Hezbollah ta shiga yaki da Isra’ila don goyon bayan Falasdinawa
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta kaddamar da yaki kan Isra’ila a yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta kaddamar da yaki kan Isra’ila a yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
Hezbollah ta shiga yakin ne bayan an kashe daruruwan mutane a bangaren Isra’ila da na Falasdinawa a yakin da ya barke a ranar Asabar.
- Mutane 2,000 sun mutu a girgizar kasa a Afghanistan
- Ya datse hannuwan mahaifiyarsa da adda saboda rashin jituwa
Kungiyar Amnesty International ta yi zargin hare-haren Hamas sun yi ajalin fararen hula amma kungiyar ta musa zargin, inda ta ce, “sojoji kawai muka kai wa hari, kuma ya kamata Amnesty ta rika bambancewa tsakanin fararen hula da sojojin Isra’ila.
“Muna kuma fata Amnesty Interanational za ta turo mana karin makamai na zamani da za mu yi amfani da su wajen kai wa zallar sojoji hari.”
A safiyar Lahadi Hezbollah ta sanar cewa ta kai hare-hare a kan sansanonin sojojin Isra’ila da ke Lebanon, da nufin kwato yankunan da Isra’ila ta mamaye da kuma goyon bayan mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas.
“A ranar Lahadi 8 ga Oktoba, 2023, mun kai harin atilare a kan sojojin mamaya na Yahudawa a wasu wurare uku a yankin Gonakin Sheba da ke Lebanon,” in ji sanarwar Hezbollah a ranar Lahadi.
A ranar Asabar kwamandan rundunar Al-Qassan Birgade na kungiyar Falasdinawa ta Hamas, Mohammed Deif, ya yi kira ga Hezbollah ta shiga yakin da ake da Isra’ila.
Gidan rediyon rundunar sojin Isra’ila ya sanar cewa an kai wa sansanonin sojojinsu hari da rokoki a yankin Dutsen Kafr Shuba daga bangaren Lebanon.
Ba a dai san ko Hamas ce ko kuma Hezbollah ta kai hairn ba, kuma har yanzu babu wanda ya dauki alhainkin harin.
Amma dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai wa cibiyoyin Hezbolla hari da jirage mara matuka a yankin Shebaa Farm a matsayin ramuwar gayya.