Hausa ta zama harshen duniya – Farfesa Abdulhamid Abubakar

kwararren malami mai nazarin harshe a Jami’ar Maiduguri, Farfesa Abdulhamid Abubakar, ya bayyana cewa yanzu harshen Hausa ya wuce matsayin marshen wata kasa guda day ko wata nahiya daya amma ya zama harshe ne da ake amfani da shi ko yake da tasiri a matakin duniya. Farfesa Abubakar wanda ya furta hakan a yayin bude […]

Hausa ta zama harshen duniya – Farfesa Abdulhamid Abubakar
Hausa ta zama harshen duniya – Farfesa Abdulhamid Abubakar

kwararren malami mai nazarin harshe a Jami’ar Maiduguri, Farfesa Abdulhamid Abubakar, ya bayyana cewa yanzu harshen Hausa ya wuce matsayin marshen wata kasa guda day ko wata nahiya daya amma ya zama harshe ne da ake amfani da shi ko yake da tasiri a matakin duniya.

Farfesa Abubakar wanda ya furta hakan a yayin bude babban taron masana harshen Hausa da Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero a Kano ya shirya, ya kuma bayyana cewa a halin da ake ciki fitattun harsunan Hausa da na Swahili ne suka yi fice kuma suka shahara a fagen nazarin kimiyyar harsuna na duniya.
Ya dangana habakar Hausa a cikin Najeriya da wasu tsare-tsare na gwamnati da tsarin ilimi na kasa, wanda ya bayar da damar koyar da harsunan cikin kasa ga daliban makarantu. Ya ce a halin da ake ciki, Hausa ta zama ita ce harshen da ya mamaye sauran kananan kabilu, wadanda suka koma amfani da shi a harkokinsu na yau da kullum. Sannan ya bayyana fatan cewa nan da wani lokaci Hausa da Swahili za su samu karbuwa a Majalisar dinkin Duniya.
A hira da shugaban Sashen Koyar Da Harsuna na Jami’ar ta Bayero, Dokta Aliyu Mu’azu ya bayyana cewa makasudin shirya wannan taron shi ne domin a tattaro masana wajen samun matsaya guda a game da yadda ake amfani da haruffa wajen rubutun Hausa, wanda ya ce ana samun sabani daga waje zuwa waje.
Ya kara da cewa wani dalilin shirya taron kuma shi ne don kara wayar da kan jama’a su fahimci muhimmancin nazarin Hausa. Ya ce nazarin Hausa daidai yake da nazarin kowane harshe na duniya. Ya ce: “Na je Italiya na ga Italiyawa suna nazarin harshensu, haka ma da na je kasar Jamus, na ga suna koyon Jamusanci.” Ya ce amma a nan an samu wasu Hausawan da suke kyamar koyo ko nazari a harshen Hausa.

Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah

Abba El-Mustapha ya samu lambar yabo kan yaƙi da cin hanci

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF