Hausawa sun rungumi kasuwancin rodi  yanzu – Shugaba

Alhaji Nasiru Adamu Abdullahi shi ne Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Rodi da ke Kasuwar Kofar Ruwa a Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda kasuwancin rodi yake da irin ci gaban da aka samu na shigar Hausawa cikin kasuwancin rodin:   Aminiya: Yaya kuke gudanar da kasuwancin rodi a wannan kasuwa? Alhaji Nasiru: […]

Hausawa sun rungumi kasuwancin rodi  yanzu – Shugaba

Alhaji Nasiru Adamu Abdullahi shi ne Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Rodi da ke Kasuwar Kofar Ruwa a Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda kasuwancin rodi yake da irin ci gaban da aka samu na shigar Hausawa cikin kasuwancin rodin:

 

Aminiya: Yaya kuke gudanar da kasuwancin rodi a wannan kasuwa?

Alhaji Nasiru: Kamar kowane kasuwanci da kika sani muna sa kudinmu mu je kamfanonin da ke yin rodi mu sayo mu kawo mu kasa a kasuwa. Kamfanonin da muke sayowa sun hada da namu na gida da ke Kano da Legas da Osun da Katsina. Idan kayan da ka auno suka zo motar za ta zo ta sauke maka su a kofar shagonka. Akwai leburori da su kuma aikinsu ne su lankwasa rodin kasancewar a tsaye yake zuwa, don haka za su gudanar da wannan aiki. Idan mai saye ya zo kuma akwai motocin daukar kaya sai kuma direban da yaron motar su zo su dauka su zuba a mota. Akalla a cikin wananan kasuwa mutum sama da dubu daya suna cin abinci.

Aminiya: Yaya nau’o’in rodi yake?

Alhaji Nasiru: Shi rodi bambancinsa shi ne lamba amma za ka samu duk iri daya ne. Za ka samu akwai lamba 35 akwai lamba 30, akwai lamba 16, akwai lamba 12 akwai lamba 10 akwai kuma lamba 8 da sauransu.

Aminiya: Lura da yadda rodi yake kamar abu ne da zai iya cutarwa wane mataki kuke dauka wajen kare kanku yayin da kuke mu’amala da shi?

Alhaji Nasiru: Idan kin kula za ki ga bakunan karfen sun kalli shagunanmu. Ana lankwasa su su kalli shago ne don gudun kada su cutar da mutanen da ke wucewa ko mutanen da za su dauke su a mota. Kasancewar wani rodin yana danne wani ba ya dagowa, don har takawa mutum zai iya yi ba tare da ya cutar da shi ba. Mu da yake mun saba har barci muke yi a kansa ba tare da wata matsala ba. Haka kuma mukan gargadi masu daukar kayan cewa idan suka dauka su rika kula da motocin da ke shigowa cikin kasuwa don kada a samu matsala.

Aminiya: Ganin yadda rodin yake zube a bakin shaguna yaya kuke yi wajen tsaro?

Alhaji Nasiru: Idan za mu tashi kowa zai sanya sarka ya daure kayansa ya sa makulli ya rufe. Sai kuma a bar wa masu gadin kasuwa. Babban dai tsaro yana wurin Allah.

Aminiya: Mece ce nasara da kalubalen kasuwancin rodi”

Alhaji Nasiru: A baya Hausawa ba su gane wa kasuwancin rodi ba sai dai su yi leburancin zuba kaya ko saukewa a mota ko su yi gadin kayan kabilun da muke zaune da su. Amma a yanzu Hausawa sun mamaye kasuwancin rodi suna da jarinsu suna da shagunansu na kansu. A yanzu Bahaushe zai tafi har Legas ko Jihar Osun ya sayo rodi ya kawo Kano ya sayar wannan babbar nasara ce a gare mu. Yana daga cikin ribar kasuwancin rodi yadda mutum ba ya faduwa. Domin shi karfe dadewa ko yin tsatsa ba ya karya darajarsa. Mutum zai iya yin gini da rodi bayan wani lokaci ya rushe ginin zai iya kai rodin nan kasuwar ya sayar da shi ya karbi kudinsa. Watakila idan ya yi sa’a rodin yana kan daraja sai ya ci riba a kan abin da ya saya a baya.

Yanzu komai yawan ruwan sama a filin nan muke barin rodin ruwa ya dake shi amma babu abin da zai yi kuma kudinsa ba zai ragu ba.

Kalubalen kasuwancin rodi bai wuce yadda ake samun hawa da saukar farashinsa ba. Wani lokaci sai dan kasuwa ya tafi Legas ya sayo kayansa kafin a kawo masa sai ka ji an ce farashinsa ya karye misali a Kano, to mutum kuma babu yadda zai yi sai dai ya sayar a wannan farashi. Kin ga mutum ya yi asara.

Aminiya: Wane kira kuke da shi ga gwamnati?

Alhaji Nasiru: Muna neman gwamnati ta gyara mana titunan da ke cikin kasuwar tare da sanya fitilu don inganta tsaron dukiyarmu a kasuwar. Muna kiran gwamnati ta dube mu kamar yadda mu ma muke yi mata biyayaya ta hanyar biyan haraji da yin zabe da sauransu. Fatanmu dai yadda gwamnati ke yin alkawura ga ’yan kasuwa ta cika