Hauwa Isyaku Abdullahi 2 Abble: Mace ta farko Kwamandar kungiyar Scout
Tarihin rayuwata: Sunana Hauwa Isyaku Abdullahi 2 Able wacce aka fi sana da Hauwan Mama. An haife ni ne a 1980 a Unguwa Uku kusa da makarantar firamare da ke Unguwa Uku, Tsohuwar Tasha a cikin birnin Kano kuma na fara karatun allo a Unguwa Uku a makarantar Malam dahiru na kuma yi makarantar rainon […]
Tarihin rayuwata:
Sunana Hauwa Isyaku Abdullahi 2 Able wacce aka fi sana da Hauwan Mama. An haife ni ne a 1980 a Unguwa Uku kusa da makarantar firamare da ke Unguwa Uku, Tsohuwar Tasha a cikin birnin Kano kuma na fara karatun allo a Unguwa Uku a makarantar Malam dahiru na kuma yi makarantar rainon yara a Fatima Nursery da ke Kundila daga nan sai na tafi firamare a Unguwa Uku Special Primary School (SPS) da ke kallon ofishin Hisba na karamar Hukumar Tarauni na kuma ci gaba da Islamiyyar Abbah da ke Unguwa Uku din. Bayan na kammala firamare sai na tafi Sakandaren ’Yan mata ta Gwamnati da ke Sule Tankarkar a Jihar Jigawa inda na kammala a 1995. Yanzu haka ina da shaidar karatu na NCE sannan ina shirin komawa karatun digiri na farko a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, insha Allah.
Aiki:
Na fara aikin koyarwa a wata makarantar kudi da ke CBN kuarters mai suna New Era Nursery and Primary School. Na yi aiki da su na shekara biyu na bar su na koma wata makarantar kudi da ke Unguwa Uku, Layin Yarbawa mai suna Friendship International School daga nan na sake komawa wata kungiyar Mai Zaman Kanta da ke cikin Asibitin Malam Aminu Kano wato Institute of Human birology Nigeria (IHbN) na yi aikin sa kai a sashin Kula da Jama’a, (Home Based Care). Tafiya sannu- sannu kwana nesa ina wannan aiki sai na shiga kungiyar Ba da Agaji ta Red Cross da ke Kano har zuwa yanzu ina cikinta. Bayan na bar IHbN sai na samu koyarwa a Ma’aikatar Ilimi wato (KS SS MB) ina matsayin malamar makaranta waiwaye adon tafiya duk da wannan ayyuka da nake ba su hana ni sana’a ba inda nake kasuwancin sayar da kayan sawa da na dakunan cin abinci. Nakan je kasashe daban-daban don sayo kaya a can. Kuma nakan yi rubuce-rubucen littatafai masu ma’ana wanda rashin samun tallafi ya hana ni buga su kamar littafina mai suna ‘Matsalolin Auren Dole’ wanda na yi dubi a kan abin da yake faruwa inda za ka ga iyaye ke sa ’ya’ya ko tilasta musu auren dole amma in wani abu ya faru kamar yarinya ta kashe mijinta ko ta yi yunkurin haka sai ka ga yarinyar kadai ce ke fuskantar hukunci, duniya kuma ta yi ta Allah wadai da ita su kuma iyayen ba hukunci a kansu wanda ni ina ganin haka a matsayin cin mutunci da keta haddin ’ya’ya mata.
Na kuma rubuta wani fim mai suna ‘Ra’ayi ko Sunnah?’ Shi ma na yi duba a tsanake a kan abin da wadansu maza ke yi a kan wadanda idan suka saki mace sai su ki ba ta kudin abinci, yara da ke tsakaninsu da matar da suka saka a wani salo na musguna wa matar da aka saki sun manta Allah Zai tambaye su kiwon da aka ba su. Za ka ga har abin ya kai ga zuwa kotu, ka ga mutum ya ce zai ba da Naira dubu uku a wata sai a zo kuma ya shafe sama da wata biyar bai biya ba amma yana ba budurwarsa ko bazawararsa kudin zuwa biki. Shi ne na yi rubutu a kai nake neman wanda zai taimaka a daukar mini shi ya zama fim don zai fadakar ya kuma ilimantar sosai.
