Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (6)

Ke nan za mu iya cewa, ba a yi Bayajidda ba, idan ma an yi shi cikin tatsuniyoyi da tarihihin Yammacin Afirka, to bai zo Daular Bornu ko kasar  Daura ko ya kasance tushe ko asalin Banza ko Hausa Bakwai ba. Idan kuma bai zo kasar Daura ba, ke nan akwai tababa game da takobinsa […]

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (6)
Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (6)

Ke nan za mu iya cewa, ba a yi Bayajidda ba, idan ma an yi shi cikin tatsuniyoyi da tarihihin Yammacin Afirka, to bai zo Daular Bornu ko kasar  Daura ko ya kasance tushe ko asalin Banza ko Hausa Bakwai ba. Idan kuma bai zo kasar Daura ba, ke nan akwai tababa game da takobinsa da tsohuwa Ayana da rijiyar Kusugu da kashe macijiya da auren baiwa ko Sarauniya Daurama!
Idan kuwa ba natsuwa cikin wannan batu na tarihi, to ina gaskiyar lamarin? Idan har wannan da tarihihi na da tababa to menene abin kamawa? Idan har muna da shakku kan wannan tarihi ko muna tsammanin hakan bai faru ba, ke nan samuwar wani wai shi Burkima da birnin Biram sai a bidi wani tarihin can daban. Ke nan zuwan Bayajidda garin Gaya da takobin da aka ce an yi masa a garin shi ma yana da tababa a tarihi. Idan kuma ana tababar zuwansa Gaya da samuwar takobin, ke nan ana da tababa da kashe macijiya da takobin da aka ce an yi shi a Gaya. Idan kuma muna da tababa da kashe macijiya, domin da alama tatsuniya ce ko tarihihi, ke nan muna da tababa da rijiyar Kusugu. Idan kuma har muna shakku kan rijiyar kusugu, ke nan ba a debo ruwa ba ke nan daga rijiyar, balle har a kashe maciya, har a yi shelar neman wanda ya kashe macijiya da kuma gano wani wai shi Bayajidda, har ya auri Kuyanga da kuma Sarauniya Daurama. Idan kuwa ba Bayajidda ko kuma bai auri Kunyanga ba ko Daurama har suka haifa masa ‘ya’ya, ke nan ba shi ne asalin Hausa Bakwai da Banza Bakwai ba!
Idan duk wadannan bayanai da muka yi sun kara ingiza mu cikin duhu ne maimakon su fitar da mu zuwa ga haske, ke nan akwai gibi mai tarin yawa da ba a cike ba a cikin wannan tarihihi na Bayajidda. Sai dai a kula, ba wani da zai iya cike wannan gibi a halin da ake ciki, mu ma abin da za mu yi a nan shi ne, mu sake bibiyar abubuwan da aka tanada domin ganin ko za mu iya shirya gadar da za a bi don a kai ga hanyar cike wannan wawukeken gibi game da tarihihin Abii Yazid ko kuma Bayajidda.
Bari mu soma da shi kan sa uban tafiyar wato Abii Yazid ko kuma Bayajidda kamar yadda yake a cikin tatsuniyar, kamar yadda wasu masana suka yi hasashe cewa tun lokacin da aka kashe Abii Yazid ko Bayajiida a shekarar 947 boren da yake jagoranta ya ci gaba da wanzuwa haka kuma mayakansa tun da ba su da shugaba na kwarai kuma ba su da sauran karfin soja, sun tarwatse ne, wasu sun ingiza zuwa cikin tsakiyar Daular Sudan, cikin Sahara, wasu sun yada zango cikin Daular Bornu, sun saje da al’ummar wannan Daula da kuma shiga cikin fadawa da shugabancin Daular ta Bornu. Da yake kuma mayaka ne, wadanda suke sababbin jini, nan da nan suka samu karbuwa a fada, ta yadda Mai na Bornu ya amince da su, suka shiga taimaka wa Daular wajen yake-yake da makwabta. Da yake kuma wadannan dakaru da ‘ya’ya na Abii Yazid sun zo da dawakai masu tarin yawa, sun taimaka wajen gina dakarun Daular ta Bornu. Ke nan ba Abii