Hausa da Hausawa: Nazarin kwayar Halitta a Matsayin Kayan Tarihi (2)

Kamar yadda bincike ya nuna akwai daga cikin ’yan uwan kakannin-kakannin Hausawa wadanda suka yi zamansu a Nahiyar Afirka, ba su fita wannan balaguro ba. Sun ci gaba da rayuwa suna gudanar da lamuransu na mulki da bautar gargajiya da neman abinci kamar yadda suka gada tunda dadewa. Ire-iren wadannan ne masana suka bayyana an […]

Hausa da Hausawa: Nazarin kwayar Halitta a Matsayin Kayan Tarihi (2)
Hausa da Hausawa: Nazarin kwayar Halitta a Matsayin Kayan Tarihi (2)

Kamar yadda bincike ya nuna akwai daga cikin ’yan uwan kakannin-kakannin Hausawa wadanda suka yi zamansu a Nahiyar Afirka, ba su fita wannan balaguro ba. Sun ci gaba da rayuwa suna gudanar da lamuransu na mulki da bautar gargajiya da neman abinci kamar yadda suka gada tunda dadewa. Ire-iren wadannan ne masana suka bayyana an gani a sassan Tsakiyar Afirka da aka sani da al’ummar Mbuti da Biaka da kuma Hadza a kasar Tanzaniya ta yanzu.

Wadannan kakannin-kakannin ’yan Adam da suka baro Nahiyar Asiya suka sake shigowa Nahiyar Afirka sun tarar da yanayi mai dadin rayuwa a ciki, sun wataya a sassa daban na Arewa da Tsakiyar Afirka, musamman a yankin da Sahara yanzu ta mamaye, daga baya suka yi mazauni na karshe a yankin Kogin Chadi, kafin daga baya da kogin ya soma kafewa, ruwa ya janye, Sahara ta sake bayyana, suka sake ingizawa gaba domin neman mafaka a cikin yankunan Nijar da sassan Arewacin Najeriya.

Kamar yadda aka sani, al’umma na kaura ne da tafiye-tafiye tattare ne da harshe da al’adu da adabi da al’amurran bauta nasu na gado, saboda haka wadannan kakannin-kakannin ’yan Adam da suka shigo wannan yanki sun taho da nasu lamuran da suka shafi fasalin addini da harshe, ana ma jin su ne al’umma ta farko da suka samar da kakan harshen Hausa na asali wato Afro-Asiatic, wanda shi ya samar da ’ya’ya masu yawa ciki har da ahalin Chadic, ke nan masu kwayar halittar Hausawa tun tale-tale, su ne asalin duk wani harshe da ya fito daga cikin wannan ahali. 

A lura a nan, kakan harshen Hausa na asali ba mai iya cewa ga sunansa, sai dai masana sun yi masa lakabi da (Afro-Asiatic), wato tushen harsunan da suka samo asali daga mazauna yankin Afirka da Asiya, kuma nazarin kwayar halitta ya tabbatar mana cewa lallai asalinmu daga Nahiyar Asiya ce da Afirka, kamar yadda muka gani a baya. Wannan kaka ya haifi ’ya’ya ko ’yan uwa da ’yan uba da suka gina wannan zuriya ta harsunan Afro-Asiatic, sun kuwa hada da tsohon harshen Masar (Ancient Egyptian) da Yahudanci (Hebrew) da Habashanci (Amharic) da Buzanci (Tamashek) da Somaliyanci (Somali) da Oromiyanci (Oromo) da Hausa da Mandara da Kanuri. Shi kuma harshen Hausa da ya fito daga cikin ahalin Chadi

Bincike-bincike sun nuna daga cikin ’yan uwan harshen Hausa da Hausawa na kusa-kusa, akwai wasu daga cikin wadannan harsuna da al’ummomi, wato irin su Ron da Bole da Zaar da Bura da Kamwe da Bata da Angas da Bade da Warji da Buduma da Musgu da Gidar da Tumak da Nancere da  Kera da Dangaléat da Mukulu da Sokoro da Ngizim da Kare-Kare da Kanakuru. 

