Hausa ta tarar da zamani
Kalmomin da zamani ya samar da su a harshen Hausa tsakanin matasa.
Akwai wasu kalmomi na Ingilishi da mutanen wannan zamani, musamman matasa, kan yi amfani da su a “Hausance”.
Galibi ba a riga an ari wadannan kalmomi ba a yadda matasan ke amfani da su domin akwai wasu na Hausa da ake fassara su da su ko kuma an riga an are su amma fasalinsu ya sha bamban da yadda ’yan zamani ke amfani da su.
Ga kadan daga cikin wadannan kalmomi – ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta ku kara wadanda kuka sani ba mu ambata ba.
- Wasannin motsa jiki
Gola (mai tsaron raga)
Jesi (= “jersey” – rigar wasa)
Tima-timai (jam’in “team” = kungiya ko tawagar ’yan wasa)
Kuloblika (jam’in kulob = “club” – a sahihiyar Hausa kulob-kulob)
- Nishadi
Furodusa (mai shirya shiri/fim ko wani abu mai kama da haka)
Darakta (mai ba da umarni a fim/shirin talabijin ko rediyo)
Albom (= “album” – jerin wakoki a faifai)
Ya/ta danse (daga “dance” – rawa)
- Ilimi/Karatu
Lakca (= “lecture” – darasi)
Lakcara (= “lecturer” – malami a makarantar gaba da sakandare)
Santoci (jam’in “centre”, wato cibiya [ta bincike ko matattara bayanai ko wurin jarrabawa])
- Siyasa
Kamfe (= “campaign” – yakin neman zabe)
Ciyama(n) (= “chairman” – shugaban jam’iyya/karamar hukuma)
Honorabul/Honorabil (= “honourable”)
Tenuwa (= “tenure” – wa’adin mulki)
Kansila (=councillor – dan majalisar karamar hukuma)
Mamba (=member – dan majalisa/dan kwamiti/dan kungiya)
- Tattalin Arziki/Kasuwanci
Dila (=dealer – dillali, mai sayo kaya da yawa don ya sayar)
Diloli (=jam’in dila)
Bajet (=budget – kasafin kudi)
Zamantakewa
Momsi (= “mummy”, “mum”, “mom” – mahaifiya)
Cika (= “chick” – budurwa)
Lobayya (daga “love” – soyayya).