Hausawan Mai-Kwari a Abuja na fargaba kan yunkurin kwace musu gonaki

Al’ummar Hausawan da suke zaune a kauyen Mai-Kwari a yankin Kwali da ke Birnin Tarayya, Abuja, na cikin fargaba sakamakon yunkurin kwace musu gonaki da barazanar korarsu daga yankin da suke zaune sama da shekara 37 kafin kafa Abuja.  A ganawarsu da Aminiya a farkon makon nan, al’ummar sun ce umarnin hakan ya fito ne […]

Hausawan Mai-Kwari a Abuja na fargaba kan yunkurin kwace musu gonaki
Hausawan Mai-Kwari a Abuja na fargaba kan yunkurin kwace musu gonaki

Al’ummar Hausawan da suke zaune a kauyen Mai-Kwari a yankin Kwali da ke Birnin Tarayya, Abuja, na cikin fargaba sakamakon yunkurin kwace musu gonaki da barazanar korarsu daga yankin da suke zaune sama da shekara 37 kafin kafa Abuja. 

A ganawarsu da Aminiya a farkon makon nan, al’ummar sun ce umarnin hakan ya fito ne daga masarautar Ashara wadda suke karkashinta a yayin wani taro a fadarta inda suka bukaci a sauya musu Sarkin Hausawan kauyen, sakamakon yanayin shugabancin da suka ce yake yi musu.
Shugabannin al’ummar sun ce maimakon share musu hawaye ne sai masarautar ta ce su bar yankin tare da yunkurin kwace musu gonakin da suka sara sama da shekara 37 a lokacin da suka zo yankin Abuja.
“Mun zo yankin nan ne daga jihohi daban-daban na Arewa a lokacin, bayan yekuwar bukatar hakan a gidajen rediyo da ke neman jama’a su zo sabon Birnin Tarayya don cike gibin ayyukan kafa sabon birnin a lokacin. Etsu Ashara na lokacin marigayi Sarki Abubakar shi ya kawo mu wannan wajen wanda a lokacin kungurmin daji ne, ya ce mu sari filin noma da na zama iya bukatarmu, ya kuma gaya mana cewa burinsa shi ne ya ga yankin ya samu mazauna daga nan har zuwa wani waje da ake kira Kwaita. Mun wahala kwarai wajen sare wannan waje wanda ya dauke mu tsawon shekaru. Kuma ba mu taba tunanin akwai wata al’umma da ke kusa da mu ba, sakamakon duhun dajin wajen nan a lokacin, sai bayan shekara daya muka gano kabilar Bassa wadanda su ne ’ya asalin garin, sannan muka kafa nan da ake kira Unguwar Hausawa,” inji su.
Sun ce daga baya ne sauran kabilu da suka hada da Gana-Gana da Tibi da Mada suka shigo yankin a matsayin baki, kamar Hausawan wadanda suke da rinjaye a tsakanin daukacin kabilun kauyen na Mai-Kwari. Sun bayyana mamaki a kan shirin kwace gonakinsu da umartansu su bar wajen da suke zargin Etsu Ashara na yanzu Dokta Salihu Hussaini ya umarce su, bayan sun sun bukaci a sauya musu Sarkin Hausawan kauyen.
Sai dai a zantawarsa da wakilinmu Etsu Ashara Dokta Salihu Hussaini ya musanta zargin kwace gonakin da kuma umartarsu su bar yankin. Ya ce ya tura wasu daga cikin mutanensa su kan su tantance gonakin al’ummar tare da daukan sunayen masu su, don magance matsalar sayar da filaye ga wasu da ake zargin su da yi.
Ya ce bai hana su bada hayar gonakin ba ga wasu muddin wadanda za su ba su mazauna garin ne ba wasu daga wani waje daban ba.
Ya ce dagewarsu na ya sauke Sarkin Hausawa da ke shugabantarsu ya biyo bayan rashin goyon bayansa ne kan ci gaba da saida filaye da suke yi da biyayyar da Sarkin Hausawan ke yi a gare shi.
Estsu Ashara ya ce sauya Sarkin Hausawan tamkar rashin ladabi ne ga magabacinsa wanda shi ne ya nada shi a lokacin da yake raye, kuma akwai umarni daga Ma’aikatar Birnin Tarayya, Abuja da ta dakatar da duk wani nadi a kan abin da ya shafi sarautun gargajiya a daukacin yankin. Sai dai ya ce a shirye yake ya sauya jagoran nasu a duk lokacin da aka dage dokar, muddin za su nuna masa dalilansu kan zargin da suke masa da za su gamsar da shi.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista