Hausawa na da farin jini -Abubakar Ladan1

Alhaji Abubakar Ladan Zariya, ya shahara a duniya wajen yi wa Afirka da mutanenta wake cikin harshen Hausa, kuma ya zagaya kasashen Afirka, inda ya karanci zamantakewa da al’adun mutane, don haka ya samu tagomashi a idon duniya, Shugaba Shagari ya ba shi lambar kasa ta MON. Wakilinmu ya tattauna da shi, ga yadda hirar […]

Hausawa na da farin jini -Abubakar Ladan1

Alhaji Abubakar Ladan ZariyaAlhaji Abubakar Ladan Zariya, ya shahara a duniya wajen yi wa Afirka da mutanenta wake cikin harshen Hausa, kuma ya zagaya kasashen Afirka, inda ya karanci zamantakewa da al’adun mutane, don haka ya samu tagomashi a idon duniya, Shugaba Shagari ya ba shi lambar kasa ta MON. Wakilinmu ya tattauna da shi, ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ka bayyana  mana tarihinka?
Abubakar Ladan Zariya: An haife ni a cikin shekarar 1934 a Kwarbai, inda ka iskeni a Zariya, na yi karatun farko na sanin Allah, wato arabiyya, inda na haddace Alkur’ani, a shekarar 1950 na shiga makarantar Elimentary, a 1954 na tafi Zariya Middle School. Sai na tafi Malumfashi Jihar Katsina wajen kawuna na zauna na huta, har na yi wa wani kwara mai Kamfanin Constant tinidies aiki, ina sayar masa da man fetir irin na da, wanda ake wanawa da hannu. Na yi shekaru can kafin na koma Kano,  amma daga 1960  zuwa 61 ina malamin duba fata, aikina shi ne na ga an gyara fatu, an shirya su an auna an fita da su kasashen waje. Na yi aikin duba gyada, inda na zauna a Maiduguri, kafin na dawo gida Zariya.
Daga Kano na fara fita Zinder da Maradi a kasar Nijar. Lokacin da fita yawon duniya sosai a 1963,  na kama hanya ta Maiduguri zuwa Chadi Port lamey (Ndjamena), a can na san Tambal Baye da kake ji ina fada cikin wakena. Na tafi Elfashar cikin kasar Sudan ta Eljineina, na wuce zuwa Khartoum da Omdurman a tafiyar farko. Daga Sudan na sake hawa mota na tafi wani gari a kasar Habasha na sauka wasu garuruwa har zuwa Asmara a kasar Eriteria. Na nemi ganin Hailas Salasi ban samu ganinsa ba, sai dansa, wanda shi ne ya ba ni tikitin Jirgi daga Addis Ababa zuwa Legas na dawo ta sama. Saboda Hailis Salasi a lokacin ba ya nan sai kanen sa na samu shi ma ya yi mini alheri.
Aminiya: A tafiye-tafiyenka, ka dauki nauyin kanka ko wani ya dauki nauyinka?
Abubakar Ladan Zariya: Allah ne mai daukar nauyina, don gaskiya ba wani mai tallafa min sai ko alheri da na ke samu wajen wadanda nake ziyarta, nakan kuma gwada hikimata ta wakoki su ji, su yi dariya su ba ni ihsani na kudi don na biya mota idan zan wuce. Haka nake tafiya a hankali har na zaga kasashen Afirka. Na taba tashi daga Legas na shiga Kotonou na wuce Dahomey na shiga Lome babban birnin Togo, daga nan na wuce Accra Ghana zamanin Shugaba Nkurumah. Na je Kumasi a cikin Arewacin Ghana, inda na shiga mota na nufi Ibory Coast na sauka Abidjan, babban birni, sai na shiga mota na wuce Bomako Mali, haka na wuce garin shahararren Malami Sheikh Ibrahim Khaulaha a kasar Senagal na kwana hudu a can, na wuce Nouchott babban birnin Mauritaniya na tafi Monrobia babban birnin Liberiya; na wuce Freetown babban birnin Saliyo.
Na sake fita yawo na wuce Dakar na sake komawa St Louis a Mauritaniya, wata mashigar jirgin ruwa ce a wajen Sanegal daga nan ta tafi Roso, shi kuma sunan kogi ne tsakanin Senegal da Mauritaniya; sai na dawo Nouchott na zauna na yi kwanaki kafin na zarce na tafi Atara, babban gari ne a cikin Sahara,  an karramani a garin da al’adarsu ita ce, suna fita da dare su je waje su kwana a tanti saboda zafi. Don haka na je wajen wani sai ya fita daga tantinsa shi da iyalansa ya koma wani tanti ya ba ni na zauna. Sai na wuce Morocco na je Casablanca har Jaza’ir. Na tafi Tarabulus kasar Libya wajen 1962, daga Ndjamena na keta cikin yashi zuwa can Tripoli, amma ba zamanin Ghaddafi ba ne; Shugaban sunansa Idris ya rasu a Masar. Ina fadin Idrisiyya a wakokina.
