‘Hawa acaba ya fi shiga jirgin sama tsada a Saudiyya’
Acaba na daya daga cikin hanyoyin sufuri a birnin Makkah na kasar Saudiyya musamman a cikin watan azumin Ramadan, lokacin da birnin yake karbar baki masu ibadar Umarah. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda ’yan acaban suke isar da jama’a wurare cikin sauki da hanzari duk da cinkoson ababan hawan da birnin yake fuskanta […]
Acaba na daya daga cikin hanyoyin sufuri a birnin Makkah na kasar Saudiyya musamman a cikin watan azumin Ramadan, lokacin da birnin yake karbar baki masu ibadar Umarah.
Wannan ba ya rasa nasaba da yadda ’yan acaban suke isar da jama’a wurare cikin sauki da hanzari duk da cinkoson ababan hawan da birnin yake fuskanta a irin wannan lokacin. Masu ibadan dai sun fi ziyarar Masallacin Harami, wanda yake a tsakiyar birnin.
Duk da yawan motocin safa-safa, yawancin masu aikin Umarah sun son hawa babur saboda a cewarsu ya fi biyan bukata cikin lokaci. Dalili da wannan ne ya ’yan acabar birnin suke cin karensu babu babbaka, inda suke cajan fasinjojinsu makudan kudi. A wasu lokutan ma, farashin acaban yakan saba hankali.
Wani dan acaba mai suna, Imran al-Yazidi, ya ce, “suna cajan Riyal 500 (kimanin fiye da naira dubu 26 ke nan) a tafiyar da ba ta wuce Kilomita biyar ba.” Kodayake, ya ce hakan ya fi faruwa ne a lokacin 10 karshe na watan azumi saboda yadda ake samun karin zirga-zirgar dimbin masu aikin Umarah. Har ila yau a daya bangaren, binciken da jaridar Arab News ta gudanar, ya nuna cewa ana samun tikitin jirgin sama ne daga Riyal 300 (kimanin naira dubu 16 ke nan).
Wannan na nufin a yanzu a birnin Makkah, farashin acaba ya fi na karamin tikitin jirgin sama da bambancin naira dubu 10 ke nan.
Har ila yau, mazauna birnin sun sha bayyana korafinsu bisa ga yadda ’yan acaban suke tukin ganganci. Wannan ya sa hukumomin birnin dauka matakai na rage yawansu, amma alamu na nuna cewa hakan na neman cin tura.