‘Hausawa masu Keke-NAPEP a Owerri suna dandana kuda’

Shu’aibu Sule, na daga cikin matasan Hausawa da suka rungumi sana’ar tukin Keke-NAPEP wajen safarar fasinjoji a birnin Owerri hedkwatar Jihar Imo. Wakilinmu ya gana da shi, inda ya bayyana irin kalubalen da ke fuskantarsu a matsayinsu na baki daga Arewa: Ko me ya kai ka ga wannan sana’a a nan garin Owerri?Neman abin da […]

‘Hausawa masu Keke-NAPEP a Owerri suna dandana kuda’
‘Hausawa masu Keke-NAPEP a Owerri suna dandana kuda’

Shu’aibu Sule, na daga cikin matasan Hausawa da suka rungumi sana’ar tukin Keke-NAPEP wajen safarar fasinjoji a birnin Owerri hedkwatar Jihar Imo. Wakilinmu ya gana da shi, inda ya bayyana irin kalubalen da ke fuskantarsu a matsayinsu na baki daga Arewa:

Ko me ya kai ka ga wannan sana’a a nan garin Owerri?
Neman abin da za mu ci da iyalina ne ya kai ni ga rungumar wannan sana’a kuma yawan mu (Hausawa) da muke yin wannan sana’a ta tukin Keke-NAPEP a garin Owerri ya kai 50. Sai dai ba mu da karfin sayen Keke-NAPEP daga aljihunmu. Muna karba ne daga hannun wasu kabilun Ibo masu kudi da suke sayo sabonsa a kan Naira dubu 350 su kara yawan kudin zuwa Naira dubu 700 da muke biya a cikin wata 18. Sai idan ka dage ka jajirce ka zama namiji sannan ne za ka iya biyan wannan kudi a cikin shekara daya da rabi.
A gaskiya babu wani ci gaba a cikin wannan sana’a sai dai kawai muna yi ne domin samun abin da za mu ci.
Akwai kananan hukumomi da wasu gwamnatocin jihohi da suke tallafa wa masu wannan sana’a ta hanyar ba su Keke-NAPEP da suke biya a hankali ba tare da kudin ruwa ba. Me ya hana ku shiga cikin jerin masu cin wannan moriya?
A gaskiya babu wani Bahaushe da yake cin irin wannan moriya a nan garin Owerri. Kuma hakan yana da nasaba da irin kabilancin da ake nuna mana ne wanda ya kai mu ga shiga halin kunci da takurar rayuwa kamar ba ’yan Najeriya ba.
Akwai shugabannin al’ummar Hausawa da ’yan siyasa a nan garin Owerri, me ya hana ku tuntubarsu domin shawo kan wannan al’amari?
Gaskiya ne akwai irin wadannan shugabanni da muke zaune a karkashinsu, amma akwai alamar cewa, su ma abin ya fi karfinsu. Saboda haka dole ne mu yi hakuri da kuncin rayuwa ko kuma mu koma garuruwanmu.
Wace shawara za ka bayar domin ganin an yi maganin wannan matsala?
Shawarata ita ce, ina kira da babbar murya ga shugabannin al’umma da siyasa da suke yi mana jagoranci a nan Owerri da su ci gaba da yin fafutikar da suka saba yi wajen ganin sun kyautata zamantakewarmu da mutanen gari da suke kallonmu a matsayin baki wanda ba haka ake yi masu a jihohin Arewa ba.
Kuma ya kamata gwamnonin jihohin Arewa su hadu su kafa kwamiti mai karfi da zai yi aikin tuntubar mutane domin gano irin matsalolin da al’ummar Arewa suke fuskanta a wannan sashi na Kudu. A ba kwamitin damar tuntubar mahukunta, musamman gwamnonin da ke mulki a wannan sashi domin shawo kan wannan matsala ta nuna mana bambanci da kyara kamar ba ‘yan kasa ba.