daga wani yanki na wajen kasar Hausa? Ko kuwa dai batun nan na Bayajidda yana da asali da tushe a rayuwar ginuwar Hausa da Hausawa a doron kasa?
Na san wadanda suke biye da wannan tattaunawa zuwa yanzu sun fahimci wani abu game da yadda Hausa da Hausawa suka wanzu da kuma ginuwa a matsayin kasa ko al’umma. A cikin shekara dubu daya da 500 da suka wuce yankin kasar Hausa da Hausawa ya shiga cikin sabon yanayi da tsari da kila bayyana shi kai-tsaye zai iya kawo rudu, musamman ganin da ake yi yankin ya sha gamaden al’ummu da addinai da harsuna da cinikayya masu tarin yawa.
A can baya mun kawo takaitaccen bayani game da dauloli ko birane ko kasashen da aka tabbatar sun ginu a wannan yanki, musamman tsakanin karni na 8 zuwa na 16. Mun ga cewa tsakanin shekara ta 700 zuwa 1,100, yankin kasar Hausa cike yake da al’umma mabambanta tun daga yankin Arewacin Afirka har zuwa kasar Nupawa zuwa Gao da Jenne-Jeno kamar yadda wasu masana suka nuna. Abin da kuma ya kawo wannan dangantaka shi ne ciniki tsakanin Ibadawa da Kibdawan wancan zamani. Haka abubuwa suka ci gaba da wakana har zuwa kusan karni na 12, wato daga shekarar 1,100 lokacin da dakarun Almurabidun da tawagar Baba ko Buzaye suka amshe mulki da kasuwancin yanki, daidai lokacin da masarautan Fatimiyya ke mulkin kasar Masar.
Kamar kuma yadda masana suka nuna, tsakanin shekarar 1,100 zuwa 1,300 al’ummar Ibadawa da Kibdawa sun ba Habashawa da ke zaune a Ahir ko Sahel damar amshe harkar kasuwancin yankin, sun kuma shahara ne daga Ahir din har zuwa Kudu maso Yamma da Agades da sassan kasar Kano ta yanzu.
Saboda haka, domin kara jaddadawa, lallai yankin da ake ce da shi na kasar Hausa yanzu, yanki ne mai dauke da dauloli ko kasashe ko birane daban-daban tun da dadewa. Kamar yadda muka nuna, ita kasar ta Hausa tana dauke da wasu kasashe ko birane ne a cikinta da suke da tsari irin na jihohi da tarayya irin na yau. kasashen nan a warwatse suke, amma suna da alaka da juna ta fuskar bautar bayi da mulki da ciniki da saye da sayarwa.
Dangane da haka idan wasu masana ko masu nazari na ganin cewa wani wai shi Bayajidda ne asalin wannan yanki, to yaya za a yi da al’ummar Hausawa da suka kasance Kabbawa ko Kibdawa ko Gobirawa ko Gungawa ko Habashawa? Ko kuma ina za a saka al’ummar yankin da ta kasance Arna ko Kiristoci ko Maguzawa ko kuma Musulmi da ke zaune a wannan yanki kafin bullar wani wai shi Bayajidda?
Idan dai ana son tunani ya daidaita, tilas ke nan a bayyana wannan hadaka ta al’umma da addinai mabambanta da asalin Hausa da Hausawa a wannan yanki da yadda ta kasance tun azal. Ke nan kalmar Hausa da al’ummar Hausawa na nuni ne ga wadansu al’ummomi da suka rayu a wannan yanki cikin tsawon tarihi, wadanda kamar yadda masana suka nuna sun rayu kafin wani wai shi Bayajidda ya shigo cikin daula ko biranen kasar Hausa. Wadanne kasashe ne ake magana kai? Akwai Gobir da Gobirawa; akwai Kabbi da Kabbawa; akwai Santolo da Santolowa; akwai Pauwa da Pauwawa; akwai Wangara da Wangarawa; akwai Zamfara da Zamfarawa; akwai Zazzau da Zazzagawa; akwai Daura da Daurawa da wasu da dama kafin zuwan wani wai shi Bayajidda yankin kasar Hausa.
To amma me ya jawo aka dauki tarihihi ya zama tarihi ko mai alamar gaskiya? Me ya jawo aka mayar da kasar Hausa da biranenta suka kasance ‘sababbi’ alhali kuwa tsofaffi ne tun asali? Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne a gane cewa wannan ‘tarihi’ ko a cikin nazari ba a dauke shi a matsayin amsasshe ko karbabben batu ba. Yawanci an fi danganta shi da adabin baka, wata sa’a da tatsuniya, wata sa’a kuma da labaran masu karin gishiri; wata sa’a kuma abin nan da ake ce da shi kunne ya girmi kaka. Duk da irin wannan rauni da taririhin Bayajidda ya zo da shi; shi ne wai ya zo daga kasashen Gabas ya yi nasarar kafa kasashen Hausa Bakwai da Banza Bakwai, wasu mutane sun aminta da shi domin kuwa abu ne da ya dade yana bibiyar kafuwar kasar da al’ummarta, ta yadda yanzu wasu da dama sun dauki tarihihin a matsayin tarihi ko gaskiya.
Saboda haka abin da za mu yi a karashen wannan tattaunawa ta Hausa da Hausawa shi ne mu koma cikin kundin tarihi mu ga yaya aka yi wannan tarihihi ya bullo, me ya sa kuma ya yi tasiri a tunanin masana da manazarta asalin Hausa da Hausawa? Tambayar da za mu yi kokarin amsawa ita ce ko an taba yin wani wai shi Bayajidda? In an taba yi yaya aka yi ya zo kasar Hausa? Idan har ya leko, me ya sa ake cewa shi ne asalin kasashen da sun rayu, sun ginu, tun kafin a haife shi ko a haifi iyaye da kakanninsa? Haka kuma za mu yi kokarin fahimtar ta yaya wanda ya samu al’umma da kasashe ginannu za a ce shi ne ya samar da Hausa da Hausawa? Shin da gaske ne ya kashe wata macijiya ko maciji a wata rijiya ta Kusugu? Haka kuma shin da ya zo, ya yi aure a Borno ko Daura? Shin da gaske ne ya haifi ’ya’yan da ake cewa su ne suka kafa kasashen da ake kira Hausa Bakwai da Banza Bakwai? Me ya sa Kabbi da Zamfara za su kasance cikin Banza Bakwai, alhali a asali da ginuwa sun ma fi wasu daga cikin kasashen Hausa Bakwai? Shin gaskiya ne Bayajidda bai taka kasar Daura ba, balle ya hadu da wata Daurama?
Za mu ci gaba