Hausa ta yi faduwar bakar tasa?

Tun daga kafuwar daular Usmaniyya (1804 – 1808) a karkashin Jagorancin Fulani, harshen Hausa ya zama harshen gwamnati, sabani yadda abin yake idan Turawa suka mulki kasa (Colonialism).Harshen Hausa ya ci gaba da jan akalar Daular Usmaniyya a hukumance har zuwa shekara ta 1903 a lokacin da Turawan Ingila suka cinye ilahirin kasar Hausa da […]

Hausa ta yi faduwar bakar tasa?
Hausa ta yi faduwar bakar tasa?

Tun daga kafuwar daular Usmaniyya (1804 – 1808) a karkashin Jagorancin Fulani, harshen Hausa ya zama harshen gwamnati, sabani yadda abin yake idan Turawa suka mulki kasa (Colonialism).
Harshen Hausa ya ci gaba da jan akalar Daular Usmaniyya a hukumance har zuwa shekara ta 1903 a lokacin da Turawan Ingila suka cinye ilahirin kasar Hausa da yaki.
Duk da sauyin da ya wakana a kasar Hausa har zuwa lokacin da aka kulla auren dole (1914) tsakanin Arewa da Kudanci aka haifar da Najeriya, harshen Hausa ya ci gaba da jan ragama wajen aiwatar da aikin gwamnati, musamman a Najeriya ta Arewa.
An yi amfani da haruffan Larabci (Ajami) wajen rubuce-rubuce a zamanin Shehu dan Fodio (1754 – 1817), wadanda suka hada da rubutun zube (Prose) da wake (Poem) da sha’anin mulki da shari’o’i da dai sauransu. Zuwan Turawa abin bai sauya ba har zuwa lokacin da aka bullo da ‘yan dabara na ‘yan Mulkin Mallaka har aka kai ga dakile haruffan Larabci (Ajami), inda aka maye gurbinsa da na Rumawa (Rubutun Boko), watakila da zummar rage tasirin addini a zukatan masu magana da harshen Hausa ko kuma wani dalili na daban.
A takaice, wannan shi ne salsalar bunkasa da raguwar harshen Hausa a Najeriya ta Arewa.
Sai dai bayan samun Mulkin kai (1960) an samu ‘yan Arewa masu tarin yawa wadanda suka bayar da gudunmawa wajen bunkasa (rubutaccen) harshen Hausa, wadanda ba sai an ambace su ba a nan.
A jamhuriya ta biyu, Gwamnatin Kano ta rusasshiyar Jam’iyyar PRP ta Abubakar Rimi ta yi wa Hausa gata, inda ta fara buga Jaridar ALBISHIR (Boko) da ALFIJIR (Ajami) da zummar wayar da kan mafi yawan ‘yan Najeriya masu magana da harshen Hausa, sai dai kash! Saboda dalili na digirgiren Shugabanci, Gwamnan Kano daga 2011-2015 ya rufe gidan domin ya hukunta wanda ya kasa kai bantensa a jaridance, kuma ya ‘bar Jaki (Shugaban), ya doki taiki (Ma’aikata).’
Shimfidar da aka yi wa wannan makala ta jan hankali ce kawai, amma ko da wasa babu shagube ko yarfe ga kowane mahaluki, domin harshen Hausa kafin Ubangiji ne, wani mahaluki bai isa ya dakile ta ba, dalili ana koyar da harshen a dukkan matakan karatu na gida da waje tun daga firamare zuwa jami’a.
Akalar wannan makala ta karkata ne zuwa kan yadda ake cin zarafin daidaitacciyar (Standard) Hausa a rubuce (Orthographically).
Akwai misalai da dama da za a bayar kan litattafan Hausa da mahukunta ke kallo ana sakin litattafan saki-ba-kaidi!
Da farko, mun yi matukar murna da bullowar jaridu da mujallu cikin harshen Hausa, amma daga bisani sai murna na neman ta komawa ciki, dalili jaridun da mujallun suna fama da karancin ma’aikata, har ta kai babu masu bita da gyara jimloli  ko kuma kalmomin Hausa (Proof.-readers), wadanda su ne tamkar wukar gindi a kowane gidan jarida (ban da Rediyo, Telebijin).
