Helikwaftoci ke kai makamai ga mahara – Dattawan Borno da Yobe

Dattawa da shugabannin siyasa a jihohin Borno da Yobe sun yi zargin cewa jirage masu saukar ungulu (helikwaftoci) ne suke kai makamai da harsasai da abinci da magunguna zuwa yankunan da aka san mazaunin ’ya’yan kungiyar Boko Harm ne a yankin Arewa maso Gabas.Kuma sun ce mahukunta a jihohin ba za su ce ba su […]

Helikwaftoci ke kai makamai ga mahara – Dattawan Borno da Yobe

Dattawa da shugabannin siyasa a jihohin Borno da Yobe sun yi zargin cewa jirage masu saukar ungulu (helikwaftoci) ne suke kai makamai da harsasai da abinci da magunguna zuwa yankunan da aka san mazaunin ’ya’yan kungiyar Boko Harm ne a yankin Arewa maso Gabas.
Kuma sun ce mahukunta a jihohin ba za su ce ba su san haka ba, kuma abin takaici ne a ce ayarin motoci kirar Toyota Hilud 20 zuwa 30 za su rika kai hare-hare ba wata matsala ba tare da an gano su ba, duk da dokar ta-baci da aka sanya wa jihohin.
Dattawan sun bayyana haka ne a taron manema labarai da suka kira a Abuja a ranar Litinin da ta gabata, inda suka kalubalanci gwamnati ta bayar da amsa kan harin da aka kai wa hedkwatar sojan sama ta Maiduguri da mahara suka kai inda aka ce sun ci karfin sojojin tare da banka wuta ga jiragen yaki da sauran gine-ginen sojoji duk da akwai dokar ta-baci da dokar hana fitar dare a birnin.
Dattawan wadanda suka yi magana a karkashin kungiyar Al’ummar Borno da Yobe sun kuma nemi wadanda suke kan madafun iko su bayyana wa ’yan Najeriya su wa suka ba da umarnin a janye jami’an tsaro daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Buni Yadi ’yan awanni kafin a kai harin da ya ci rayukan dalibai 59.
Tsohon Hafsan Sojin Sama Mashal Al’amin Daggash (mai ritaya), wanda ya yi magana a madadin dattawan, ya samu rufa bayan tsohon Ministan Kudi, Malam Adamu Ciroma da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Babagana Kingibe da datttijo Alhaji Shettima Mustapha da sauran shugabannin siyasa daga jihohin biyu.
Ya ce, “Shin mahukunta ba su da masaniyar helikwaftoci suna jefa bindigogi da harsasai da abinci da samar musu da magunguna a yankunan da aka san mazaunin maharan ne ba?”
Ya kara da cewa, “Yaya aka yi maharan suka iya kai hari ga hedkwatar sojan sama ta Maiduguri suka lalata tare da kone jiragen yaki da sauran gine-gine da kayayyakin sojojin, duk da akwai dokar ta-baci da ta hana yawon dare a garin? Ta yaya motoci kirar Toyota Hilud 20 zuwa 30 za su rika kai-kawo cikin jerin gwano, su kai hari alhali akwai dokar ta-baci ba tare da an gano su ba?”
Ya sake tambayar cewa, “Yaya aka yi kananan yara marasa alkibla, za su juya su zamo kwararru dauke da miyagun makamai suna kai-kawo ba wata matsala cikin jerin gwanon motoci da helikwaftoci ke yi musu rakiya?”
Ya kara da cewa, “Yaya aka yi tankar yaki kirar Shilka Tank da take iya harbo jiragen yaki dauke da makaman atilare da aka girka domin kare Barikin Soja na Giwa ta kasa aiki, lamarin da ya jawo asarar dimbin rayukan fararen hula da sojoji, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito? Shin ko muna fuskantar wani mugun shiri ne na boye a wannan rikici?”
Ya nuna mamaki kan yadda maharan suka iya kashe Janar Mamman Shuwa, wanda ya bayyana a matsayin gwarzon yakin basasa, duk da kasancewar an girka sojoji a kofar gidansa.
Tsohon Hafsan Sojan Saman ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta fallasa wadanda suka “kaddamar da kamfe din bata suna don haddasa rikicin addini da kabilanci a kasar nan ta hanyar intanet.”
Kuma ya bukaci Gwamnatin Tarayya cewa kada ta kara wa’adin dokar ta-baci da ta ayyana a jihohi uku na Arewa maso Gabas, inda ya ce, dokar ta gaza cimma manufar kafa ta.
Dokar ta-bacin, wadda aka kafa ta da farko a watan Mayun bara kuma aka sabunta ta na tsawon wata shida a watan Nuwamba, za ta kare a ranar 19 ga wannan wata na Afrilu.
Daggash ya ce kimanin garuruwa 18 maharan suka kai wa hari a cikin watan da ya gabata, inda suka hallaka dimbin jama’a, maimakon hanawa, sai hare-haren suka karu kuma kiri da muzu.   
Ya ce, “Ci gaba da zubar da jinin ya jawo asarar rayukan sama da mutum dubu 17. Kuma kididdigar da Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta fitar ya nuna fiye da mutum miliyan daya ne maharan suka raba da muhallinsu a watanni uku na farko, bana kawai. Kuma galibin wadanda lamarin ya shafa mata ne da kananan yara da kuma tsofaffi. Wannan hali da ake ciki ya nuna akwai bukatar gwamnati da kasashen duniya da kuma daukacin ’yan Najeriya su hanzarta shawo kan wannan bala’i da ke auka wa dan Adam a yankin.”