Hawaye don kasata
A halin yanzu kasar Nijeriya na cikin mawuyacin halin da Allah ne kadai yasan ranar fitarta.Tun lokacin samun yancin kai a kasar, kasar ta shiga taskun da aka rasa ta ina abin ya bayyana? Wanda kuma hakan ba ya rasa nasaba da tuggun masu mulkin mallakar waccan zamanin, duk mutumin da aka ce kana da […]
A halin yanzu kasar Nijeriya na cikin mawuyacin halin da Allah ne kadai yasan ranar fitarta.
Tun lokacin samun yancin kai a kasar, kasar ta shiga taskun da aka rasa ta ina abin ya bayyana? Wanda kuma hakan ba ya rasa nasaba da tuggun masu mulkin mallakar waccan zamanin, duk mutumin da aka ce kana da bambancin akida da kuma addini da shi, to labudda sai ka yi da gaske zamanku cikin amana zai tabbata.
A wajen shekarun 1970 rikicin kabilanci bai yi tasiri a kasar Nijeriya ba, kamar yau, amma a yau bayan rikicin kabilanci da ake fama da shi, sai kuma wani babban kalubalen da ke fuskantar kasar wanda ke barazanar rabewarta gida biyu, abin da wasu masana da dama ke ganin yiwuwar hakan zai kawo zaman lafiya, koma dai mene ne lokaci ne zai tabbatar da hakan.
A shekarar 1960 bayan samun ’yancin kai yankunan kudu sun mai da hankali kwarai wajen ciyar da garuruwansu gaba, tare da inganta ilimi a jihohinsu, abin da ya ba su damar rike kambin nagartar ilimi a kasar, wani abin mamaki kafin samuwar man fetur a kasar yankin Arewacin ke rike da ragamar arzikin kasar ta hanyar noma da kiwo, amma bayan samuwar man fetur sai yankin Arewa ya zama ci baya, ta hanyar watsar da noma da kiwon da aka san shi da su, ya rungumi sabgogi abin da ya janyo zubewar martarbar yankin.
Naka shi ke bayar da kai
A halin yanzu takai yankin kudu suna ganin yankin arewa sun zame musu alakakai ta hanyar cin arzikin kasar bada guminsu ba. Yanzu ta kai suna kallon yankin arewacin kasar da yanta’adda wadanda suke bata sunan kasar ta hanyar tayar da hankali a kasar wannan ce tasa suke ganin lokaci ya yi da za ‘a raba kasar kowa ya ci abin da yake dashi. Ko a kwanan baya sai da wasu jihohi daga yankin kudu suka fito da wani sabon salo na yi wa duk wani dan ci rani daya fito daga yankin arewacin kasar lasisi a matsayin wanda aka san da zamansa saboda kada su tayar musu ta fitini, domin suna musu kallon hatsari a jihohinsu.
Kafin wannan ma, cikin wadancan jihohi sai da jihar Imo ta kama wasu daruruwan mutane wadanda suka fito daga arewarcin kasar da sunan masu tada zaune tsaye.
Yanzu dai takai yankin kudu shi ke lakace wa Arewa hanci da kallon rainin wayo, wani karin abin takaici shi ne yanzu martabar da dan Arewa ke da shi a lokutan baya ta zube, inda ake kallon duk mutumin da ya yi shiga ta kamala a matsayin dan ta’adda.
Wai Arewa ba manya ne?
Shugabanci nagari da shi ne kowace al’umma take samun cigaba, amma a kasa irin ta Nijeriya abin ba haka yake ba, musamman a Arewa, inda yawanci wasu daga cikin manyan yankin ba su damu da halin da yankin ya shiga ba, misali yadda mutanen Arewacin kasar suke fama da matsanancin duhun kai da jahilci, wanda takai kwakwalensu ba sa ba su sako daidai, abubuwa da yawa suna faruwa a yankin wajen tuggu, amma mutane ba sa fahimtar komai balle su ba yankin nasu kariya.
Abubuwan da mahukuntan yankin suka kasa samarwa yankin.
