Hausa ne harshen da aka fi amfani da shi a Afirka ta Yamma —Bincike
An dai fara gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya ne a shekarar 2015.
Bincike ya nuna cewa Harshen Hausa shi ne na 11 a jerin harsunan da aka fi amfani da su a duniya, kuma na farko a Afirka ta Yamma.
Harshen Hausa dai na da masu amfani da shi sama da mutum miliyan 150 da suka warwatsu a kasashe sama da 30, kuma shi yake biye wa Faransanci a yawan masu amfani da shi a duniya.
- ‘Akwai ’yan gudun hijirar Kamaru 73,000 a Najeriya’
- Yadda Daruruwan Likitoci Ke Tururuwar Barin Najeriya
Ana amfani da harshen a kasashe 32 daga cikin kasashen Afirka 54 bayan sun yi hijira zuwa can saboda dalilai daban-daban.
Hatta a kasar Sudan, bincike ya nuna akwai Hausawa kimanin miliyan 10 ’yan asalin kasar.
An dai fara gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya ne a shekarar 2015 a kafafen sada zumunta na zamani.
A lokacin dai, wani ma’aikacin Sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Jari ne da wasu abokansa suka fara bikin ranar domin samar wa da masu amfani da harshen damar tattauna abubuwan da ke ci wa harshen tuwo a kwarya.
Daga bisani a shekarar 2018, an fara gudanar da bukukuwa na zahiri a Gidan Dan Hausa da ke Jihar Kano da ma wasu sassa na duniya, ciki har da kasar Ghana.
Wadanda suka kirkiro bikin sun ce sun yi hakan ne da nufin tuna wa al’ummar Hausawa muhimmancin yarensu da kuma tara su a waje daya domin tattauna yadda za a inganta shi.
Ya zuwa shekarar 2020, an gudanar da bikin Ranar Hausa a kasashe sama da 25 na fadin duniya, ciki har da Faransa da Saudiyya.
Masana dai sun ce Hausa na daya daga cikin harsunan da suka fi saurin yaduwa a duniya, inda hatta manyan kamfanonin sadarwa irinsu Facebook da Google da IOS sai da suka saka shi a jerin harsunan da suke amfani da su.
Ko a ’yan shekarun nan ma, Hukumar Lafiya ta Duniya ta saka Hausa a jerin harsunan da take amfani da su wajen yaki da annobar COVID-19.
Kazalika, a shekarar 2020 ma, kasar Saudiyya ta saka Hausa a jerin harsuna 10 da take amfani da su wajen fassara hudubar ranar Arfa, taron addini mafi girma a duniya.