Hayaki ya kashe matasa a Kaduna

A ranar Larabar makon jiya ne wadansu matasa biyu ’yan  kasar Nijar suka rasu bayan shakar hayakin gawayi da suka yi. An tsinci gawarwakin matasan ne a shagonsu da ke Titin Ibrahim Taiwo kusa da Kasuwar Barci a Tudun Wada, Kaduna. Shaidu sun ce babu wanda ya san ainihin abin da ya yi sanadiyar mutuwar matasan […]

Hayaki ya kashe matasa a Kaduna
Hayaki ya kashe matasa a Kaduna

A ranar Larabar makon jiya ne wadansu matasa biyu ’yan  kasar Nijar suka rasu bayan shakar hayakin gawayi da suka yi.

An tsinci gawarwakin matasan ne a shagonsu da ke Titin Ibrahim Taiwo kusa da Kasuwar Barci a Tudun Wada, Kaduna.

Shaidu sun ce babu wanda ya san ainihin abin da ya yi sanadiyar mutuwar matasan biyu da shekarunsu bai wuce ashirin da ’yan kai ba.

Amma ana ganin kamar shiga da tukunyar dafa shayi da murhu cikin shagonsu da suke ne ya yi sanadiyar mutuwarsu bayan sun shaki hayakin da ya cika shagon cikin dare a lokacin da suke kwance.

Daya daga cikin wadanda ke sana’ar sayar da gwanjo a kusa da shagon sayar da shayin da aka tsinci gawarwakin matasan mai suna Kabiru ya shaida wa Aminiya cewa sai da aka balle kofar shagon kafin a fito da gawarwakin matasan.

“Da misalin karfe 6 na safe da ba a ga sun bude kofar shagon ba, sai aka rika kwankwasa musu amma ba su bude ba. Ganin haka sai aka balle kofar inda aka tarar da su a mace cikin mayafi. Ko da aka bude an tarar da hayaki cikin dakin wanda hakan ya sa ake tsammanin shi ya yi sanadiyar mutuwarsu. Dukkansu ’yan kasar Nijar ne. Na kuma ga gawarwakinsu kwance a lokacin da muka shiga shagon,”inji shi.

Tuni dai aka yi jana’izar matasan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.