Idan ka dauki jaridu da mujallun da ake wallafa su da Hausa a Najeriya, kusan kowane sakin layi (Paragraph) sai ka samu akalla kura-kurai kamar biyar wadanda suka jibanci hadawa da rabawa tsakanin gabobin magana (Parts of Speech). Misali hada lamiri da suna kamar “shine” maimakon “shi ne” ko hada fi’ili da lamiri kamar “yace” maimakon “ya ce” da kuma kalmar nan da take  yawan fitowa a kanun labaran jarida “in ji”, sai ka ga an hada su kamar “inji” da dai sauransu.
Maganin wannan kwamacala da ko-in-kula da suka samu gindin zama cikin rubutun Hausa, shi ne, shirya wa ma’aikata bitar sanin makamar aiki ta cikin gida (in-house training) kusan sau 4 a shekara da kara yawan ma’aikata masu karatu da gyara ka’idojin rubutu (Proof-readers) bayan sun samu cikakken horo kan daidaitacciyar Hausa (Standard), ta hanyar gayyato Malaman Jami’a da na Kwalejojin Ilimi da ke fadin Tarayyar Nijeriya.
Duk wani tunani da zai bijiro kan harshen Hausa idan ba ci gaba ba ne, tunani ne na rashin kangado da rashin kishin kasa idan ma ba a ce baragada ba.
A nan za mu yi kira ga Gwamnonin Arewa, musamman jihohin nan 12 da suka ayyana amfani da tsarin Shari’ar Musulunci da su kafa dokar-ta-baci kan dawo da martabar harshen Hausa a Najeriya da Nahiyar Afirka ta yamma. Yin haka alhaki ne da yahau kan kasashen da suka karbi tutar Shehu (Flag-Bearing Emirates) har da Borno Empire da tsakiyar Najeriya (Middle-belt) wadanda tutocin ba su kai can ba, saboda dalili na sadarwa, amma ba bijirewa ba.
Jaridu da mujallun Hausa, za su ci gaba da taka rawa wajen kaifafa basira ga masu karanta su ta hanyar mayar da su kwararru wajen sarrafa akalla harsuna biyu (bi-lingual) ko fiye da biyu (multi-lingual) a maimakon dakile basira a tsaya kan harshe daya (mono-lingual).
A nan masana ke ganin beken masu fada-a-ji cikin al’umma, wadanda suka daura yaki da harshen Hausa ganin sun manta da cewa, Hausa na daya daga cikin manyan harsunan Afirka hudu da duniya ta amince da su a ilimance (conbentionally) sauran su ne Larabci daga Arewacin Afirka, Swahili daga Gabashin Afirka, Afirkana daga Kudancin Afrika sai Hausa daga Yammacin Afirka, sauran harsunan ‘yan rakiya ne kuma madalla da su.
A karshe, ina yin kira da murya madaukakiya ga gidajen Jarida musamman Media Trust da ta duba yiwuwar bullo da jaridar Hausa da haruffan Larabci (Ajami) da kara yawan ma’aikata ko da na wucin gadi ne (Casuals) domin yi wa Hausa gata a fagen ilimi da adabi (conbentionally) domin harshen ya ci gaba da rike kanbinsa na Jagoranci a yammacin Afirka (West Afirkan sub-region) kuma a yi wa kidahumai mahangurba a turmusa hancinsu ya zama darasi ga na-baya ko kuma masu tunanin rashin tunani irin nasu. Idan aka ci gaba da yi wa wannan muhimmin harshe rikon sakainar kasha, tabbas za a iya yanke cewa, ‘Hausa ta yi faduwar bakar tasa.’
ALIYU UMAR, Edita, Jihar Kano A yau Ma’aikatar yada Labarai PMB 3088 Kano. 08065570493

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya