Hausawa sun nemi gwamnatin Oyo ta gina musu rijiyar burtsatse a Garejin Akinyele

Shugaban matasan Hausawan ya ce, ya zama dole mu yi ƙarin kuɗin wankin motocin saboda mu ma da tsada muke sayen kayan aiki da suka haɗa da ruwa da sabulu da kuma sufuri,

Hausawa sun nemi gwamnatin Oyo ta gina musu rijiyar burtsatse a Garejin Akinyele

Matasan Hausawa masu sana’ar wankin manya da ƙananan motoci a Garejin Akinyele sun roƙi Gwamnatin Jihar Oyo ta taimaka wajen gina masu rijiyar burtsatse da za ta sauƙaƙa musu sana’ar tasu da bunƙasa tattalin arzikin jihar baki ɗaya.

Matasan sun bayyana haka ne a hirar Aminiya da jagoransu, Malam Ibrahim Muhammed, wanda ya ce shekara 10 ke nan da ya fara sana’ar wankin motoci a Garejin Akinyele.

“Muna wanke motoci manya da ƙanana musamman kanta da balbo da tirela. A baya muna cajin Naira 800 wajen wanke kanta amma yanzu mun ƙara zuwa Naira 2500. Ita kuma balbo muna karɓar Naira 3,000 don wanke ta maimakon Naira 2,000 da muke karɓa a baya.

Tirela ta koma Naira 6,000 maimakon 3,000 da muke caji a baya,” in ji shi. Ya ce ƙarin kuɗin wankin motocin, ya biyo bayan janye tallafin man fetur ne da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tare da faɗuwar darajar Naira da suka haifar da tashin farashin kayan buƙatun yau da kullum. “Babu yadda za mu yi domin mu ma lamarin ya shafe mu.

Ya zama dole mu yi ƙarin kuɗin wankin motocin saboda mu ma da tsada muke sayen kayan aiki da suka haɗa da ruwa da sabulu da kuma sufuri,” in ji shi.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci ƙaramin filin da matasan suke gudanar da wannan sana’a, ta tarar da Malam Ibrahim Muhammed da yaransa sun taƙarƙare suna wankin motoci a wurin da ke da taɓo a kowane lokaci.

Shugaban matasan Hausawan ya ce yanzu haka akwai yara 18 da suke aiki a ƙarƙashinsa da kowanensu ya dogara da sana’ar wajen ciyar da iyali da biyan wasu buƙatun iyaye da ’yan uwa. Ya ƙara da cewa “A kowace rana muna wanke motoci manya da ƙanana da yawan su ya kai 25. Sai dai babbar matsalarmu ita ce rashin wadataccen ruwa.”

Ya ce, “Muna sayen ruwa da tsada daga ’yan-ga-ruwa kuma muna doguwar tafiya kafin mu ɗebo ruwa da kansu. Shi ne ya sa muke miƙa ƙoƙon bararmu ga Gwamnatin Jihar Oyo da Ƙaramar Hukumar Akinyele su taimaka su gina mana rijiyar burtsatse a wannan wuri don taimakawa wajen bunƙasa wannan sana’a da za ta samar wa gwamnati kuɗin shiga da bunƙasar tattalin arziki.”