Hayatu-deen ya fasa neman takarar shugaban kasa a PDP
Ya janye a sa’o’i kadan kafin fara taron zaben dan takarar jam’iyyar a zaben 2023
Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Mohammed Hayatu-deen ya janye aniyarsa a ranar zaben fitar da dan takarar jam’iyyar.
Hayatudeen ya sanar da janyewar tasa ce ta wasikar da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Dokta Iyorcha Ayu.
- APC ta dage taronta na zaben dan takarar shugaban kasa
- Bayan shan kaye, Sanata ya sa deliget su dawo da motocin da ya ba su
Sai dai wasikar tasa ba ta bayyana dalilin janye takarar tasa ba, duk da cewa ta fito ne sa’o’i kadan kafin fara babban taron.
Yanzu da janyewar tasa, mutum 14 ne za su fafata domin samun tikitin takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawar a zaben 2023.
Janyewar Mohammed Hayatu-deen ta zo ne kwanaki kadan bayan tsonon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya janje daga neman takarar, ya kuma fice daga jam’iyyar.
PDP na gudanar da babban taronta na kasa, inda za ta zabi dan takararta da zai daga tutarta da babban zaben 2023, daga ranar Asabar, 28 zuwa Lahadi, 21 ga watan Mayu, 2022.
Tuni dai al’amura suka fara kankama a filin taron da ke gudana a Birnin Tarayya, Abuja.
Latsa nan donn zuwa shafinmu kai-tsaye domin samun bayanai dall-dalla kan abubuwan da ke wakana a wurin taron.