Hedikwatar Tsaro ta musanta kashe fararen hula a harin Zamfara
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, Amnesty International, ita ma ta yi iƙirarin cewa sama da mutum 100 ne suka mutu.
Hedikwatar Tsaron Najeriya, DHQ, ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe fararen hula a wani harin sama da sojoji suka kai a Kasuwar Tumfa da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.
Sojojin sun ce babu wata sahihiyar hujja da ke tabbatar da cewa fararen hula ne suka mutu a harin da aka kai a ranar Lahadi.
- Jami’an tsaro sun kori ‘yan ta’adda daga Firamaren Dangani a Katsina
- Dalilin da muka hana Obi da Kwankwaso tikitin takara — PRP
Mai magana da yawun hedikwatar tsaron, Manjo Janar Michael Onoja, ya musanta zargin halaka fararen hulan, inda ya ce sun ƙaddamar da farmakin ne kan ’yan ta’adda a yankin kuma suna ci gaba da samun galaba a ƙoƙarinsu na murƙushe ’yan bindiga.
Rahotanni daga wasu kafafen watsa labarai na ƙetare sun yi iƙirarin cewa aƙalla mutum 72 ne suka rasa rayukansu a harin, yayin da wasu suka ce adadin na iya zarta haka yawa saboda yadda ‘yan bindiga da mazauna ke amfani da kasuwar.
Wani shugaban al’umma, Garba Ibrahim Mashema, ya ce ba a iya tantance ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, saboda kasuwar na haɗa mazauna da ‘yan bindiga a lokaci guda.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, Amnesty International, ita ma ta yi iƙirarin cewa sama da mutum 100 ne suka mutu, tare da cewa an yi jana’izar gama-gari ga wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa.
Sai dai da yake ƙara musanta lamarin, Manjo Onoja, ya ce harin ya ta’allaƙa ne kan ‘yan ta’adda bayan samun sahihin bayanan sirri.
Ya ce an harin kan wani taron shugabannin ‘yan bindiga, ba fararen hula ba, kuma har yanzu bincike bai tabbatar da zargin kashe fararen hula ba.
Sojojin Najeriya na ci gaba da kai hare-haren sama da na ƙasa kan ‘yan bindiga a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma a ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaro.