Hayaƙin janareta ya kashe dalibai 7 a Bayelsa

Ma’aikatan da ke cikin ɗakin suna yin aiki har tsakar dare, bayan sun kunna janareta saboda rashin wutar lantarki.

Hayaƙin janareta ya kashe dalibai 7 a Bayelsa

Kimanin mutum bakwai ne suka n rasa rayukansu bayan shaƙar hayaƙin janareto a wani ɗakin naɗar sauti (studio) a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

An ce waɗanda suka mutun suna aiki ne a studion, mallakin ɗaya daga cikinsu mai suna Akpos Barakubo, a lokacin da lamarin ya faru a daren ranar Litinin.

A cewar mazauna yankin, ma’aikatan sun yi aiki har tsakar dare, inda suka sanya janareton lantarki  saboda rashin wutar lantarki, inda suka yi barci suna aikin.

Aminiya ta samu rahoton cewa an gano gawarwaki shida da safe, yayin da mutum ɗaya da aka samu baya cikin hayyacinsa aka garzaya da shi asibiti, daga baya ya rasu.

An kuma samu rahoto cewa akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su ɗalibai ne a wata jami’a da ke Jihar Delta kuma sun kasance suna naɗar waƙa ne domin samun kuɗin karatunsu.

Har zuwa lokacin gabatar da rahoton, jami’an tsaro sun killace wurin, yayin da aka kwashe gawarwakin zuwa ɗakin ajiyar gawa.

Wani mazaunin yankin, Mista Damion Asamonye, ​​ya zargi gwamnatin jihar da ta tarayya da kuma kamfanin rarraba wutar lantarki a kan lamarin, inda ya ce da a ce akwai wadataccen wutar lantarki, da ba a buƙaci yin amfani da janareta da daddare ba.

Ya ce, “Gwamnatin Tarayya da ta jiha duk sun gaza. Idan da akwai wutar lantarki, wataƙila da waɗannan mutane ba za su rasa rayukansu a cikin wannan yanayin ba.