Hausa da Hausawa a Doron kasa: kurungus?
Ya zuwa yanzu tambayoyi da yawa na san sun fara karakaina a zukatun masu karatu, musamman ganin cewa an fita daga fagen da aka saba da shi na nazarin tarihi da tarihihi da kuma bayanan kunne-ya-girmi-kaka da tarihin-tarihi an koma cikin fagen kimiyya domin samun haske. Yin haka shi ne abin da ya fi komai […]
Ya zuwa yanzu tambayoyi da yawa na san sun fara karakaina a zukatun masu karatu, musamman ganin cewa an fita daga fagen da aka saba da shi na nazarin tarihi da tarihihi da kuma bayanan kunne-ya-girmi-kaka da tarihin-tarihi an koma cikin fagen kimiyya domin samun haske. Yin haka shi ne abin da ya fi komai dacewa a halin yanzu, ba don komai ba sai ganin cewa yanzu binciken sanin asali ya wuce batun hakar kufai da bibiyar littatafai da takardun da aka ajiye tun tale-tale, an koma ga batun abin da Allah Ya ajiye a jikin halittarSa ta asali, wato kwayar halitta. kila tambayar da wadansu za su fara yi ba ta wuce yaya aka yi Hausawa suka samu shiga cikin wannan fagen nazari da bai gama game duniya ba, musamman dangane da neman sanin asali? Amsar dai ba mai wahalarwa ba ce in aka yi la’akari da irin ci gaban da aka samu a wannan fage a duniyar nazarin asalin ’yan Adam.
Tun a shekarar 2007, lokacin da na kai ziyarar bincike a Ingila na ci karo da wannan sabon fage na nazarin kwayar halitta domin gano asalin ’yan Adam da National Geographic Society da aka kaddamar a Amurka a 1888, tare da hadin gwiwar Genographic Project da aka soma gudanarwa a shekarar 2005, shi ma a Amurka, suka soma. A daidai wannan lokaci na karanci lamarin da kyau, na kuma fahimci cewa bincike ne da zai agaza wajen gane yadda al’ummar duniya ta samo asali daga tushe guda da kuma yadda al’ummar ta hayayyafa yau zuwa sama da mutum biliyan bakwai a doron kasa.
Ganin irin yadda aka tsara batun, ya sa a shekarar 2016 na kai ziyara birnin Washington da ke Amurka, hedikwatar National Geographic da kuma Genographic Project, inda aka debi miyau daga cikin bakina, na kasance ni ne na dubu 779 da 696 daga cikin al’umma daga sassan duniya da suka amince su shiga cikin wannan tsari na binciken asalin ’yan Adam, domin a fitar da wani bangare na asalin Hausawa daga ahalina. A shekarar 2018 kuma an sake dibar miyan nawa domin kara tabbatar da abubuwan da aka ci karo da su a can baya. Masana kimiyyar kwayar halitta sun bi diddigin dubban ’ya’yan kwayoyin halittar daga wannan miyau nawa, ta haka suka fasalta yadda zuriyar ahalina ta kasance cikin tarihi, suka kuma nuna yadda kakannin-kakannina suka yi tattaki a doron kasa a tsawon zamani, ta bangaren mahaifina. Abu na farko da aka gani daga cikin wannan nazari shi ne, ni da sauran Hausawa ba mu da ko digon jinin Turawa a rayuwarmu, ke nan kakannin-kakannina da kuma sauran Hausawa ba su yi auratayya da Neanderthal ba, wadanda ke dauke da kaso mafi tsoka na kwayar halittar al’ummar yankin Turai.
Tun asali masanan kwayar halittar sun riga sun fito da wata itaciya ta asalin dukan ’yan Adam a yau, inda suka nuna duk wani dan Adam da ke shakar iska yana da reshe a jikin wannan itaciya.
Daga cikin kwayar halittata da aka yi nazari aka gano reshen da nake kai, wanda yake kuma reshe ne na Hausawan wannan zamani. Daga wannan dogon nazari an fitar mini da bayani gamsasshe da ya bayyana kakannina, akalla hula shida a baya. Wannan bincike shi ne ya nuna abin da ke kunshe cikin kwayar halittata ta asali da kuma yadda ta gwamutsu da wasu daga baya a tsawon dubban shekaru.
Kamar yadda muka gani a bayanan baya, ni da sauran ’yan uwana Hausawa al’umma ce da ke zaune yanzu a sassan Yammaci da Tsakiyar Afirka, amma domin a san asalin ’yan uwana da kuma sauran Hausawa an gwada kwayar halittata da ta wadansu da ke cikin bankin kwayoyin halittu da ke ajiye a dakunan binciken da ke can Amurka. An yi haka ne domin a fahimci su wa ke da irin tawa kwayar halittar, domin ta haka ne za a gane ’yan uwana da na sauran Hausawa. Sai dai a lura binciken ba yana nufin cewa duk kwayar halittar da ta yi kama da tawa ’yan uwa muke ba, ko kuma ’yan uwan Hausawa ba ne, kamanci ne na lissafin asali, wanda zai iya kaiwa ga dangantaka ta kut-da-kut ko kuma rara-gefe.
Ya zuwa yanzu me ya rage a yi domin kara tabbatar da wannan bincike? Kamar yadda masanan suka yi nuni sai an sake samun wadansu daga cikin al’ummar Hausawa sun shiga cikin wannan tsari na bincike, tattare da sauran ’yan uwa da aka bari a can baya a lokacin yawon duniya da tattaki a doron kasa a tsawon zamani. Ma’ana, a samu wadansu daga cikin al’ummar Asiya da Saudiyya da al’ummar Siwa da wadansu maza daga Kudancin Masar da Yahudawan Afirka da wadansu daga al’ummar kasar Aljeriya da Maroko da Sudan da Libya da Nijar da Chadi da Mali da Muritaniya da Kamaru da Habasha da kasar Afirka ta Tsakiya tsundum a cikin wannan nazari. Yin haka zai kara haskaka turbobin da kakannina da na Hausawa suka bi a lokacin da suke bisa hanyar zuwa inda suke a yanzu, ta bangaren uba.
Duk lokacin da aka samu irina daga sassan duniya suka shiga wannan tukunyar bincike, to za a kara samun haske game da asalin Hausawa fiye da wanda ake da shi a halin yanzu. Ke nan idan har muna son mu san inda dangantaka ta kut-da-kut ta kasance a tsakaninmu da sauran sassan al’ummar duniya sai an yi abubuwa uku. Na farko a kara mika wannan binciken da aka yi wa kwayar tawa halittar ga masu binciken kwakwaf na kimiyya (Science) don su kamanta da sake kwatantawa da nasu bankin kwayar halittun.
Na biyu, a samu ’yan sa-kai daga Hausawa da madangantan Hausawa daga sassan duniya daban-daban da za su shiga wannan tsari na binciken kwayar halitta don sanin asalin Hausawa, ana kuma bukatar akalla mutum dubu 3 kafin a ci dunun binciken. Na uku, a kuma kalli bangaren uwa ko mahafiya, a ga yadda shi kuma ya malkayo cikin tarihin, domin ta haka ne za a ga hoton asalin nawa da sauran al’ummar Hausawa fiye da wanda muke da shi a yanzu.