Aminiya: Wane lokaci ne wakokinka suka fara bayyana sosai?
Abubakar Ladan Zariya: Wakokina sun fara shahara a kasashen Afirka daga Garwa ne ta kasar Kamaru a rediyo, wanda ya shahara a wancan lokaci ya yi suna. Sai kuma rediyon Cairo ta kasar Masar, nan ma na yi wakoki, inda na yabi Shugaba Ghamal AbdunNasir da sauransu; suma sun watsa wakokina. Sai mutanen BBC, inda na je Landan wajen 1970 muka yi hira sosai da su; kwanana tara a Landan daga nan muka wuce Amurka birnin Washington. A can su ma mun yi hira da su sosai na yi wakoki.
Aaminiya: Ka taba yin tunanin shiga mawuyacin hali a Najeriya da Afirka?
Abubakar Ladan Zariya: Gaskiya wancan lokaci ba alamar hakan, amma yanzu an shiga rauni lamurra sun lalace, saboda rashin aikin yi, talauci ya dabaibaye mutane, abin da kasashe suka mallaka domin gyara rayuwar mutane kuma wasu kalilan sun kwashe, sun handame ba ta amfane su ba, ba ta amfani mutanen kasashen su ba, an wayi gari musamman a Najeriya ba sana’a matasa ba sa samun abin yi su ci abinci. A wani gefen kuma sun raina sana’ar da suke da ita, wani ba zai iya acaba ba zai dauka ya fi karfinta. Matasa a da kuwa sai su yi ita ce su kawo gari su sayar, don su rufa asirin kan su, amma yanzu girman kai da buri ya hana.  Idan ka duba daga ilmin Middle na yi malamin fata, na yi akawun gyada na yi aikin Norla, na sayar da littafan Gaskiya. Ko a Bauchi ina da babban abokin huldar littattafai, Alhaji Baban Takko.
Aminiya: Yaya tasirin harshen Hausa a wuraren da ka ziyarta a Afirka?
Abubakar Ladan Zariya: Tunda ba Hausawa ba ne wuraren  da na je, amma yawanci wurin da Hausawa suke za ka iske suna da farin jini, don haka wadanda ba Hausawa ba ke daukar Hausawa da kima, saboda alherinsu da rashin rowa da sanya kaya na kasaita saboda yawancin kasashe basa sa kaya masu tsada kamar yadda Bahaushe ke sawa. A Sudan Bahaushe ya zama Sarki cikin wadanda suke tafiya Makka a kasa, wasu kuma sun kasance masu dukiya sosai. Akwai masu tafiya Makka ta kasa su nemi taimako, su tsaya su yi noma su wuce, idan sun samu abin da suka samu daga nan har su ketare ruwa su isa Jeddah.
Aminiya: Ko akwai wata lambar girmamawa a Afirka da ka samu?
Abubakar Ladan Zariya: Na taba samun lambar girma a Garwa lokacin Shugaba Ahidjo, ya ban lamba, amma na mance sunanta, sai kuma a nan Najeriya wani Gwamnan Kaduna ya taba ba ni lambar girma, sai kuma lokacin Shugaban kasa Shagari, an ba ni lambar girma ta kasa MON, kuma wannan lamba tasa kowane taro ina iya shiga ko da ba a gayyaceni ba. Haka idan tafiya ta kama mutum ya je filin jirgi yana tasiri, don na taba nuna ta a Ghana Airways da ke Legas sun daukeni kyauta har zuwa Accra, don haka wancan lokaci wannan lamba na da matukar tasiri, ban san kuma a yanzu ba.
Aminiya: kungiyar hada kan kasashen Afirka  wato OAU ko AU, kana da alaka da ta taba hadaka da su?
Abubakar Ladan Zariya: Na taba zuwa Addis Ababa Ethiopia, su ne suka ba ni tikiti zuwa Legas, suna taro na je wajen, kuma na samu kowace kasa sun dasa itacen ranar da suka samu ‘yanci a Addis Ababa duk kowace kasa ta dasa itacen ta, amma baicin wannan su babu wata lambar girmamawa da suka ba ni.
Aminiya:  Wacce gajiya ka taba ci tun daga wancan lokaci zuwa yanzu?