Yazid ko Bayajidda ne ya shigo Daular Bornu ba, tun da ya rasu tun a 947, sai dai daga cikin ‘ya’yansa ko kuma wasu daga cikin shugabannin dakarunsa da aka tarwatsa a can baya. Daga cikin wadannan ‘ya’ya nasa ke nan wasu suka kara yin gaba zuwa cikin sassan da ake kira na kasar Hausa bayan shekaru. Sai dai kamar yadda hasashen masana ya nuna, wadannan iyali na Abii Yazid, sun shigo cikin sassan kasar Hausa ne suka iske kasashe zaunannu, da sarakanansu da ke da alaka da Babar tun can asali. Ba abin mamaki ba ne daga cikin iyalan Abii Yazid, da yake mayaka ne, kuma ‘yan jinin sarauta, sun nemi su karbe mulki daga sarakunan da suka iske a lokacin. Sun dai yi haka, ko dai ta amfani da talakawan da suke zaune tare da su, ko kuma ta goya wa sarakunan da suke iske baya, musamman da yake sun zo da dakaru da dawakai da ba a saba gani ba a kasar Hausa a wancan lokaci. Ta haka ne wadannan Barbar suka saje da sauran al’ummar wannan yanki, addinin Musulunci da suka zo da shi, ya nemi ya bace, musamman da yake al’ummar da suka iske, tsantsar arna ne ba Musulmi ba, kamar yadda bincike ya nuna, daga baya ne, kusan shekara 400, sa’annan Musulunci ya sake zaunawa da gindinsa a wannan yanki.
Idan wannan hoton yana kalluwa, ke nan za mu iya cewa lalbalai  Abii Yazid ne ya shigo cikin Daular Bornu ko kasar Hausa ba, sai dai wani daga cikin iyalansa ko dakarunsa, wanda kila shi ne aka kora daga Bornu, kila shi ne ya auri Gimbiya, kila shi ne ya haifi Burkimu, kila shi ne ya je Gaya, aka yi masa takobi. Haka kuma kila shi ne ya isa Daura da dokinsa, wanda bai jin Hausa da, ta yadda mutanen Daura suka kira shi da Abu Yazid ko Bayajidda, amma da yake tarihin ya dade an fara mantawa da abin da ya faru, ga shi kuma wannan da ko jika ko wani daga cikin dakarun na Abii Yazid, ya kasance mai jar fata irin ta Larabawa, domin kuwa Barbar suna da kama ta kusa a kalar jiki da Larabawa, kila shi ya sa suka ce (Bayajidda) dan Sarkin Bagadaza Abdullahi ne, maimakon (Bayajidda) da ko jika ko dakare ne na Abii Yazid tun asali. Wannan ke nan game da Bayajidda.
Idan ke nan mun amince cewa ba Abii Yazid ne ainihin Bayajidda ba, wani ne daga cikin iyali ko dakarun marigayi Abii Yazid shi ne ya iso Bornu, shi ne kuma ko wani na kusa da shi ya ingiza zuwa Daura, a bisa hanya Gimbiyar da ya aura a Bornu ta haifa masa Burkimu a birnin Biram, ya kuma je Gaya aka yi masa takobi, ya isa Daura ya auri Daurama, za mu iya yarda cewa lallai abin da ya faru yana da kashin gaskiya, kila inda ake da shakku shi ne inda aka ce ya isa Daura ya iske macijiya ta hana dibar ruwa a rijiya, sai ranar Jumu’a kurum. Wannan na daga cikin zuki-ta-millau da aka gina daga baya daga tarihin da ake da shi saboda dadewar zamani duk kuwa da ana cewa kunne-ya-girmi- kaka, wata sa’a kunnen na jin abu, amma sai baki ya fadin abin da ba shi kunnen ya ji ba, kamar yadda muka ga cewa Abii Yazid ko Bayajidda ba shi ne ya shigo Bornu ko Daura ba, sai dai kila wani daga cikin iyalansa ko dakarunsa.
Saboda haka batun da ya dace mu zauna kansa shi ne, wani daga cikin iyalai ko dakarun Abii Yazid shi ne Bayajidda, ba ainihin mataccen da aka baro can baya da dadewa ba. In kuwa haka ne, me za mu ce game da takobin Gaya da kashe macijiya da auren Kuyanga da Sarauniya Daurama, su ma sun auku?

 Za mu ci gaba.