Hausawa sun yi zanga-zanga kan kama mutane 73 da ke kwana a masallaci
Wadansu Hausawa da ke gudanar da sana’o’i daban-daban a jikin wani masallaci da ke garin Dutsen Apo a yankin birnin tarayya Abuja,sun gudanar da zanga-zanga saboda kama wadansu daga cikinsu da jami’an ’yan sanda na Abuja suka yi a cikin dare ranar juma’a ta makon jiya, inda aka kama mutum 73 da misalin karfe daya […]

Wadansu Hausawa da ke gudanar da sana’o’i daban-daban a jikin wani masallaci da ke garin Dutsen Apo a yankin birnin tarayya Abuja,sun gudanar da zanga-zanga saboda kama wadansu daga cikinsu da jami’an ’yan sanda na Abuja suka yi a cikin dare ranar juma’a ta makon jiya, inda aka kama mutum 73 da misalin karfe daya na dare.
Sun ce sun yi zanga-zangar ne bayan sun gano cewa limamin masallacin Malam Abdulhamid Imam yana da hannu a kamen mutanen, wadanda suka hada da masu sana’ar tukin tasi da Keke NAPEP da kuma ‘yan Achaba da ’yan garuwa, kamar yadda jagoran al’ummar Hausawa da Fulani na garin, Malam Abdulhamid Muhammad ya sanar da Aminiya.
daya daga cikin wadanda aka Kama mai suna Bashari Salisu, ya ce a baya limamin ya taba bukatarsu da su nemi wajen kwana a wani waje, “amma sai muka ci gaba da kwana a harabar masallacin, ana cikin haka ne kuma sai wannan kamen ya bijiro.’’
Shi ma Jamilu Umar ya bayyana cewa, bayan wadanda suka kama su sun tayar da su daga barci a cikin daren, sun bukaci da su yi dogon layi, daga nan ne kuma suka bukaci su shiga cikin motocinsu biyu, inda suka yi sawu biyu suna kai mutane, a na ukun ne, inji shi, suka bukaci wadanda suka kaman da su yi belin kansu gabanin karasawa da su ofishin ’yan sanda.Ya ce, “sun karbi Naira 1,500 daga hannun kowa, a nan muka dawo bayan an wuce da na farko.’’
Shi ma wani matashin mai suna Lawwali Sani da ke cikin wadanda aka wuce da su ofishin ‘yan sandan, wanda ke sana’ar kayan koli a garin na Dutsen Apo, ya yi bayani a kan yadda aka kwashe su a yayin kai su ofishin a cikin mota, ya ce, “sun dauke mu wadansu a kan wadansu a takure, ko dabbobi ba a yi wa haka nan.’’
A korafin da ya yi, shugaban kungiyar Hausawa da Fulani na kauyen na Dutsen Apo, Malam Abdulhamid Muhammad, ya ce wadanda aka kaman an kama wadansu ne suna cikin baca, wadansu a cikin motocinsu na sana’a, sai kuma wadansu da ke kwana a barandar masallaci.
Ya ce, sun gano al’amarin ne lokacin da suka lura da karancin jama’a a yayin Sallar Asuba ta ranar Asabar, “a nan muka bukaci Limaminmu da mu je ofishin ’yansanda tare, amma ya kauce. Zuwanmu wajen ne muka gano cewa ashe shi ne ya ba da umarnin a kama mana mutane. A nan muka dawo muka bukaci lallai sai ya je ya yi belinsu. Ya karbi Naira dubu 20 daga cikin kudin masallaci ya je ya yi belinsu su 73 bayan mun bi ta wajen Dagacin gari wanda shi ma ya sa baki.’’
Jagoran hausawan ya ce, “Mun nuna wa liman bacin ranmu a kan matakin da ya dauka, inda da farko ya karyata, amma daga bisani ya amsa laifinsa, a nan muka bai wa jama’a hakuri. Sai dai a sakamakon hakan mun bayyana masa cewa dole ne a kafa kwamitin gudanarwa na wannan masallaci, kamar yadda a ke yi a ko’ina, wanda zai kunshi ’yan agaji da wadansu malamai da sauran jama’a, kuma ya amince.’’
A ganawarsa da wakilimu, limamin Masallacin Malam Abdulhamid Imam, ya ce bayan la’akari da yanayin halayyen da wadansu daga cikin masu fakewa da masallacin suna kwana a haraba ko daura da shi, sun bukaci jama’a da su yi kokarin kama dakin haya a cikin garin gwargwadon karfinsu, Wanda a sakamakon hakan aka rushe tsohon masallaci da ke wajen wanda wadansu suka maida shi wajen kwana bayan wani bawan Allah ya gina musu sabo.Ya ce ya amsa laifin da mutane suka dora masa na cewa yana dan hanu a al’amarin, “kuma a dalilin hakan ne na je na sa baki aka sake su. Sai dai ina fata za su yi kokari su samu mahalli da za su rika kwana, kamar yadda ’yan sanda suka umarce mu da mu yi.’’
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’Yan sanda ta Abuja, DSP Hyelira Altine Daniel, wadda ta tabbatar da kamen da kuma sakin wadanda a kaman, ta ce samame ne da rundunarsu ke yi a dukkan wurare mai yanayin baca don tantance irin mazauna wajen, a kokarinsu na raba Abuja da bata-gari.