Hauwa: Bafulatanar daji da ta dauki nauyin karatun danta zuwa jami’a
Burina in ga ’ya’yan Fulani sun samu ilimi.
Hajiya Hauwa Ardo Sulaiman Bafulatana ce haifaffiyar dajin Falgore a Jihar Kano wacce a yanzu take zaune a Rugar Ardo da ke Janguza.
Duk da cewa ba ta yi karatun boko ba, kai duk danginta ba a taba samun wanda ya yi karatun boko ba, amma saboda huldarta da ’yan boko a dalilin sayar da fura da take yi a Jami’ar Bayero, Kano ya sa kanta ya waye game da ilimin boko har ta kai ga daukar nauyin karatun ’ya’yanta 9.
- Yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada —Sheikh Ibrahim Khalil
- Daliba ta rasu ana tsaka da daukar lacca
A tattunawarta da Aminiya ta ce za ta iya salwantar da duk dukiyarta wajen ne wa ’ya’yanta ilimi, kuma tuni ta sayar da shanunta biyu don daukar nayin karatun danta mai suna Sadik da yanzu ke shekararsa ta karshe a Jami’ar Alkalam da ke Katsina.
Hajiya Hauwa wacce ta dauki tsawon shekara 17 tana sayar da fura a harabar Jami’ar Bayero ta ce ta fara sha’awar sa ’ya’yanta a makarantar boko ne lokacin da ta fahimci cewa mutanen da take ciniki da su a makaranta, wasu da kyar suke samun Naira 50 na sayen furar, amma da zarar sun kammala karatu sai ta ga sun zama wani abu, rayuwarsu ta sauya.
“Wallahi wasu ma ba na gane su sai dai idan sun yi min bayani, har sukan yi min kyauta. Daga nan na fara tunanin cewa akwai bukatar ni ma ’ya’yana su yi karatu.
“Da na shawarci mahaifinsu sai ya amince duk da cewa da farko ya nuna turjiya inda ya nuna cewa ba ya da karfin da zai dauki dawainiyar karatunsu.
“Ni kuma na ce na ji na gani. Da dan cinikin furata nake biya musu kudin makaranta,” in ji ta.
Hajiya Hauwa ta ce duk da cewa ta sha surutu a rugarsu amma a yanzu ta zama abin koyi ga abokan zamanta.
Ta ce, “A yanzu haka mahaifiyata ba ta san ’ya’yana suna karatun boko ba, saboda ba ta so. Sai dai ta kai abokan zamana su ma sun sa ’ya’yansu a makaranta, saboda sun fahimci amfanin ilimin.”
Ta ce ba ta taba sarewa ba game da daukar nauyin karatun ’ya’yanta.
“Lokacin da Sadik ya kammala firamare sai na tambaya cewa wacce makaranta ce mai kyau sosai a bangarenmu sai aka gaya min Musa Iliyasu.
“Sai na kai shi can idan ya tashi sai ya taho cikin jami’a mu ci gaba da sayar da fura. Har Allah Ya sa ya kammala.
“A wancan lokaci ne sai ya nuna sha’awarsa ga makarantar koyon tukin jirgin sama. Da ya gaya min burinsa sai na ce ya nemi gurbi ni kuma koda za ta kai ni ga sayar da shanuna to zan biya masa ya je.
“Da kansa ya je makarantar ya tambaya aka ce kudin sun fi Naira miliyan bakwai. Na ce masa kada ya damu ya ci gaba da nema. Sai dai kuma cikin ikon Allah bai samu gurbi ba.
“Don haka sai muka nemi Jami’ar Bayero sai dai kasancewar bai samu abin da ake nema a jarrabawar Post UMTE ba, sai muka nemi gurbi a Jami’ar Alkalam da ke Katsina.
“Da aka zo batun kudin makaranta sai da na sayar da shanu biyu kafin in biya masa kudin makaranta. Ga shi kuma cikin ikon Allah yana shekararsa ta karshe.
“Haka sauran kannensa suna karatu, wasu a firamare wasu a sakandare. Saboda karatun yara duk da sana’ar da nake yi har yanzu ba ni da fili nawa na kaina.
“A yanzu haka wurin da muke zaune ba namu ba ne. Idan muka kafa bukkokinmu idan mai filin ya zo zai yi gini sai mu matsa gaba,” in ji ta.
A cewarta ba ta taba samun tallafi daga wani kan karatun ’ya’yanta ba sai dai wadanda sukan taimaka mata da bashi idan abin ya kakare.
“Idan na yi ciniki ko Naira dubu hudu to dole in boye dubu biyu saboda kudin makarantar yara.
“A wani lokaci mun hadu da bala’in Boko Haram suka kwashe mana shanu a Maiduguri da muka kai kiwo.
“A wancan lokaci ne na yi kokarin ganin Shugaban Jami’ar kasancewarsa abokin cinikina amma abin bai yiwu ba.
“Haka dai Allah Ya taimake ni har na samu na hada kudin aka je aka biya.
“Kuma a lokacin cutar Kwarona wani a cikin jami’a ya taba ranta min Naira dubu 100 saboda zan biya kudin makaranta,” in ji ta.