Idan dai wadannan harsuna da al’ummu ’yan uwa juna ne na kusa da Hausa da Hausawa, ke nan tana kuma yiwuwa daga cikin wadannan dangi ne Hausa da Hausawa suka tusgo. Daga nazarin da aka gudanar an fahimci ba wani abu harshen Hausa ko kuma Hausawa a tsawon zamani. Harshen Hausa na asali ya mutu, abin da muke ji da gani yanzu ya gaje shi  ko kuma ya bullo ne daga cikin wadansu harsuna da suka yi hadaka daga baya. Daga nan harshen Hausa da Hausawa suka mamaye yankunan da muka yi magana da sauran harsuna da al’ummomi, suka zama harshen Hausa da Hausawa.

Bincike ya nuna cewa wadannan gungun al’umma da suka kasance Hausawa a yau, suna da ’yan uwa a sassan duniya daban-daban, ciki kuwa da wasu ’yan kadan daga al’ummar Turai, sai kashi 20 cikin 100 na kwayar halittar irin wadannan al’umma da ake gani yanzu a tsakanin al’ummar Barbar da ke zaune a yankin Siwa a kasar Masar. Haka kuma akwai kwayar halittar kashi 6 cikin 100 a jikin mazajen al’ummar kasar Masar da ke zaune yanzu a Kudancin kasar ta Masar. Ana kuma iya ganin kwayar halittar wadannan kakanni-kakanni namu a jikin Yahudawan da ke warwatse a sassan Afirka da kuma wani bangare na Larabawan Saudi Arabiya.

Haka ma a Tsakiya da Yammacin Afirka ana ganin kwayar halittar wadannan kakannin-kakanninmu a zahiri, inda masana suka tsinci kashi 20 cikin 100 nakwayar halittar a jikin mazajen da ke zaune a yankin. Sai dai abin mamaki an fi ganin wannan kwayar halitta ta kakannin-kakannin namu da muka gada mai tarin yawa a jikin al’ummar da ke makwabtaka da yankin da Hausawa suke zaune yanzu a Tsakiyar Afirka kamar su al’ummar Ouldeme da ke dauke da kashi 96 cikin 100 na kawayar halittar da kuma al’ummar Mada, mai kashi 82 cikin 100 da kuma al’ummar Mafa, mai dauke da kashi cikin 100.

A daidai wannan gabar bari mu dubi wuraren da za a iya kira mazaunin kakannin-kakannin Hausawa daga cikin ’yan Adam da suka yi waccan watayawa zuwa yau. Da farko dai an fahimci cewa inda ‘yan uwan Hausawan yanzu suka fi yawa shi ne yankin Tsakiya da Yammacin Afirka, inda ake da kaso 77 cikin 100, sai kuma Gabashin Afirka da ake samun kashi 17 cikin 100, daga nan sai Arewacin Afirka da ya dauki kaso 5 cikin 100. 

Domin ganin fasalinn sosai ga yadda kason yake na kasashe ko yankunan da za a iya tsintar wadannan ’yan uwa na Hausawa. Akwai dai kasar Aljeriya da kuma jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo, inda ake da yawaitar kwayar halittar ’yan uwan Hausawa na yanzu mai tarin yawa. Ana samun kaso sama da 70 zuwa 80 cikin 100 na kwayar halittar a nan, wanda ke iya nuni da cewa nan ne ainihin ‘asalin Hausawa’ ko kuma nan ne mazaunansu na gaskiya a tsawon zamani, kafin yau.

Sauran yankuna da ke dauke da kwayar halittar da ta gaza kashi 60 inda Hausawa ke da ’yan uwa ko kuma sun yi zama a wuraren tun tale-tale sun hada da Saudi Arabiya da Sudan da Masar da Libya. Haka akwai ’yan uwa ko mazaunan Hausawa daga nazarin kwayar halitta a yankunan kasar Mali  da Muruteniya da jamhuriyyar Niger da Chadi da wani bangare na kasar Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Arewacin Najeriya da wani yanki na Kamaru da kasar Habasha.