Hausawa sun yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri
Akasarinsu Kanawa ne daga garin Tsakuwa da ke Ƙaramar Hukumar Garko da ke Jihar Kano.
A kwanakin baya Hausawa mazauna Jahar Imo suka yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri Fadar Gwamnatin Jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabas yankin da ake kira da Ibo.
Hausawa mazauna Jihar Imo da ke Owerri babban birnin jahar a kwanan baya sun yi bikin cika shekara 153 da zuwa Owerri, Jahar Imo da zama domin gudanar da harkokin na kasuwanci.
- DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’
- Sarki Sanusi ya ziyarci unguwar da mutane suka rasu a dalilin rusau
Yawancin garurukan Asaba da Benin da Obudu a Jihar Kuros Riba su ne mazaunin Hausawa na farko a Jahar Kuros Riba sai kuma garin Alele a Jihar Ribas mai iyaka da Jihar Bayelsa da garin Fatakwal da sauran wasu garuruka a Kudu maso Kudu da garin Anaca Jahar Anambra.
Hausawa sun zo garin Owerri tun kimanin shekara 153, wanda akasarinsu Kanawa ne daga garin Tsakuwa da ke Ƙaramar Hukumar Garko da ke Jihar Kano, kamar yadda Sarkin Hausawan Owerri, Alhaji Auwalu Baba Sai’idu Sulaiman ya shaida wa Aminiya.
Masarautar Hausawan kamar yadda Sarkin Alhaji Sai’du Suleiman ya tabbar, tana ƙunshe da ƙabilun Arewacin Nijeriya Musulmi da waɗanda ba Musulmai, suna zaune lafiya tsakaninsu da kuma ’yan asalin jihar.
Ko a gwamnatin da ta shude tsohon Gwamnan Jihar Imo ya naɗa ɗan Arewa muƙamin mataimaki na musamman kan harkokin baki wadanda ba ’yan asalin jihar ba.
Ta bangaren ci gaba da bmazauna Jahar Imo da kuma babban birnin Owerri, Sarkin ya ci gaba da cewa, “Wannan masarauta tana da hakimi guda da dagaci guda da ke kowace karamar hukuma da ke Jihar Imo guda 27 da ke daukacin kananan hukumomin 27 na Jihar ke nan.”
Da yake karin haske game da masarautar, kakakin Sarkin, Nura Bala Ajingi ya ce, masarauta ta faɗaɗa ne zuwa sauran kananan hukumomin da aka ambata saboda ci gaban da ake samu na al’ummar Arewa mazauna jahar a karkashin wannan masarauta da Alhaji Auwal Baba Sa’idu ke shugabanta.
Haka nan kuma sarkin Hausawa Owerri shi ne sakataren sarakunan daukacin majalisar sarakunan Hausawa mazauna shiyyar Kudu maso Gabashin Nijeriya.