Hajiya Hauwa ta ce burin da take da shi, shi ne ta ga ’ya’yanta sun yi ilimi ana kuma damawa da su a duniya.
“Ina son su zama masu ilimin da za su amfani kansu da al’umma. Haka kuma ina so in ga ko bayan raina su yi alfahari da ni a matsayin wacce ta tsaya musu.
Sai ta yi kira ga mata cewa su mai da hankali sosai kuma su jajirce “Domin idan muka jajirce a kan komai to Allah zai taimake mu har mu kai ga cim ma burinmu.
“Kada mu dauka dole ne sai mazanmu sun yi mana komai, mu nemi na kanmu mu tallafa wa kanmu da ’ya’yanmu.
“Ni da kika gani ban san hutun haihuwa ba ballanta tsohon ciki ya hana ni sana’a. Na sha zuwa BUK idan na koma gida in haihu cikin dare.
“Idan na haihu nakan zauna a gida na wasu ’yan kwanaki sannan in koma sana’ata,” in ji ta.
Burina in ga ’ya’yan Fulani sun samu ilimi—Sadik S. Dikko
Danta Sadik S. Dikko dalibin shekarar karshe a Sashen Ilimin Kwamfuta a Jami’ar Alkalam da ke Katsina a tattaunwarsa da Aminiya ya ce yana da burin ya dage da karatu don ya ga ya fita kunyar mahaifiyarsa wacce ta dauki nauyin karatunsa da sana’ar da take yi ta fura da nono.
Da yake waiwaye game da halin da ya shiga lokacin da aka sa shi makaranta, Sadik Dikko ya ce “Lokacin da aka sa ni a makaranta na dauka wata duniya za a kai ni.
“Kuma kasancewar a ruga muka taso, ba mu da wayewa da takalmin roba muke zuwa makaranta.
“ ’Yan uwanmu dalibai suna ta tsokanarmu wai ’ya’yan Fulani amma ba mu damu ba. Ya ce kasancewar yana la’akari da wurin da ya fito bai tsaya ya yi wasa da karatu ba.
“Kullum burina shi ne yadda zan fitar da mahaifiyata kunya saboda ina ganin irin dawainiyar da take yi a kaina.
“Don haka na dage duk da cewa ba na cikin jerin farko na san ina tsakiya.
“Akwai wata rana a Makarantar Musa Iliyasu aka yi taron bayar da kyaututtuka sai aka samu sunana a cikin wadanda za a ba kyauta, amma daga baya sai aka ce kuskure aka yi.
“Wannan abu ya bata ran mahaifiyata inda ta dauka cewa an yi haka ne don kasancewarmu talakawa.
“Ni kuma na san ba haka ba ne. To tun daga wancan lokaci na dage kan karatuna domin a lokacin ina daukar na ashirin da amma daga baya na dawo ina daukar na biyu.
“Haka kuma ko lokacin da na fara karatu a Jami’ar Alkalam na kama kaina na mayar da hankalina kan karatuna.
“Kasancewata mutum na farko da ya fara karatu a rugarmu da ma danginmu, duk abin da zan yi zai zama abin koyi ga na baya don haka nake takatsantsan,” in ji shi.
Sadik wanda ya ce, “A farkon shigarsa Alkalam ba wanda ya san shi a ajinsu sai da sakamakon jarrabawa ya fito ya samu CGPA 4.77.
“Wannan ne ya sa na yi abokai, har ma ya zama ina koyar da sauran dalibai (tutorial) ba wai kawai na sashen kwamfuta ba har ma da na sauran bangarori, hakan ya janyo mutane da dama suka san ni.
“Sai kuma dalibai suka sanya ni a siyasar makaranta inda na zama Mataimakin Shugaban Dalibai na Bangaren Kwamfuta.”
Ya ce burinsa a yanzu bai wuce ’ya’yan Fulani su samu ilimi ba.
“Abin da nake so in ganin a yanzu haka na samar da wata kungiya ta matasa makiyaya.
“Muna so mu ga yadda gwamanti za ta shigo ta taimaka wa ’ya’yan Fulani don ceto rayuwarsu su yi karatu su samu ayyukan yi.
“Ta sanadiyyar wannan kungiya mun gano wasu matasan Fulani irinmu da suka yi karatu.
“To mun hadu muna so a canza rayuwar ’ya’yan Fulani domin dukkan abubuwan da suke faruwa na ’yan ta’adda rashin ilimi ke kawo shi.
“Ina so ya zama cewata sanadiyyata rayuwar wasu ’ya’yan Fulani ta canza.”
A cewarsa bai gamsu da kungiyoyin Fulani ba, inda ya yi zargin cewa yawancinsu suna yi ne ba don ci gaban Fulanin ba sai don kansu.
“Ni a yau ba zan iya nuna miki wani Bafulatani da ya amfana daga wata kungiya ta hanyar samun tallafin gwamnati ba.
“Ko kuma a ce ga shi an samar wa dabbobinmu abinci musamman a lokacin rani. Yawancinsu ba Fulani ne na ainihi ba, ba su san halin da Fulani suke ciki ba.
“Abu daya na sani shi ne sukan wuce gaba a yi sulhu a tsakanin gwamnati da masu garkuwa da mutane da sauransu,” in ji shi.