Hausa ta shiga sahun harsunan fassara hudubar Masallacin Madina

Hausa ne kadai harshen da aka zaba a nahiyar Afirka

Hausa ta shiga sahun harsunan fassara hudubar Masallacin Madina

Masallacin Manzon Allah da ke birnin Madinah

Hukumomin Masallacin Annabi Muhammad (S.A.W) da ke Madina a kasar Saudiyya, sun sanar da harshen Hausa a cikin harsuna 10 da za a rika amfani da su wajen fassara hudubar sallar Juma’a.

Hakan dai na nufin Hausa ne kadai harshen da ya samu damar shiga jerin harsunan.

Sanarwar ya fito ne ranar Juma’a, kamar yadda kafafen yada labaran Saudiyya suka rawaito.

Ga jerin harsunan:

1.English

2.Urdu

3.French

4.Bengali

5.Malay

6.Turkish

7.Hausa

8.Chinese

9.Russian

10. Persian