*Ilimi
*Lafiya
*Wutar lantarki.
*Hanyar sufuri.
*Sana’o’in dogaro da kai.
Mu dauka cewa wutar lantarki matsala ce da ke addabar kasar baki daya, amma ragowar wadancan abubuwa yankin Arewa ya fi samun koma baya fiye da yankin kudu, to wai shin ina shugannin suke.
A yau ta kai idan kana son ilimi da lafiya da kuma ruwan sha sai ka saya da kudinka.
Wani abin mamaki shi ne manyan Arewa suke bada gudummuwa wajen dankwafe mutanen yankin, inda za ka ga yaran manyan yankin makarantunsu daban da ta talakwan kasar haka unguwanninsu daban da na talakawan kasar, wannan ne dalilin da ya janyo talakawan kasar basa samun damar ganawa da manyan yankin balle har su kai musu kukansu.
Abin mamaki kwanan baya na ji wani daga cikin malaman manyan makarantun gaba da sakandire a Arewa yana bada sanarwar cewa duk dalibin da bai samu cin jarabawar Turanci da lissafi ba za a ba shi matsugunni a jami’a ba.
Abin da na tuna a lokacin shi ne makarantu irin ta ’ya’yan talakwan sam ba a koyar da Turanci yadda ya kamata balle su iya shi sosai, lissafin kam ba a maganarsa, domin yana cikin darussa masu wahala a makaranta, wannan tasa mafi yawa daga cikin yaran talakawa ba sa samun damar shiga manyan makarantu sakamakon faduwa wadancan darusa da aka gindaya sharadin sai ka ci za ka samu nasara.
Naka sai naka
Allah ya hore wa Arewa manyan mutane masu arziki ya kuma hore wa yankin kasar noma, amma abubuwa a yankin ba sa tafiya daidai sakamakon halin ko-in-kula da manyan ke yi wa kankanan.
Ba na mantawa da wata hikima ta ’yan Kudu, a duk lokacin da aka samu wani mai hannu da shuni a unguwa to zaka ga ya dauki dawainiyar karatun wasu matasa a unguwar, kuma da zarar wadannan matasa sun kammala karatunsu su ma za su dauki nauyin karatun wasu a tare da su wannan ce tasa suka yi wa ilimi kwaf daya.
Amma a yankin Arewa za ka ga mutum mai mulki wanda nauyin talakawa ya hau kansa, amma sam ya kasa biya musu bukatunsu, balle kuma ka zo batun mai hannu da shuni wanda yake ganin ba hakkin kowa a kansa.
To gaskiyar magana ita ce lokaci ya yi da manyan masu mulkin za su hada karfi da karfe ku dawo da martabar yankin, ta hanyar ciyar da yankin gaba, hakan ko ba zai samu ba sai kun jure matukar jurewa kun ajiye son zuciya, kun nuna yatsa ga duk wanda ya nuna wa Arewa yatsa kuma ku ji cewa ciyar da yankin gaba tamkar shi ne aikinku na karshe a duniya, wannan shi ne abin da magabata suka yi irinsu:
Sa Abubukar Tafawa Balewa.
Sa Ahmad Bello Sardauna.
Sun yi aiki na kwarai kuma har yau ana tunawa da su.
Don haka ina sake kira gareku ku dage sosai wajen taimakon al’ummarku, musamman wajen ciyar da iliminsu gaba kada ku bari matasan Arewa su lalace, domin yanzu shaye-shaye ya yi a cikinsu sakamakon rashin ilimi da kuma abin yi.
Ku gina biranen Arewa da karkarunsu kamar yadda yankunan Kudu suke ginuwa irinsu.
Porthaircurt
Legos.
Delta
Ribas.
Imo da sauransu.
Ku kusanci danginku ku ji matsalolinsu ku bude idanununku sosai ku zakule su waye ke amfanin da sunan yankin Arewa suke bata sunan yankin?
Zubar da jinin ya isa haka, ya kamata ku yi wani abu. Allah ya taimaka. Za a iya tuntubarsa ta i-mel dinsa: r
[email protected]