Hausawa da Yarabawa sun yi addu’ar zama lafiya a Ile-Ife
Al’ummar Hausawa da Yarbawa mazauna garin Ile-Ife a Jihar Osun sun gudanar da addu’o’in hadin gwiwa na Musulmi da Kirista, inda suka roki Allah Ya gafarta wa daruruwan mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin rikicin kabilanci a tsakaninsu da aka yi a garin Ile-Ife, a bara. danmasanin Ile-Ife Sheikh Aminu Imam shi ne ya […]

Al’ummar Hausawa da Yarbawa mazauna garin Ile-Ife a Jihar Osun sun gudanar da addu’o’in hadin gwiwa na Musulmi da Kirista, inda suka roki Allah Ya gafarta wa daruruwan mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin rikicin kabilanci a tsakaninsu da aka yi a garin Ile-Ife, a bara.
danmasanin Ile-Ife Sheikh Aminu Imam shi ne ya yi huduba a kan kyautata zamantakewa da zama lafiya a tsakanin al’umma, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Haka kuma malamin ya jagoranci malaman da suka sauke Alkur’ani sau uku domin rokon Allah Ya gafarta wa mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin rikicin.
Mataimakin Sakataren kungiyar Kiristoci (CAN) reshen Ile-Ife, Michael Omoyayi shi ne ya jagoranci mabiya addinin Kirista da suka yi addu’ar zama lafiya a Ile-Ife da Jihar Osun da kasa baki daya.
An gudanar da addu’o’in ne a harabar Babban Masallacin Unguwar Sabo, Ile-Ife. Mai masaukin baki, Sarkin Hausawan Ile Ife Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali ne ya shugabanci zaman taron, wanda ya samu halartar ’yan kasuwa Yarabawa da Hausawa da suka yi hasarar kadarori a lokacin rikicin na bara.
Majalisar Sarkin Hausawan Ile Ife ta bayar da umarnin dakatar da dukan hada-hadar kasuwanci na tsawon awoyi biyar a unguwar ta Sabo, domin girmama zaman taron addu’ar na wannan rana.
Wadamsu ’yan kasuwa Yarabawa da Hausawa da suka yi hasarar kadarori a lokacin rikicin, sun yi wa Aminiya bayanin farin cikinsu da shirya taron addu’ar da irin matakin da Majalisar Sarkin Hausawan ta dauka na raba musu abin da ya sauwaka na tallafin kudi da kayayyaki da aka samu daga jama’a daga sassan kasar nan.
A jawabinsa, Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali ya jinjina wa Gwamna Rauf Aregbesola na Jihar Osun da Gidauniyar dangote da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi da Ooni na Ife Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa, wadanda ya ce, sun taimaka sosai wajen shawo kan matsalar da ta faru a bara.