Ina wadannan aikace-aikace da rubuce- rubuce da neman kudi sai muka hada gwiwa da Ibrahim Isyaku wanda aka fi sani da 2Able Graphics muka bude shago tare muna aikin wallafe-wallafe da ake kiran shagonmu da suna 2 Able Graphics wato ni da shi don haka nauyi ya kara hawa kaina inda na zama Manajar Darakta ta 2Able Graphics da ke Unguwa Uku, Layin Mai Nono da ke karamar Hukumar Tarauni amma shi Allah Ya yi masa rasuwa. Bayan wallafe-wallafe muna yin kwangilar abincin biki ko na suna ko na aure da sauransu har rigunan T-Shirt muna yi musu rubutu da ado.
Kwasa-Kwasan da na yi:
A shiga ta kungiyar Scout zuwa yanzu na samu damar yin kwasa-kwasai da dama kamar haka: General Information Course (G.I.C) sai kuma Basic Training Course (B.T.C) na yi shi ne a Jihar Kogi a wani gari da ake kira Asaya a yankin Kabba, sannan na rubuta jarrabawar kwas din da ake cewa Throy duk wannan na yi su ne a karkashin kungiyar Scout sai na sake komawa na yi wani kwas din irin wannan a CUBs Scout wato bangaren yara ke nan su kuma a Jos na yi.
Nasarori:
Alhamdillah, na samu nasarori da dama musamman ta sanayyar jama’a, ina jin dadi idan na ga daliban da na koyar sun zama wadansu. Kuma har gida na yi da mota. Sannan wannan aikace -aikace da nake kan yi musamman na Scout ya ba ni damar karawa da saura ’yan Scout na Najeriya wanda hakan ya sa na zama mace ta daban a Arewacin Najeriya domin duk yankin Arewa babu mace mai mukamai irin nawa, kuma ina mai alfahari da hakan. Har ila yau ni ce mace tilo a duk Arewa da take da yara ’yan Scout wato Scout Troops.
kalubalen da na fuskanta:
A rayuwa ba za a yi gwagwarmaya a rasa kalubale ba amma abin da ya fi ci mini tuwo a kwarya shi ne yadda wadansu maza ke amfani da raunin da ’ya mace take da shi wajen cimma bukatun Shaidan a wajen aiki, ga gaskiya karara ana gani sai ka ga an take kawai wai don mace ba ta biya musu wasu bukatunsu ba.
Kungiyoyi:
Na shiga kungiyoyi da dama kamar Foundation For The Support of Less Pribilege, Reformation, wato Gidauniyar Taimaka wa Gajiyayyu da Marasa Galihu, da Pronet, wato kungiyar Matasan Arewa da dai sauransu.
kasashen da na je:
Na ziyarci kasashe irin su Benin da Ghana da Nijar da Togo da Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai). Sannan na ziyarci jihohi da dama a Najeriya.
Burina a rayuwa:
Burina in zama babbar ’yar kasuwa a wannan kasa tamu Najeriya. Sannan ina da burin kare hakkin mata da kuma yaki da gurbacewar tarbiyyarsu.
Tufa:
Tufar da ta fi burge ni kuma nake amfani da ita, ita ce doguwar riga marar nauyi da za ta rufe mini jikina wanda duk ya gan ni ba zai yi min kallon mutunuyar banza ba, sannan sai in yafa gyale don na kara rufe jikina da kyau.
Hutu:
Na fi yin hutu a Jihar Legas amma da so samu ne da na rika fita kasashen waje ina yi a can.
Yawan iyali:
Yanzu dai ba ni da iyali amma ina rokon da Allah Ya kawo masu albarka
Shawara ga iyaye:
Kira na farko ga iyaye musamman iyayenmu mata shi ne su riki addini da kyau. Sannan su yi kokarin tura ’ya’yansu makaranta ta addini da ta zamani. Sannan ba na goyon bayan a rika cire yara mata in suna karatu ana yi musu aure, yin haka ba karamar koma baya ba ce. Karatu ba ya hana aure, sannan aure kuma ba ya hana karatu. Sannan iyaye musamman mata su daina dora wa ’ya’yansu mata talla, don talla wata jami’a ce ta kawar da budurcin mata.