Abubakar Ladan Zariya: Baicin lokacin Shagari da aka ba ni wannan lamba shi ke nan, sai ko daidaikun jama’a masu kaunata da gwamnoni ko ministoci ko manya akan samu jefi-jefi, kamar Gwamanan Kaduna Lamaran Yero ya taba ba ni Naira dubu 50, sai Janar Buhari shi ma ya taba yi mini alheri, sai Gwamna Lawal Kaita na Katsina ya taba ba ni mota.
A yanzu kuma Gwamna Shema na Jihar Katsina shi ma yana yi min alheri; akwai gwamnan ku Malam Isa Yuguda shi ma yana yi mini alheri, don tun kafin ya zamo gwamna na sanshi ina zuwa gidansa yana bani kudi da taimako. Akwai irin su Alhaji Kawu na Sogiji, shi ma a Bauchi yana saukar da ni a Hotel ya yi min alheri; da su Ahmadu  Adamu Mu’azu su ma nawane. Akwai irin su dahiru Musa Jahun, shi ma mai wake ne a Bauchi mutumina ne. Kuma idan na je Bauchi ana saukeni a Zaranda ko Awala Hotel.
Aminiya: Yaya alakarku da wadanda kuka yi karatu a Middle take?
Abubakar Ladan Zariya: Akwai Sarkin Zazzau Shehu Idris yana raye mun yi karatu a Huda-Huda, da Maccido Mohammed a Kaura yake, da Jakadan Najeriya a Landan, Alhaji dalhatu Sarki Tafida da Ango Abdullahi duk mun yi Huda-Huda, duk nakan je wajensu idan na samu hali. Saboda ba ni da mota kai ko mashin ban mallaka ba, ka duba yadda na ke zaune gidana duk ya lalace ba wanda zai ce ni ne na yi wannan suna. Yanzu ba ni da karfin yawo balle a taimaka mini, yarana kuma yawanci ba mawadata ba ne, don haka yanzu muke cikin wahala sosai.
Aminiya: Mene ne kiranka ga wadannan mutane da kuka taso tare?
Abubakar Ladan Zariya: Ina gayama ka gaya wa mutane masu taimako idan da mai gero ko dawa ko dan kobo ya miko min, saboda ina cikin mawuyacin hali wanda daga ni sai Allah kurum muka san halin da nake ciki, don haka a taimaka mini don na samu na ci da iyali. Yarana sun kai 11 maza da mata. Kuma ina da mata ga girma ya zo ba abin da na mallaka, sai godiya ga Ubangiji kurum, ga lafiyar ma ta kusa tukewa, abin sai hamdala.
Aminiya: Ko a cikin ‘ya’yanka akwai wanda kake zaton zai gajeka wajen waka?
Abubakar Ladan Zariya: A gaskiya babu, saboda yawanci ba mu samu sukunin su yi karatu sosai ba, saboda karatu yanzu sai da kudi ni kuma ba ni da su, duk abin da aka samu bai wuce wanda za a ciyar da iyali ba, sai ko ina da guda daya da ake kira Abdurrahman wanda ya shahara wajen zane, don muna zaune yanzu duk sai ya zana mu.
Aminiya: Wacce shawara za ka bai wa ’yan Najeriya game da halin rayuwa yau?
Abubakar Ladan Zariya: A a horar da mutane su samu abin yi, a kuma hukunta duk wanda ya aikata ba daidaiba ko ya handame dukiyar bayin Allah, wato dauri ko duka ko kisa daidai laifinsa. Idan ba haka ba to lallai ba za a ji dadi ba. A nisanci mutanen banza wajen amana. A gaskiya Najeriya ta baci sosai. Mun san gyara na Allah ne, amma akwai wahala gyaruwarta. Ga fashi da makami, a shiga gidan mutum a ci mutuncinsa, a bi shi hanya a tare shi, a karbe abin da ya mallaka. Wani bala’in haka suddan abi mutum a kashe shi ba laifin tsaye, ba na zaune . Saboda ba wanda ke da garanti a Najeriya a halin yanzu. Ko Turai a kwace abin da ka mallaka, amma ba a kisa barkatai kan babba da yaro, talaka da mai mulki, tamkar a Najeriya yanzu. Mu rika yi wa ‘yan uwa gargadi, kowa ya je makaranta;  kowa ya nemi sana’a komai karantarta kar a raina, da haka sai Allah yasa wa abin da ake nema albarka. Amma idan ba sana’a ba abinci, idan ba abinci kuma ba rayuwa. Allah ya yi mana jagora, mu tamu ta kare, yanzu shekara wajen 80 sai mu tausaya wa kanmu. ‘Yan baya akwai aiki sosai a gabansu. Allah ya gyara mana.