Hedkwatar soja ta gargadi matan sojojin da suka yi zanga-zangar tura mazansu fagen-daga

Sakamakon harin da ’yan Boko Haram suka kai garin Gwoza da ke Jihar Borno a makon jiya da ya yi sanadin rasuwar mutane da dama har da wasu jami’an tsaro, matan sojoji agarin Maiduguri sun gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da sake tura mazansu fagen daga ba tare da samar musu da kayan yaki […]

Hedkwatar soja ta gargadi matan sojojin da suka yi zanga-zangar tura mazansu fagen-daga
Hedkwatar soja ta gargadi matan sojojin da suka yi zanga-zangar tura mazansu fagen-daga

Sakamakon harin da ’yan Boko Haram suka kai garin Gwoza da ke Jihar Borno a makon jiya da ya yi sanadin rasuwar mutane da dama har da wasu jami’an tsaro, matan sojoji a
garin Maiduguri sun gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da sake tura mazansu fagen daga ba tare da samar musu da kayan yaki masu inganci ba.
daya daga cikin matan Malama Mary James ta shaida wa wakilinmu cewa ba su gamsu da yadda ake tura mazansu su fuskanci Boko Haram ba alhali ba a ba su kayan aiki. “Muna gudanar da wannan zanga-zanga ce saboda an sha kashe mana mazaje a wannan yaki amma har yanzu gwamnati ba ta daukar matakin da ya dace. Misali a makon jiya abin da ya faru a Gwoza an kashe mana mazansu kusan 50, don haka mun gaji da irin wannan wahala da muke shiga. Mu ne muke cikin wahala ga yara na zama marayu, mun rasa yadda za mu yi, domin manyan ba sa biyanmu hakkinmu da ya kamata su biya, kuma cikin gaggawa ake tashinmu daga gidajen da muke ciki, abu ya taru ya yi mana yawa. Ga matsalar rashin miji ga matsalar rashin muhalli da rashin abin da mutum zai ci da ta karatun yara,” inji ta.
Ta ce ko shakka babu suna bukatar a samu zaman lafiya a Borno da kasa baki daya suna so wannan abin ya kare da taimakon Allah kuma da taimakon mazansu, to amma
dole ne gwamnati ta duba irin asarar rayukan mazansu da kuma mummunan halin da iyalansu ke shiga, ta inganta masu kayayyakin aiki na zamani ta yadda za su iya fuskantar mutane don abin ya kare a lokaci daya.
Ta ce muddin aka bar mazansu babu ingantaccen kayan aiki za su tafi ne kawai a kashe su, shi ya suka ce sun gaji da irin wannan abu da ya ki ci ya ki cinyewa.
A martanin da hedkwatar sojan Najeriya ta mayar ta gargadi matan sojojin su guji tsoma baki kan yadda ake tura sojojin fagen daga, kamar yadda wata sanarwa da aka sanya a kafar sadarwar intanet na hedkwatar ta bayyana.
Hedkwatar sojan ta ce an samu shawo kan zaman dar-dar a barikin Giwa da ke Maiduguri da ayyukan matan sojojin suka haifar.
Zanga-zangar matan sojojin ta hana tura sojoji zuwa garin Gwoza da mayakan Boko Haram suka kwace shi a ranar Talatar makon jiya, inda bayanai suka ce an bar mata da aikin binne gawarwakin mazan da aka kashe a harin, lamarin da aka ce matan sun gaji da binne gawarwakin mazajen da aka kashe a garin.