Hector Moreno ya nemi afuwar Shaw
Mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta PSb Eindhoben, Hector Moreno, ya nemi afuwa kan ketar da ya yi wa Luke Shaw na kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester United.Shaw ya karye a wuri biyu a kafarsa bayan da Moreno ya yi masa keta a wasan da United ta sha kashi a hannun PSb Eindhoben […]
Mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta PSb Eindhoben, Hector Moreno, ya nemi afuwa kan ketar da ya yi wa Luke Shaw na kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester United.
Shaw ya karye a wuri biyu a kafarsa bayan da Moreno ya yi masa keta a wasan da United ta sha kashi a hannun PSb Eindhoben a gasar cin Kofin Zakarun Turai da suka buga.
Shaw ya shafe minti 10 ana ba shi agajin gaggawa kafin ya bar cikin filin a karawar da suka yi ranar Talata a Holand.
Moreno mai shekara 27 ya ce “Ban ji dadi ba da na zama sanadiyyar jin raunin Shaw, kuma ina neman afuwa.”
Hukumar kwallon kafa ta Turai ba ta da niyyar sake kallon ketar da aka yi a wasan ta faifan bidiyo, kuma kasancewar alkalin wasan bai hukunta Moreno ba, ita ma ba za ta dauki wani mataki a kai ba.
Ana saran Shaw mai shekara 20 zai yi jinya mai tsawo sakamakon karayar biyu.
“Abin babu dadi. Yadda aka kai masa hari bai dace ba. Ya yi kuka sosai saboda raunin,” inji kocinsa Louis ban Gaal.