Hayakin janareto ya kashe mutane 6 a Bayelsa
Hayakin janareto yayi sanadin ajalin wasu iyalai su biyar a kauyen Emeyal, dake karamar hukumar Ogbia jahar Bayelsa.Hayakin ya kashe miji maisuna Goodluck Tubotamuno da matarshi Jennifer Asiagbuladia da kuma ’ya’yan guda uku. Hayakin janareton ya turnuke dadin da suke kwance ne a lokacin da suke barci. Wata majiya ta tabbatarwa da Aminiya cewa yadda […]
Hayakin janareto yayi sanadin ajalin wasu iyalai su biyar a kauyen Emeyal, dake karamar hukumar Ogbia jahar Bayelsa.
Hayakin ya kashe miji maisuna Goodluck Tubotamuno da matarshi Jennifer Asiagbuladia da kuma ’ya’yan guda uku. Hayakin janareton ya turnuke dadin da suke kwance ne a lokacin da suke barci.
Wata majiya ta tabbatarwa da Aminiya cewa yadda suka gane “mutuwar mutanen shi ne tunda suka kwanta barci ranar lahadi basu farka ba domin kofar su ba a budeta ba har said a muka fara jin wani wari mara dadi a ranar laraba shine muka shigo gidan muka fasa dakin aka ga gawarwakin su su biyar duka sun mutu”.
Da muka tuntubi mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar bayelsa Asinim Butswat, ya tabbatar mana da afkuwar wanan lamari, ya tabbatar da cewa hayakin janareto da suka shaka ne yayi ajalinsu. Ya kara da cewa sun sami labarin haddarin ne da misalin karfe 3.50 na yammacin Laraba, daganan suka garzaya kauyen inda suka tarar da wannan al,amari.
Harwayau Aminiya ta samu labarin wata gobara da akayi a mahaifar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wato Otuake, ta lakume rayukan wasu yara biyu a kauyen masu suna Fabour Agamawa da Juliet Agamawa. Duk ‘yan gida daya ya da kanwa.