Hayaƙin janareta ya kashe dalibai 2 a Kogi

Daliban sun rasu yayin da suke barci.

Hayaƙin janareta ya kashe dalibai 2 a Kogi

Hayaƙin janareta ya yi ajalin wasu daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi biyu, yayin da suke barci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Ovye Aya, ya tabbatar wa Aminya faruwar lamarin a daren ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewar daliban sun rasu ne bayan yin barci a gidan wani abokinsu da ke wajen makarantar.

An tsinci gawar daliban; Bilikisu Tijani Eleojo mai shekara 20 da Ibrahim Haliru, mai shekara 26.

Wata majiya ta bayyana cewa, wani daga cikin abokan daliban ne, ya gano sun rasu a ranar Talata, bayan ya je duba su.

An bayyana cewa daliban na zaune a unguwar Ganaja da ke Lokoja, amma saboda nisan gidansu suka yanke shawarar kwana a wajen abokinsu domin samun damar halartar aji washegari cikin sauki.

An garzaya da daya daga cikin wanda ya tsira zuwa asibiti, yayin da aka ajiye gawar wadanda suka rasu a wani asibiti da ke Lokoja.

Mai magana da yawun Kwalejin, Uredo Omale, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kai rahoton faruwar lamarin ga rundunar ‘yan sandan jihar domin gudanar da bincike.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Aya, ya bayyana cewa bincike ya nuna daliban biyu sun rasu sakamakon shakar hayaƙin janareta.

Ya ce sun kunna janareta kusa da tagar dakin da suka kwanta, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu kafin wayewar gari.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS