Hayar keke ta rufa min asiri – Musbahu DK

Musabahu Ahmad wanda aka fi sani da (DK) wani matashi ne da ke gudanar da kasuwanci a Unguwar Tudun Maliki, Layin Allasure a Birnin Kano. Aminiya ta tattauna da shi kuma ya bayyana yadda harkarsa ta bayar da hayar keke ta rufa masa asiri inda ya samu nasarori masu yawa:   Mene ne takaitaccen tarihinka […]

Hayar keke ta rufa min asiri – Musbahu DK

Musbahu Ahmad (DK)

Musabahu Ahmad wanda aka fi sani da (DK) wani matashi ne da ke gudanar da kasuwanci a Unguwar Tudun Maliki, Layin Allasure a Birnin Kano. Aminiya ta tattauna da shi kuma ya bayyana yadda harkarsa ta bayar da hayar keke ta rufa masa asiri inda ya samu nasarori masu yawa:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka da yadda ka tsinci kanka a harkar hayar keke?

Sunana Musbahu Ahmad an haife ni a garin Lamire da ke Karamar Hukumar Garko a Jihar kano, ina zaune a Unguwar Sheka a Birnin kano. Shekarata 39 kuma ina da mace daya da ’ya’ya takwas. Akwai abokina Muhammad Salisu shi ne wanda ya fara ba ni shawara a kan in fara hayar keke. Mahaifiyar Salisu ita ce ta fara saya min keke ina biyanta, har ni ma Allah Ya hore min nawa, kuma yau akalla shekarata 18 ina yin wannan harka ta hayar keke.

Wanda zai fara  sana’ar hayar keke me zai bukata?

Da farko idan mutum zai fara hayar keke yana da kyau ya tanadi jarin da zai sayi kekuna, sai agogo na duba lokaci, sai littafin rubuta sunaye masu karbar haya. Sannan ya tanadi wurin da zai zauna ko rumfa ko shago ko duk inda zai kasance idan ana nemansa za a same shi. Sannan ya kasance inda zai fara wannan harkar an san shi a sosai shi ma ya san jama’ar da zai yi mu’amala da su. Domin harka ce ta amana za ka bayar da dukiyarka haya zuwa wani lokaci dole ya kasance ka san da su wa za ka yi harka. Idan ba ka san su ba, to ya kasance akwai wani da zai ba ka shaida a kansu.

Wace nasara ka samu a harkar hayar keke?

Na samu nasarori maso yawa. Da wannan harka na mallaki gida sannan ga shago na sayar da kayan masarufi, kana ga kadarori da na mallaka duk sanadiyar wannan harka ta hayar keke. Babban al’amari ’ya’yana takwas, bakwai daga ciki suna zuwa makarantar firamare kuma mai zaman kanta, kuma suna zuwa Islamiyya kuma duk da wannan harka nake biya musu kudin makaranta. Alhamdulillahi wannan harka ta biya ni daidai gwargwado. Wadansu mutane suna ganin sana’a ce ta kaskanci amma akwai rufin asiri a cikinta sai wanda yake ciki zai fahimci haka ga shi har abin hawa gare ni.

Mene ne babban kalubalen harkar hayar keke?

Kalubalen da muke fuskanta shi ne satar kekuna, wani lokaci wadansu za su zo su yaudare ka su tafi maka da keke ba za ka sake ganinsu ba. Idan ma kun hadu to sun riga sun sayar sai dai a bar ka da jele zuwa wurin ’yan sanda. Don haka babban kalubalenmu ita ce sata da wadansu batagari suke yi mana.

Kuma ga shi babu wata na’ura da za mu rika bibiyar kekunanmu da ake sacewa , idan har kekenka ya bata to sai dai ka yi hakuri, idan kuma Allah Ya sa kana da rabo, sai ka ganshi a wani waje ko dai an sayar da shi ga wani, ko kuma ka ganshi a wajen sayarwa.

Mene ne burinka nan gaba?

Burina a nan gaba ina so kamar yadda nake bayar da hayar keke ya zama motoci nake bayarwa da baburan Keke NAPEP domin ina da ido a harkar. Sannan ina so in taimaka wa wadanda ba su da aikin yi domin idan aka ce yau ina bayar da hayar mota ko Keke NAPEP ka ga wadansu za su samu aikin yi, ni kuma babban burina ke nan. Idan ka duba babbar matsalar da ta addabe mu ba ta wuce rashin tarbiyya da zaman kashe wando da wadansu daga cikin matasanmu suke yi ba.

Ko kuna bukatar tallafi daga  hukuma domin inganta wannan harka taku?

Tabbas idan gwamnati za ta ba mu tallafi za mu yi maraba da shi, domin idan gwamnati ta ba mu tallafi, ba mu kadai zai shafa ba, wadansu da dama za su karu, domin za mu dauki wadansu, su rika taya mu aiki su ma suna samun kudin shiga ka ga an taimaka wajen rage zaman banza. Don haka muna kira ga gwamnati ta karamar hukuma ko ta jiha ko Gwamnatin Tarraya su ci gaba da tallafa wa masu irin wannan sana’a tamu domin rage zaman banza a tsakanin matasa.

Wace shawara za ka ba matasa kan neman na kansu?

Shawarata ga matasa musamman wadanda suka je jami’a ko wadanda suke ciki a yanzu su farka daga barcin da suke yi. Domin yanzu lokaci ya yi da za su gane muhimmancin sana’a. Yanzu kowa ya amince gwamnati ba za ta iya ba wa kowa aikin yi ba, don haka wannan babban kalubale ne gare su. Lallai matasa su rungumi sana’a kada su raina ta su rike ta da muhimmanci. Maimakon raina sana’a da suke yi su rika amfani da abin da suka koyo a makaranta su inganta karamar sana’a zuwa babba. Idan muka rungumi sana’o’i muka inganta su to ba kanmu kadai muka gina ba, mun gina al’umma baki daya domin da ’ya’yanmu da kannenmu za su taso cikin yanayin dogaro da kai hatta tarbiyya za ta gyaru domin duk wand ka taimake shi zai rika girmama ka abin da a yanzu muka rasa. Kanana ba sa girmama manya.